Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Aljeriya ta zama wurin ziyarar addini ga Kiristoci mabiya Katolika a duniya?
Daga lokacin da ya zama Fafaroma a fadar Vatican, Fafaroma Leo XIV ya aikewa shugaban ƙasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune wasiƙa ta "musamman", inda a ciki ya bayyana "matuƙar kwaɗayin son kai ziyara ƙasar.
Bayan samun wasiƙar ne kuma ita kanta Aljeriyar ta yi maraba da hakan, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Ƙasashen Ƙetare ta Aljeriya ta bayyana. Kana ƙasar ta tura jakadanta Rachid Beledane zuwa Vatican inda ya halarci taron taya sabon fafaroman murnar zama jagoran Mujami'ar Katolika ta duniya.
To amma menene sirrin wannan buƙata da fafaroman ya nema, sannan wace alaƙa "ta musamman" ce ke tsakanin jagoran cocin da kuma ƙasar Aljeriya?
A cikin wasiƙar ya bayyana manufarsa ta so kai ziyarar, da dangantarkarsa da ƙasar. A tattaunawarsa da jakadan Aljeriya, fafaroman ya bayyana yana son kai ziyara ne mahaifar waliyi St. Augustine, wanda mabiya addinin kirista ke matuƙar girmamawa, kuma wanda ake ɗauka a matsayin wanda ake ganin sa tushen 'yan Latin mabiya Cocin Katolika baya ga manzonsu Paul.
A jawabinsa bayan da aka ya zama fafaroma, ya bayyana kansa a matsayin "ɗa ga St. Augustine", inda ya ce ya ɗora aƙdar addininsa bisa koyarwa da tsarin rayuwarsa. Babu shakka ana ganin wannan ne babban dalilin da ya ja hankalin fafaroman ya ke son jefa ƙafarsa Aljeriiya.
Wanene St. Augustine (354AD-430AD)?
Ana bayyana St. Augustinea matsayin uban kiristoci kuma masanin falsafa da ya shahara a addinin na kirista, kuma gimshiƙi ne a cikin adabi da al'adar ƙasashen yamma. Ana ma ganin shi ne wanda ke kan gaba wajen wallafa littattafai da bayanan addinin kirista fiye da manyan malaman lokacinsa.
Manyan malaman addinin kirista da masu rubuta tarihin mutane har yanzu suna al'ajabin yawan littattafai da wasiƙun da St. Augustine ya rubuta, waɗanda kawo yanzu an fiye guda 230.
An kuma fassara galibin littafansa zuwa harsunan duniya da dama, sai dai har yanzu akwai da dama da ke ajiye a ɗakunan karatu da aka bar su cikin harshen Latinanci da tun asali aka rubuta su a ciki.
St. Augustine dai masai kimiyya da fasaha ne, ƙwararre ne a lugga mai kare ra'ayinsa. Ya sadaukar da galibin rubuce-rubucensa ga muhawara da mayar da martani ga masu tsarin wa'azi da ya saɓawa aƙidarsa. Masanin adabi ne da kiɗ da al'adu da falsafa da kuma shari'a.
Ɗaya daga cikin fitattun ayukansa shi ne Iƙirari [Confession]. Littafin na da babi 13, inda a ciki ya yi bayanin rayuwarsa da gwagwarmayar neman ilmi da tauhidi, da shigar sa addininin kirista. An ce wannan littafin shi ne irin sa na farko da aka rubuta game da tarihin rayuwa a duk ƙasasen yamma.
Henry Chadwick farfaesa ne a fannin ilmin tauhidi a Jami'ar Cambridge, wanda ya bayyana St. Augustine a matsayin "gwanin duiyar yau" a tarihi. Rubuce-rubuce da ilmin da ya bayar ana jinjina su da cewa "sun yi fintinkau". Y bada gudummuwa matuƙa wajen ɗora ƙasashen yamma a akan turbar fahimtar "ɗabi'ar ɗan'adam" da ma'anar kalmar [Ubangiji] "Lord".
An haifi Saint Augustine a ranar 13 g watan Nuwamban 354 AD a garin Tagast (Souk Ahras), a inda ƙasar Aljeriya ta ke. Mahaifinsa Patricus ba shi da addini, sai dai an ce ya shiga Kirinstanci ɗan lokaci kafin mutuwarsa. Mahaifiyarsa Monica, ta sadaukar da rayuwarta wurin bautawa addinin, har ma hakan ya sa aka kira ta da waliyiya.
Lokacin ziyarar ibada zuwa St. Augustine
Ziyarar da Fafaroma Leo na huɗu ke so kaiwa ƙasar na da abubuwa da dama da suka shafi rayuwarsa wadda ke daidai da tsarin Koyarwar Augustine, wadda ya jagoranta, ya kuma bayyana cewa yana kan wannan aƙidar da koyarwar.
A garin Ahras (Tagast) zai kai ziyara wurin wata bishiyar zaitun mai ɗimbin tarihi da ta fi shekaru 3,000.
A ƙarƙashin bishiyar nan kabarin mahaifiyarsa, Sain Minica ya ke, wadda aka ce St. Augustine ya sha ambatawa a littafansa cewa ta taimaka masa wajen gudanar da ayukkan ibada.
Wannan zai iya zama tamkar wata ziyarar ibadar mabiya addinin Kirista ce..
A yankin Annaba (Hipon) nan ne ake da kufan Mujami'ar Zaman Lafiya, wadda Bishop Augustine ya jagoranta a lokacin rayuwarsa. Daga wurin ne ya gudanar da ayukansa na ibada da muhawara da sauran su. An ce a nan ya kan yi halwa na tsawon lokaci domin ya yi rubutu.
Wannan tafiya ce da ta haɗa muhimman dauloli da wuraren tarihi na Romawa da Numidiya da daular Byzantine da daular Musulunci a nahiyar ta Afirka, da ke kudu da Tekun Bahar Rum. A nan ne masu nazari da bincike za su bi diddigin asalin waliyin da ya samar da tsarin koyarwar addinini kirista na wannan zamani. Wato dai rana ce da ta fito daga kudu ta haska arewa.
Farfesa Chadwick ya faɗa a littafinsa, mai suna "The Dawn of the Church" cewa St. Augustine ya zarce duk tsaransa ɓangaren da ya shafi ilmi da tunani, har ma yana gaba da waɗanda suka yi rayuwa da daɗewa kafin shi, abin da ya fito da tasirin da ya ke da shi ga dukan mabiya Katolika da Otodoks.
Wannan tunanin cewa tuni Saint Augustine ya sha gaban masana da masu ilmin falsafa shekaru aru-aru, ya kuma yi wannan ficen a lokacin da ake da tunanin cewa mata ba su da wata kima kuma su ba kome ba ne face wani abu da maza suka mallaka. Kuma har yazu akwai masu adawa da wannan tsarin koyarwa ta Saint Augustine.