Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko akwai wani abu da ya rage wa Salah a Liverpool?
- Marubuci, Andy Cryer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Senior Journalist
- Lokacin karatu: Minti 5
Za a ci gaba da tunawa da tattaunawar da Mohamed Salah ya yi da manema labarai a matsayin daya daga cikin tattaunawa mafi zafi a gasar Premier.
A yammacin ranar Asabar Salah ya ba mutane da dama mamaki lokacin da ya sanar da ’yan jarida cewa alakarsa da mai horaswa Arne Slot “ta lalace”.
Dan asalin kasar Masar din ya kasance daya daga cikin ‘yan wasa mafiya shahara a tarihin gasar Premier ya dora babban nauyi a kan Slot bayan shafe wasanni uku yana zama a benci, inda a wasanta da Leeds ranar Asabar ta tashi canjaras 3-3.
Tabbas zargin da Salah ya yi na cewa “an ajiye shi gefe daya” sannan kuma wani “ba ya kaunar zaman shi a kungiyar,” abu ne da koci Arne Slot ba zai taba so ya ji an fadi hakan ba a bainar jama’a, musamman ganin halin da kungiyar take ciki na rashin tabuka abin kirki inda take a matsayi na 9 a kan teburi.
To amma yanzu me ya rage wa Salah a Liverpool?
A watan Afrilu ne Salah mai shekara 32 ya sanya hannu kan sabon kwantaragin shekara biyu, sai dai a ranar Asabar ya bayyana cewa ba ya da tabbas ko ya riga ya buga wasansa na karshe a Liverpool.
BBC ta duba abin da zai iya faruwa ga dan wasan, wanda ya ci wa Liverpool kwallo 250 a wasa 420 da ya buga wa kungiyar.
'Tabbas alakar Salah da Arne Slot ta lalace'
Salah bai cika magana da ‘yan jarida ba, amma duk lokacin da ka ga ya zanta da su to lallai akwai abu mai muhimmanci da yake son ya fada.
Lokacin da aka tunkare shi a wannan karo, ya nuna karara cewa yana son zai yi magana.
Babu tabbas ko a kan mene ne yake son ya yi maganar.
Amma bayan ya fara magana, kalamansa sai suka jefa mai horaswa Arne Slot cikin matsi.
Kwana daya bayan haka, a ranar Lahadi, babu wata muhimmiyar alama da za ta nuna cewa Salah ya yi nadama ko kuma zai so ya janye kalamansa.
Majiyoyi da ke da masaniya sosai kan abin da ke faruwa a Liverpool sun fada wa BBC cewa tabbas alakar Slot da Salah ta lalace.
Sun ce kwata-kwata ba ya ganin cewa yana da sauran gudumawar da zai bayar a kungiyar karkashin jagorancin Slot.
Wannan ya sha bamban sosai da halin da ake ciki a watannin baya lokacin da Liverpool ta lashe kofin Premier inda bayan haka da kankanin lokaci ya sanar da sanya hannu kan kwantaragi mai tsoka.
Haka wasu majiyoyin sun ce Salah ba ya jin dadin yadda wasu masu sharhi da kuma tsofaffin yan wasan kungiyar ke nuna kamar yana daga cikin manyan matsalolin da suka sanya kungiyar ba ta tabuka abin kirki a wannan kakar.
Sun ce Salah na ganin cewa Slot na daukar abin da masu sharhin suke fada - to amma ko ba a saka shi a wasa ba, Liverpool ba wani kokari take yi ba.
An shaida wa BBC cewa Salah ba ya jin dadin sauyin tsarin wasa da aka samu a kungiyar a wannan kakar sanadiyyar sabbin ‘yan wasa da kungiyar ta sayo.
Majiyoyin sun bayyana yadda suke jin zafin hakan ganin yadda Salah ke matukar son Liverpool da kuma yadda ya damu da matsalar da kungiyar ke ciki.
An shaida wa saahen wasanni na BBC cewa Liverpool na duba komai game da Salah ci gaba da zaman Salah a kungiyar da idon basira duk da sha’awar daukar sa da ake samu daga kungiyoyin Saudiyya.
Ana ganin cewa Al-Hilal da ke karkashin jagorancin Simone Inzaghi na daga cikin na gaba-gaba a wannan yunkuri.
Sai dai har yanzu babu wata takamaimiyar magana mai kwari. A yanzu dai ana ganin Salah shi ma yana du a abubuwa ne da idon basira, musamman ganin yadda gasar Cin Kofin nahiyar Afirka ke gaban shi.
Me zai faru a nan gaba?
Magiya bayan Liverpool - da kuma masoya kwallo kafa na duniya za su jira su ga abin da zai faru a gaba.
Kuma da wuya a dade ana jira, domin a yanzu ma kungiyar ta cire sunan dan wasan daga cikin wadanda za suka je domin buga karawar kumgiyar da Inter a gasar zakaru ta Champions League.
Bayan nan kungiyar za ta fuskanci Brighton a gida a ranar Asabar, wanda zai zama wasa na karshe kafin Salah ya tafi gida domin halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Babu tabbas ko Salah zai buga wasan na Asabar, idan ma zai buga babu tabbas game da tarbar da zai samu daga masoyan kungiyar.
Ko ma dai mene ne zai faru, babu shakka wannan mako zai zama mai muhimmanci game da makimar dan wasan a Anfield.
'Salah ya yi kuskure' - martani
Toshin mai tsaron raga na Liverpool Rob Green ya shaida wa gidan rediyon BBC cewa:
Yana magana ne kawai idan ba ya jin dadin abin da ke faruwa ko idan ana cikin matsala.
Amma wannan ya ba Slot zabi ne da yawa.
Yanzu da gasar cin kofin Afirka ke matsowa,Slot zainiya cewa babu wanda ya fi karfin kungiya, ka tafi kawai.
Yanzu matsin ba ya kan Slot, gaskiya Mo Salah ya yi kuskure domin ganin irin abin da ke faruwa, da canjaras din da kumgiyar ta yi da Leeds, da ya yi shiru, domin matsi na karuwa bayan kowane wasa da ba a saka shi ba.
Yanzu Slot ne zai yanke hukunci. A nawa tunanin Salah ya cancanci yabo saboda gudumawar da ya bai wa Liverpool. Yanzu kana cewa za ka tafi. Kila yanzu, zainiya yiwuwa idan aka shiga Janairu kungiyar ta ce rabuwa ce ta fi alkhairi ga kowa. Ba zan yi mamaki ba idan haka ta faru.
Tsohon mai tsaron raga na Newcastle da Man City, Shay Given, ya shaida wa BBC cewa:
Na dan ji tausayin Mo Sallah. Lokacin da ala sanya maka bututun magana ba abu ba ne mai sauki, musamman idan mutum bai biga wasa sa yawa, musamman idan babban dan wasa ne kamar shi.
Sai dai babban abin da ya ban mamaki shi ne me ya sa Arne Slot bai tattauna da Salah ba kan halin da ake ciki gabanin yanzu? Ana magana ce ta babban ɗan wasa.
Na san cewa Mo yana cikin fushi ne, in ba haka ba ba zai fadi irin wadannan maganganu ba. Duk mun shiga irin wannan hali, idan ba a saka ka a wasa ba za ka ji haushi.
Tsohon ɗan wasan Ingila da Liverpool Michael Owen, ya wallafa a shafinsa na X: OhMo Salah. Na san irin yadda kake ji. Ka yi ɗawainiya da tawagar nan na tsawon lokaci kuma ka samu nasarorin da duk suka kamata. Amma wannan abu ne na ƙungiya, bai kamata ka faɗi irin abubuwan da fada ba a bainar jama'a. Za ka tafi gasar Afcon nan da mako ɗaya. Za ka zauna ka yi nazari kan abin da ya faru.