Ko kun san yadda za ku riƙa sabunta soyayyarku?

Hoton wata mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ''Dole a kodayaushe ka yi abin da za a so, ka nuna ƙwarewarka a kan kai kanka da kuma matarka''
    • Marubuci, Isidore Kouwonou & Alassane Dia
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afrique
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shasshafa abokiyar zamanka a bakin kofa lokacin da ta tare ka bayan ka dawo gida da yamma ko gogar jikinta idan za ka wuce a cikin gida, ko ka shammace ta da sumbata a lokacin da ba ta tsammani, duka wadannan abubuwa ne da ke tabbatar da kyakkyawar soyayya da alaka mai kyau tsakanin masoya.

Kyakkyawar mu'amulla da ke janyo so da kauna da sha'awa, ga aboki ko abokiyar zamanka, na da amfani kamar yadda numfashi yake da amfani da jikin mutum.

Hakan wata hanya ce da ya kamata ku rika yi kusan a kodayaushe domin inganta alakarku ta soyayya, amma kuma a kiyaye kada ya zama abu daya a lokaci daya ta yadda zai sa ku gunduri juna, har ma abin da ya kai ga rabuwa ko saki.

Tsokano sha'awa abu ne da yake da muhimmanci a soyayya.

A aure, '' dole a kodayaushe ka yi abin da za a so, ka nuna kwarewarka a kan kai kanka da kuma matarka,'' in ji Ndeye Khady Soumaré, wadda ake kira da inkiya Kira, ƙwararriya a kan koyar da yadda alaka za ta ɗore, a hirarta da BBC.

A soyayya ba abin da ake rainawa. A cewar mai koyar da masoya yadda ake jan hankali, dole ne masoya a kodayaushe su lalubo hanyar da za su kara yaukaka soyayyarsu, su ji kamar yadda suke ji tun a farkon lokacin da suka hadu - soyayyarsu ta zama kamar sabowa kullum.

Ba shakka idan mutum ya lakanci yadda ake janyo so da sha'awa tsakaninsa da matarsa ko abolkiyar zamansa , wannan yana sa alakarsu ta yi karko.

To amma mutane da dama suna faman sanin yadda za su iya sabunta soyayya ko alakrsu, ko ma yadda soyayyar za ta dore, bayan sun dade tare.

Mene ne jan hankali na soyayya?

Kwararriya a kan alakar soyayya, Ndeye Khady Soumaré,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wajen Ndeye Khady Soumaré, hanyar ɗauka ko jan hankali, ba wai lalle ba ne ka sa abokiyar alakarka ta bi abin da ka koya a gida ba.

Kira ta ce, shi dan'Adam Allah Ya halicce shi ne ya so abin da yake da kyau, ya ga mutumin da yake da ban sha'awa, wanda ake mutuntawa.

"Idan kana daukar hankali, za ka ga mutane suna mutunta ta, sannan ka ga suna son su taimake ka," in ji ta.

Daukar hankali ko burgewa ko ma shawo kai ta hanyar murmushi da kalamai masu dadi na sa a dauke ka da muhimmanci ka zama wani na daban, hadi da alkawarin kyautata wa mutum a duk tsawon rayuwa, na iya sa a kaunace ka, ka zama abin so da za a so zama da kai - wato ta haka za ka saye zuciyar mace ko ita mace ta saye zuciyar namiji, kauna ta kullu kenan.

To amma akwai bukatar a rika sabunta hanyoyin jan hankali da sa sha'awa ta yadda wannan alaka za ta rika zama kamar sabuwa a kullum.

Yadda za ka ja hankali?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ndeye Khady Soumaré ta bayyana karara cewa jan hankali a so ka, a yi sha'awarka ba abu ne mai sauki ba. "Dole ne a koya."

Saboda za ka iya koyon yadda za ka kula da jikinka da kuma muhallinka daga wajen iyayenka.

To amma fa idan mutum ya kai wasu shekaru, '' abu ne da ke zama mai matukar muhimmanci musamman a zaman aure

Kuma wannan ya dogara ga muhallin da mutum ya girma ko kuma yadda rayuwarsu take a matsayin ma'aurata.

Misali wadda ta taso a gidan da ake cin abinci a tebur da shirya cokula da kwanuka ko tangaran na cin abinci da kyau, za ka ga ta dauki wannan dabi'a har zuwa gidan aurenta.

To amma kuma rayuwar aure daban take zai iya kasancewa gidan da ta je aure su ba a tebur ake cikin abinci ba. Maimakon tebur su a kasa suke zama su ci abinci a kwano, in ji Kira.

Saboda haka a wajen Kira, jan hankali a nan ba lalle yana nufin ka sa wanda ba ku samu tarbiyya iri daya ba ka sa lalle ya yi koyi da abin da ka koya a gida ba.

A takaice ke da kika koyi cin abinci a tebur, idan kia je aure gidan da suke cin abinci a kasa, sai ki ajiye waccan tarbiyya taki, ko koyi ta gidan auren da kika je - cin abinci a kasa.

A zaman soyayya dole ne ka rika la'akari da abin da yake da kyau na rayuwa, ka yi yadda abokin zamanka zai kaunace ka zai ji yana son kasancewa da kai domin kana sa shi farin ciki.

Misali kana iya gaya wa matarka ko ki gaya wa mijinki cewa, '' gaskiya na yi sa'a da na same ki a rayuwa.''

Kwararriyar ta ce, a duk lokacin da mace ta tambaiyi mijinta abin da za ta yi ta sa shi dariya ko ya ji dadi, domin ya manta da gajiyar aiki, wannan na kara dankon soyayya tsakanin abokan zaman.

Halayyar wanda ya iya jan hankali

Mace da namiji a wajen furanni

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iya dafa abinci, da zubawa da gyara wajen cin abinci duka wadannan dabaru ne na jan hakali da kowa ya kamata ya koya. Haka kuma gyara waje a ofis da gida da daki duka suna da muhimmanci.

Mutumin da ya iya jan hankali a kodayaushe yana kokari ya sabunta hanyoyi da dabarunsa na burgewa, in ji Ms. Soumaré.

''Dole ne ta zama mai neman sanin yadda abu yake. Idan ba ka yi nasara ba

Akwai hanyoyi da daban-daban na kwarewa wajen daukar hankali, wadanda mutum zai yi kokari ya kware a kan wasu daga ciki domin cimma maunfa.

"Muna daukar hankali ta hanyar tufafin da muke sawa, da irin launin kayan da muke sawa da adon da muke yi da turaren da muke sawa, duka wadannan hanyoyi ne da mutum zai dauki hankali.''

"Da jin kanshin tuarren da mutum ya sa za mu smelling the perfume, we get an idea of ​​who we're dealing with," she adds.

Ndeye Khady Soumaré ta kara da cewa a wani bangaren mutane na la'akari da yanayin ilimi da iya maganar mutumin da ya dauki hankalinsu.

Wannan na sa mutum ya kaunace ka - wato ka dauki hankalinsa kenan.

Ka yi wa abokin zamanka kalamai masu dadi - kamar cewa kana sonta, ko tana da kyau, da sauransu wannan na inganta soyayya.

Ka guji yin abu ɗaya kodayaushe

Wata mata na shinshina fure

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kasancewa kusa da wasu mutane kamar 'ya'ya ko iyaye na hana ma'aurata ko masoya yin abin da zai ɗau hankali.

Dole ne a kodayaushe a rika farfadowa da sabunta soyayya a tsakanin maurata ko masoya da suke tare, domin wannan shi ke sa aure ya yi karko, da ginshiki mai karfin gaske.

Komai shekarun ma'aurata akwai irin yadda za su rika gudanar da nasu dabarun na sabunta soyayya.

Masoya za su rika sabunta soyayyarsu ta hanyar yin aubuwan da suke yi lokacin farkon alakarsu.

Kasancewar ma'aurata kusa da 'ya'ya ko iyayensu na iya hana su yin abin da zai kara dankon soyayyarsu, saboda haka akwai bukatar ma'aurata su samu lokaci da waje da za su iya raya soyayyarsu - kamar tafiya wani gari, ko zuwa gidan cin abinci ko tattaki tare.

Ndeye Khady Soumaré ta jaddada muhimmancin rawar da namiji zai taka wajen kyautata soyayyarsa da matarsa, kamar yadda yake mata tun farko ya ja hankalinta.

Misali ya rika yabonta, ya rika nuna sha'awarsa a kanta da sauran abubuwa ko maganganu da dadadawa da za ta ji dadi.

Al'ada kan hana jan hankali na soyayya a Afirka

Kwararriya Kira, ta ce, ''shekara goma da ta wuce musamman a Senegal mutane na jin kunya su gaya wa wani matsalolin da ke damunsu a alakarsu ta soyayya.''

To amma a yau abubuwa na sauyawa, mutane na kara fahimtar muhimmancin fitowa su yi maganar abin da ke damunsu

Masaniyar ta shawarci ma'aurata da su rika nazari da lura da halin da miji ko matarka ke ciki, domin kyautata alaka da kawar mata abin da ke damunta, ita ma kuma haka, saboda ta haka ne aure ke dorewa.

Ta ce, babban abin da ake bukata shi ne bayar da dama ta yadda matarka za ta iya fitowa fili ta gaya maka abin da ke damunta kai ma kuma ka iya fada mata abin da ke damunka, domin samun mafita - a gudu tare a tsira tsare.