Tottenham ta dage kan Rodrygo, Crystal Palace ta fara tattaunawa da Wharton

Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham na ci gaba da zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Real Madrid Rodrygo, mai shekara 24, kuma za ta shirya biyan farashin da kulob ɗin na Sifaniya ke nema na fam miliyan 70 kan ɗan wasan na Brazil. (Fichajes)

Crystal Palace na tattaunawa da ɗan wasan tsakiya na Ingila Adam Wharton, mai shekara 21, kan sabon kwantaragi bayan ɗan wasan ya fara kakar wasa ta bana da ƙafar dama. (Give Me Sport)

Manchester United na buƙatar sayen ɗan wasan tsakiya a watan Janairu, inda ta sanya ido kan ɗan wasan Atletico Madrid Conor Gallagher, mai shekara 25, da ɗan ƙasar Jamus Angelo Stiller na Stuttgart, mai shekara 24. (Give Me Sport)

United ta nakuma zawarcin ɗan wasan Valencia Javi Guerra, duk da cewa Atletico da AC Milan suma sun nuna sha'awarsu kan ɗan wasan mai shekara 22. (Fichajes)

United ta fuskanci cikas a yunƙurin ta na dawo da ɗan wasan gaban Denmark Rasmus Hojlund mai shekara 22 daga aro da ya dke yi a Napoli a watan Janairu. (Star).

Ɗan wasan tsakiya na Scotland Scott McTominay na son Napoli ta sayi tsohon abokin wasansa na Manchester United Kobbie Mainoo, mai shekara 20, wanda ke fama da rashin tagomashi a Old Trafford. (Sun)

Wolves za ta mara wa sabon kocinta Rob Edwards baya a kasuwar musayar ƴan wasa a watan Janairu, inda ta ke da burin sayen matasan ƴan wasa na cikin gida. (NBC).

Ɗan wasan West Ham Niclas Fullkrug, mai shekara 32, na jan hankalin ƙungiyar AC Milan ta Italiya, a daidai lokacin da Hammers ke tunanin bayar da aron ɗan wasan na Jamus a watan Janairu. (Tuttomercatoweb).

Zakarun Denmark Copenhagen na son sayen ɗan wasan bayan Newcastle Emil Krafth, mai shekara 31, a watan Janairu. (Shields Gazette).