Yadda ɗana ya kuɓuta daga masu garkuwa a Neja

Lokacin karatu: Minti 4

Da yake tattaunawa da BBC, mahaifin wani yaro mai shekara shida wanda ya kuɓuta daga masu garkuwa lokacin da ƴanbindigar suka je makarantarsu, ya yi bayani dangane da yadda ya sake yin ido biyu da ɗan nasa.

"Lokacin da na gan shi," in ji Lucas wanda ba sunansa ba ne na asali, "na ji daɗi ƙwarai."

"Na kira shi da sunansa, sai ya juyo sannan ya taho wurina da gudu ya rungume ni."

Lucas ya ce ɗan nasa ya shaida masa cewa yaran da aka sace daga makarantar St Mary's Catholic School suna bacci lokacin da hargowar masu garkuwar ta tashe su.

Masu garkuwar sun ɓalle tagogi bayan farfasa gilasai sannan suka kutsa cikin azuzuwan bayan buɗe wuta ga ƙofofin.

Wasu yaran sun haura ta kan kataga mai wayar tsaro da ta kewaye makarantar sannan suka tsere, to sai dai kuma ɗan nasa ya gaza tsallake shingen saboda yarintarsa, inda kuma ya samu wani wuri ya ɓuya.

Duk da cewa Lucas ya yi idanu biyu da ɗan nasa to amma sauran ƴaƴansa biyu da suka ɗan tasa har yanzu ba a gan su ba.

An dai sace ɗalibai 303 tare da malamansu 12 daga makarantar da ke ƙauyen Papiri na jihar Neja duk da hukumomi na cewa yara 50 sun kuɓuta daga hannun masu garkuwar.

Sai dai kuma wasu majiyoyi na cewa yaran guda 50 da suka kuɓuta ba da hannun ƴanbindigar suka ƙwace ba, inda aka ce suna daga cikin ɗaliban da suka tsira lokacin da ɓarayin suka shiga makarantar.

Alƙaluman sun dace da waɗanda ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN ta bayar, "mun samu tabbacin hakan daga iyayen wasu yaran da muka ziyarta".

In ji wakiliyar BBC, Madina Maishanu wadda ta kai ziyarar aiki garin da abin ya faru, ta ce ta yi magana da iyayen da suka yi ido biyu da ƴaƴansu a sa'a 24 da ta gabata.

Halin da iyaye ke ciki

Sai dai kuma wannan sanarwa ta janyo ruɗani a tsakanin iyaye inda wasu iyayen suka yi zaman dirshan a wajen makarantar da aka ɗauki yaran nasu, suna cike da ɓacin rai da damuwa kan cewa me ya sa ba a sanar da su labarin ba kai tsaye.

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, a wata tattaunawa da kafafen watsa labarai na cikin gida, ya ce an yi ƙarin gishiri dangane da yawan yaran da aka sace. "Idan muka yi ƙidaya, yawan bai kai yadda ake faɗa ba nesa ba kusa ba."

Gwamnan ya kuma zargi makarantar da buɗe ta duk an samu barazana daga ƴan bindiga shekaru hudu da suka gabata da kuma watanni biyu da suka shuɗe.

"Makarantun yankin sun kasance a rufe shekaru huɗu da suka gabata, na yi mamakin jin cewa makarantar tana buɗe."

Ya kuma sha alwashi yin duk mai yiwuwa wajen ganin an ceto dukkannin yaran. Sai wasu iyaye da suka tattauna da BBC ba su gamsu da abin da hukumomin ke cewa na yi ba na ganin an ceto yaran nasu.

"Ba zan iya faɗin halin da nake ciki ba," in ji Peter wanda ba sunansa na gaskiya ba ne wanda kuma ya ƙara da cewa " ban taɓa shiga damuwa kamar yadda nake ciki ba a yanzu."

Peter na cike da takaicin cewa gwamnan jihar Neja bai ziyarci makarantra da al'amarin ya faru ba, wani ƙauye kusa da mu kawai ya zo domin yin magana da jami'an tsaro da shugabannin al'umma dangane da yanayin."

"Saboda haka mun tabbatar d acewa gwamnati ba ta damu da mu ba, muna kamar mu ba ƴan ƙasar ba ne, sun yi watsi da mu."

Shi ma wani wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru ya shaida wa BBC cewa

"An kora yaran a ƙafa kamar yadda makiyaya ke kora dabbobinsu, wasu yaran na faɗuwa amma ƴan bindigar suna gargaɗin su da su tashi," in ji Theo wanda shi ma ba sunansa ba kenan.

"Yanbindigar sun haye a kan babura kimanin 50 a lokacin da suke kora yaran."

Ya kuma ce duk da ya ga yadda ake kora yaran amma ba bu wani abun da zai iya a kai.

"Ina jin kamar na bi su amma sai na yi tunanin cewa to ka na je wurin babu abin da zan iya yi."

Garin Papiri a baya-bayan nan ya kasance wani wuri da ya zama mai haɗari saboda garkuwa da jama'a domin neman kuɗin fansa, kuma a bayyane rashin tsaron da garin fama da shi yake.

Wasu da dama dai na ɗora laifin rashin tsaro ga irin girman jihar Neja wadda a taswira ta fi ƙasashen Turai da dama kamar Denmark da Netherlands abin da ya sa jihar ke da girman dajin da gwamnati ba ta da iko a kansa. Sannan kuma dazukan sun kasance hanyoyin saduwa da wasu ƙasashen Afirka.

Garkuwa da ƴan makarantar na Papiri shi ne karo na uku da ake sace ƴan makaranta a mako guda.

Ko a ranar Litinin sai da aka sace ƴan mata ɗalibai 20 a jihar Kebbi waɗanda aka shaida wa BBC cewa Musulmai ne.

An kuma kai wa wata coci hari a jihar Kwara inda aka kashe mutum biyu sannan aka sace gommai.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sha faɗin cewa gwamnatinsa na ɗaukar duk matakan da suka dace domin shawo kan matsalar..