Halin da gwamna Radda ke ciki bayan hatsarin mota

Asalin hoton, Umar Dikko Radda
Gwamnatin jihar Katsina ta yi ƙarin haske kan halin da gwamnan jihar, Dikko Umar Radda ke ciki bayan bayan wani hatsarin mota da ya yi a kan hanyar Katsina zuwa Daura a ranar Lahadi.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin X, ya nuna gwamna Radda na yin godiya ga jama'a bisa "addu'o'in da suke yi masa".
"Muna godiya da addu'o'i da ake ta yi mana. Allah ya jarabce mu da hatsarin mota amma mun samu sauki, muna nan a asibiti ana ci gaba da duba mu domin samun sauƙi," in ji gwamna Radda.
Bayanin da gwamnatin ta fitar game da hatsarin ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da gwamna Radda ke kan hanyarsa ta zuwa Daura, inda wata mota ƙirar Golf ta kauce hanyarta, kuma ta faɗa wa motar da gwamnan ke ciki.
Daraktan yaɗa labaran gwamnan jihar Katsina, Maiwada Dammallam ya tabbatar wa BBC cewa ''bayan abin ya faru, an kwashe su an kai su asibitin Daura inda aka ba su taimakon gaggawa na farko, daga nan kuma ya taho nan Teaching Hospital ta Katsina inda ƙwararrun likitoci suka sake duba shi domin tabbatar da cewa babu wata matsala kamar yadda yake a tsari kiwon lafiya,''
Gwamnatin jihar Katsina ta ce daga gwaje-gwajen da likitoci suka yi, gwamna Dikko Umaru Radda yana cikin ƙoshin lafiya.
Maiwada Dammallam ya ce akwai mutane uku a cikin mota a tare da gwamna Radda lokacin da abin ya faru, kuma su ma an duba lafiyar su a asibiti.
''Yana tare da chief of staff ɗin shi, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir da hakimin Kuraye da kuma Alhaji Shamsu Funtua. To dukkan su babu wani wanda ke da mummunan rauni, akwai dai wanda ke buƙatar dinki an yi, duk ma sun baro Daura, suna Katsina yanzu haka", in ji Maiwada Dammallam.
Daraktan yaɗa labaran gwamnan jihar Katsinan ya ce gwamnan ya ɗauki matakin rage yawan jerin gwanon motocin da ke yi masa rakiya zuwa Daura tun bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, saboda yana yawan zuwa garin na Daura da kuma komawa Katsina daga lokaci zuwa lokaci saboda mutuwar.
Ya ce ''Kamar mota uku ne a cikin tafiyar saboda tun da aka yi rasuwar nan yana ta zirga-zirga zuwa Daura, to don ya rage tsadar tafiye-tafiyen shi ne ya ke rage motocin da ake amfani da su tunda ana rugawa ne a je, a dawo.''
Wannan bayani na gwamnatin jihar Katsina dai ya musanta rade-raɗin da wasu ke yaɗawa a kafafen sada zumunta game da halin da gwamna Dikko Umar Radda ke ciki bayan hatsarin motar da ya ritsa da shi a ranar Lahadi.
Wane ne Dikko Radda?
Dikko shi ne gwamnan jihar Katsina mai ci, wanda ya kasance mai ilimi a fannin tsimi da tanadi.
An zaɓe shi kan muƙamin gwamna ne a shekara ta 2023
Kafin zama gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya kasance shugaban hukumar haɓɓaka manya da ƙananan masana'antu na Najeriya (SMEDAN).
Baya ga haka nan ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Katsina, kuma ya taɓa zama shugaban ƙaramar hukumar Charanci.
Radda ya taka muhimmiyar rawa a shirye-shiryen jana'izar tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar 13 ga watan Yuli a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.










