Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin naira tiriliyan 58.47
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ya gabatar da naira tiriliyan 58.47.
A kasafin, Tinubu ya tsara kashe naira tiriliyan 15.25 domin gudanar ayyukan yau da kullum na gwamnati, sannan ya ware naira tiriliyan 26.08 domin gudanar da manyan ayyuka da more rayuwa a ƙasar.
Tinubu ya tsara kasafin ne a bisa hasashen farahin gangar ɗanyen man fetur a kan dala 64.85.
Haka an yi hasashen sama da gangar ɗanyen man fetur miliyan 1.84 a kullum, sannan ya ayyana canjin dala a kan naira 1,400.
Ma'aikatun da suka fi samun kasafi su ne:
- Tsaro: Naira tiriliyan 5.41
- Aikace-aikace: Naira tiriliyan 3.56
- Ilimi: Naira tiriliyan 3.52
- Lafiya: Naira tiriliyan 2.48
Me ya kamata kasafin ya mayar da hankali a kai?
Wani masanin siyasa da BBC ta tattauna da shi, Henry Olonimoyo ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta yi bayani filla-filla kan yadda ta aiwatar da kasafin kudin da ya gabata, yayin da shugaban ƙasa ke shirin gabatar da kasafin shekara mai zuwa.
Olonimoyo ya ce akwai damuwa tsakanin al'umma kan cewa har yanzu ba a aiwatatar da wasu sassa na kasafin kudin shekarun 2023 da kuma 2024 ba, inda ya nanata buƙatar ganin ana fayyace duk wasu ayyukan gwamnati gabanin gabatar da sabon kasafin kudi.
"Zan so a ce gwamnati ta yi bayani sosai kan kasafin kudin da ya gabata, kasancewar akwai alamun cewa akwai ɓangarori da dama na kasafin 2023 da 2024 da har yanzu ba a aiwatar ba."
Ya ce bayanai sun nuna cewa duk da umarni da aka bayar na buƙatar bunƙasa yadda ake aiwatar da kasafin kuɗi, akwai ayyuka da dama wadanda ba a aiwatar ba, sai ga shi kuma yanzu an kawo kasafin 2026.
"Ina fatan cewa ko dai daga fadar shugaban ƙasa ko kuma daga ma'aikatar kasafin kudi za a samu wani jami'i da zai bayyana wa al'ummar ƙasa inda ake, domin gane yadda ake aiwatar da kasafin," in ji Olonimoyo.
Masanin siyasar ya kuma dora ayar tambaya kan ikirarin gwamnati game da kuɗaɗen shiga, kasancewar, a cewarsa abin da gwamnati ke fada ya saɓa da wanda ƴan kwangila ke bayyanawa.
"Tabbas shugaban ƙasa ya faɗa sau da dama cewa an samu ƙarin kudaden shiga a wannan shekara, cewa an cimma yawan harajin da aka yi hasashe.
"Amma daga abin da muke ji, ba a iya biyan ƴan kwangila ba, akwai matsaloli. Ko hakan na nufin cewa akwai matsalar kuɗaɗen shiga? Ya kamata shugaban ƙasa ya fito ya yi bayani kan wannan," in ji shi.
Yayin da ake shirin gabatar da kasafin kudin na shekarar 2026, Olonimoyo ya yi kira ga gwamnati ta mayar da hankali kan muhimman ɓangarori da suka shafi rayuwar ƴan Najeriya na yau da kullum.
"Ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci kamar noma da tsaro da kuma samar da kayan ci gaba, idan aka yi la'akari da ƙalubalen da muke fuskanta."
Ya kuma jaddada muhimmancin samar da sabbin ayyukan ci gaban ƙasa, ba tsayawa kawai kan ayyukan da aka fara ba.
"Bai kamata kawai a mayar da hankali kan babban titin gefen teku ba, domin wannan aiki ne na daban, amma ya kamata a duba yanayin manyan titunan gwamnatin tarayya da ke faɗin ƙasar.
Na san cewa suna buƙatar a waiwaye su."