Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Iran ta yi watsi da sansanonin sojinta da ke Syria
- Marubuci, Nafiseh Kohnavard
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent, BBC World Service
- Aiko rahoto daga, Reporting from Syria
- Lokacin karatu: Minti 8
An yi watsi da abincin da aka ci aka rage a kan gadaje, ga kayyakin aikin soja da makamai da aka tafi aka bari - waɗannan su ne abubuwan da suka yi saura bayan janyewar ba zato ba tsammani da aka yi daga wannan sansanin mallakar Iran da ƙawayenta da ke ƙasar Syria.
Iran ta kasance abokiyar ƙawancen tsohon shugaba Bashar al-Assad na Syria fiye da shekara 10. Ta tura masa masu ba da shawara kan ayyukan soji, ta tattara masa mayaƙa na ƙasashen waje, ta kuma kashe kuɗaɗe masu yawa kan yaƙin na Syria.
Manyan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun gina sansanonin ƙarƙashin ƙasa, inda suke safarar makamai da horar da dubban mayaƙa. Iran ta ɗauki waɗannnan matakan a matsayin wani ɓangare na ''shingen tsaro'' tsakaninta da Isra'ila.
Muna kusa da garin Khan Shaykhun a lardin Idlib. Kafin faɗuwar gwamnatin Assad a ranar 8 ga watan Disamba, ta kasance ɗaya daga cikin muhimman wurare da ke ƙarƙashin ikon rundunar IRGC da ƙawayenta.
Daga babban titin da ƙyar ake ganin ƙofar shiga, wadda take ɓoye a bayan tulin yashi da duwatsu. Akwai wata hasumiyar tsaro a kan wani tudu, wanda har yanzu ke ɗauke da launin fentin tutar Iran.
Wani littafin da muka gano ya tabbatar da sunan sansanin: Matattarar Shahidi Zahedi - wanda aka sanya wa sunan Mohammad Reza Zahedi, babban kwamandan IRGC wanda aka kashe a wani harin da Isra'ila ta kai kan ƙaramin ofishin jakadancin Iran a Syria a ranar 1 ga Afrilun shekara ta 2024.
Akwai kayayyakin da aka shigo da su a baya-baya—mun tarar da rasit na alawa da shinkafa da man girki — waɗanda ke nuni da ci gaba da rayuwar yau da kullum a wurin har zuwa lokacin da suka watse. Amma yanzu sansanin ya samu sabbin mazauna, mayaƙan Uyghur guda biyu ɗauke da makamai daga ƙungiyar Hayaat Tahrir al-Sham (HTS), ƙungiyar masu fafutukar yaɗa addinin Islama wadda shugabanta Ahmed al-Sharra ya zama sabon shugaban ƙasar Syria na riƙon ƙwarya.
Uyghur ɗin sun iso ne kwatsam a cikin wata motar soji, suka buƙaci mu nuna masu shaidarmu ta ƴan jarida.
"Ƴan Iran ne ke zaune a nan, amma duk sun tsere," in ji ɗaya daga cikinsu, yana magana da yaren ƙasar Turkiyya. "Duk abin da kuka gani a nan nasu ne. Hatta wannan albasar da ragowar abincinsu ce."
Akwai kwanduna shaƙe da albasa a farfajiyar sansanin wanda har sun fara tsiro.
Sansanin na ɗauke da ramukan ƙarƙashin ƙasa masu zurfi da aka haƙa cikin tsaunuka. Akwai gadaje a wasu ɗakunan da babu tagogi. Rufin ɗaya daga cikin ɗakunan yana lulluɓe da yadudduka da ke da launukan tutar Iran kuma akwai wasu littafan yaren Farisa a jibge kan wani teburi.
Sun bar wasu takardun da ke ɗauke da muhimman bayanai na sirri. Duk a cikin harshen Farisa. Takardun na ɗauke da cikakkun bayanai kan dakarun, kamar lambobin jami'an soji da adireshin gidajensu, da sunayen ma'aurata da lambobin wayarsu a Iran. Daga cikin sunayen, a bayyane yake cewa mayaƙan da dama a wannan sansani sun fito ne daga rundunar Afghanistan da Iran ta kafa domin su yi yaƙi a Syria.
Majiyoyin da ke da alaƙa da ƙungiyoyin da Iran ke marawa baya sun shaida wa BBC Persian cewa galibin sojojin da ke sansanin ƴan Afghanistan ne tare da rakiyar "masu ba da shawara kan ayyukan soji" na Iran da kwamandojinsu.
Babban abin da Tehran ta ba da a matsayin hujjar shigar da sojojinta Syria shi ne "yaƙar ƙungiyoyi masu ikirarin jihadi" da kuma kare "wuraren da ƴan shi'a ke ɗauka da muhimmanci" daga ƴan sunni masu tsattsauran ra'ayi.
Hakan ya haifar da ɓullar ƙungiyoyin mayaƙan da galibi suka fito daga Afghanistan da Pakistan da Iraƙi.
Duk da haka, lokacin da komai ya fara taɓarɓarewa, Iran ba ta shirya ba. Umarnin janyewa ba su isa wasu sansanonin ba sai da lokaci ya kusa ƙurewa. Wani babban mamba na wata ƙungiyar sa kai ta Iraqi mai samun goyon bayan Iran ya shaida min cewa: "Abubuwa sun faru cikin gaggawa ne. Kawai an bayar da umarni ne cewa kowa ya sungumi jakarsa ya tafi."
Wasu majiyoyi da dama na kusa da IRGC sun shaida wa BBC cewa yawancin sojojin sun tsere ne zuwa Iraƙi, wasu kuma an umurce su da su je Lebanon ko sansanonin Rasha don a kwashe su daga Syria.
Wani mayaƙin HTS, Mohammad al Rabbat ya bayyana yadda ƙungiyar ta kama hanya daga Idlib zuwa Aleppo daga nan kuma zuwa Damascus babban birnin Syria.
Ya ce suna tsammanin aikin nasu zai ɗauki "kusan shekara guda" kuma mafi kyawun sakamako shi ne, "za su kame Aleppo cikin wata uku zuwa shida". Amma abin mamaki sai suka shiga Aleppo cikin ƴan kwanaki kaɗan.
Faɗuwar da gwamnatin ta yi cikin gaggawa ta biyo bayan harin da Hamas ta kai kan Isra'ila ne a ranar 7 ga watan Oktoba.
Wannan harin ya haifar da ƙaruwar hare-hare ta sama da Isra'ila ke kai wa IRGC da ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran a Syria da kuma yaƙi da wata babbar ƙawar Iran - ƙungiyar gwagwarmaya ta Hezbollah ta Lebanon, wadda aka kashe shugabanta a wani hari ta sama.
Wannan galabar da aka samu kan Iran da Hezbollah shi ne jigon rugujewarsu, in ji Rabbat mai shekara 35.
Amma babban raunin da aka yi masu daga cikin gida ne: an sami rashin jituwa tsakanin Assad da ƙawayensa masu alaƙa da Iran, in ji shi.
"An samu rashin aminci da rashin haɗin gwiwar soji a tsakaninsu. Ƙungiyoyin da ke da alaƙa da IRGC suna zargin Assad da cin amana da kuma ganin cewa yana kwarmata wa Isra'ila bayanai kan wuraren da suke."
A lokacin da muke wucewa ta Khan Shaykun, sai muka ci karo da wani titi da aka yi wa fentin da launukan tutar ƙasar Iran. Hanya ce ta zuwa wata makaranta da ake amfani da ita a matsayin hedkwatar Iran.
A bangon da ke hanyar shiga banɗaki, an rubuta taken: "Down with Israel" da "Down with the USA", wato a taƙaice a daƙushe Amurka da Isra'ila.
Ya bayyana cewa an kuma kwashe mutanen da ke wannan hedikwatar cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Mun sami takardun da aka keɓe a matsayin "masu muhimmanci".
Abdullah, mai shekara 65, da danginsa suna cikin ƴan ƙalilan da suka zauna kuma suke rayuwa a nan tare da ƙungiyoyin da IRGC ke jagoranta. Ya ce ya kasance cikin rayuwar ta ƙunci.
Gidan nasa ba shi da nisa da hedkwatar kuma a tsakankani akwai ramuka masu zurfi tare da shingayen bincike da aka kiallace da wayar tsaro.
An mayar da gidan maƙwabcinsa matattarar soji. "Sun zauna a wurin da bindigoginsu suna kallon hanya, suna yi mana kallon waɗanda ake zargi," in ji shi.
Yawancin mayaƙan ba sa jin Larabci, in ji shi. "Su ƴan Afganistan ne da ƴan Iran da kuma Hezbollah. Amma duk muna kiransu ƴan Iran ne saboda Iran ce ke ɗaukar nauyinsu."
Matar Abdullah Jourieh ta ce ta yi matukar farin ciki da cewa "Rundunar sojin Iran" sun fice amma har yanzu tana tunawa da lokacin da suka kasance cikin ''damuwa" kafin janyewar sojojin. Ta yi tunanin za su kasance a tsaka-mai-wuya yayin da ƙungiyoyin da Iran ke marawa baya ke karfafa matsuguninsu da shirin yin yaƙi, amma sai "suka ɓace cikin ƴan sa'o'i kaɗan".
"Wannan mamaya ce, mamayar Iran," in ji Abdo wanda, kamar sauran, ya dawo nan tare da iyalinsa bayan shekara 10. Gidansa kuma ya zama sansanin soja.
Daga zantawar da na yi da ƴan ƙasar Syria, na yi la'akari da fusatar jama'a kan Iran, amma suna nuna sassauci kan Rasha.
Na tambayi Rabbat, mayaƙin HTS, me ya sa haka?
"Rasha na ta jefa bama-bamai daga sama, bayan haka, sun kasance ne a cikin sansanoninsu yayin da Iran da mayaƙansu suke a ƙasa suna mu'amala, mutane suna ganinsu kullm, kuma da yawa ba su ji daɗin hakan ba."
Wannan yanayin yana bayyana a cikin manufofin sabbin shugabannin Syria a game da Iran.
Sabbin hukumomin ƙasar sun sanya dokar hramtawa ƴan Iran da ƴan Isra'ila shiga Syria. Amma babu irin wannan haramcin a kan ƴan Rasha.
Har yanzu dai ofishin jakadancin Iran da fusatattun masu zanga-zanga suka mamaye bayan faɗuwar gwamnatin ƙasar ya ci gaba da kasancewa a garƙame.
Martanin jami'an Iran game da abubuwan da ke faruwa a Syria na cin karo da juna.
Yayin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ali Khamenei ya yi kira ga "matasan Syria" da su bijirewa waɗanda "suka kawo rashin zaman lafiya" a Syria, ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ɗauki ra'ayi mai sauƙi.
Ta ce ƙasar "tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke samun goyon bayan al'ummar Syria".
A ɗaya daga cikin hirar da ya yi ta farko, sabon shugaban Syria Al Sharaa ya bayyana nasarar da suka samu kan Assad a matsayin "ƙarshen shirin Iran". Amma bai yanke hukuncin samun "daidaitacciyar" dangantaka da Tehran ba.
A halin yanzu dai, ba a maraba da Iran a Syria. Bayan tsawon shekaru tana faɗaɗa aikin soji, duk abin da Tehran ta gina a yanzu ya wargaje, a fagen daga da kuma ga dukkan alamu, a idon akasarin al'ummar Syria.
A sansanin da aka yi watsi da shi, alamu sun nuna cewa an ci gaba da yunƙurin faɗaɗa ayyukan sojan Iran har zuwa cikin kwanaki na ƙarshe. Kusa da sansanin akwai ƙarin ramuka da ake ginawa, wanda da alama asibiti ne ake shirin ginawa. Simintin da ke jikin bangon har yanzu a jiƙe ya ke kuma fentin bai bushe ba.
Amma abin da aka bari a baya yanzu yana nuni ne da ɗan taƙaitaccen artabu -- akwai ƴan harsasai da kuma kakin sojoji da ke jiƙe da jini.