Labarin Mo Salah da yadda aka yi ya zama gwarzon Liverpool

Lokacin karatu: Minti 11

"A duk lokacin da na shigo nan, ba abin da nake tunawa sai yadda yake gudu da sarrafa kwallo, wanda hakan wani abu ne daban."

Daya daga cikin kocin Mohamed Salah na farko yana bude sabbin cibiyar horar da matasa a Nagrig, wani ƙauye mai kimanin nisan sa'o'i uku a Arewacin Alkahira.

A nan ne abin ya fara ga ɗaya daga cikin manyan 'yan wasan gaba a duniya – ɗan wasan da ya taka rawar da ta kai Liverpool ta lashe kofin Premier a watan Mayu.

A kan titunan Nagrig ne Salah ɗan shekara bakwai, ke buga kwallon kafa tare da abokansa, yana mai nuna cewa shi ne ɗan wasan gaba na Brazil, Ronaldo ko fitaccen ɗan wasan Faransa, Zinedine Zidane ko ɗan ƙasar Italiya Francesco Totti.

"Mohamed ƙarami ne idan aka kwatanta da takwarorinsa na ƙungiyar, yana yin abubuwa ko da manyan yara maza ba za su iya ba," in ji Abd El-Hamid El-Saadany yayin da yake nuna filin wasa na wucin gadi wanda a yanzu aka sanya wa suna don girmama Salah.

Salah, mai shekaru 33, yana dab da fara kakar wasa ta tara a Liverpool, inda dan wasan ya ci kwallo 245 a wasa 402 da ya buga a gasar lig da kofuna tun bayan da ya koma ƙungiyar a shekarar 2017.

Tauraron ɗan wasan ƙwallon ƙafar ya zama na farko daga Masar da ya lashe duk wata gasar Ingila da kuma ta zakarun Turai tare da Reds, amma har yanzu bai ɗanɗana nasara a ƙasarsa ba.

Yayin da ake shirin fara gasar cin kofin nahiyar Afirka a watan Disamba da kuma ta duniya a 2026, BBC Sport ta ziyarci Masar domin gano abin da Salah ke fata ga al'ummar ƙasar da ta kai miliyan 115, da kuma yadda wani ƙaramin yaro ya zama abin alfahari na ƙasar.

"Har yanzu ina tuna farin cikin mahaifina idan na kalli Salah," in ji Lamisse El-Sadek, a ɗakin likitan haƙora da ke gabashin Alƙahira. "Bayan Salah ya koma Liverpool, muna kallon kowane wasansa a talabijin tare."

An sanya wa gidan cin abin da shan gahawa sunan asalin sana'ar tsohon mutumin, kuma yanzu shi ne inda magoya bayan Liverpool ke taruruwa don kallon wasanni akan babban allo.

Lamisse tana sanye da rigar Liverpool mai ɗauke da sunan mahaifinta a baya. "Ya rasu shekaru biyu da suka wuce," in ji ta.

"Kowane wasa na Liverpool yana daga cikin sa'o'i biyu mafi farin ciki a gidanmu da muke yi, kowane mako kuma ko da na rasa wasu wasan saboda makaranta ko aiki, mahaifina yakan yi min saƙon taya murna na minti ɗaya.

"Salah bai fito daga gidan gata ba, haƙiƙa ya yi aiki tuƙuru da sadaukarwa, hakan ya sa ya kai inda yake a yanzu, yawancinmu muna ganin kanmu kamar shi."

'Kowanne yaro yana son ya zama kamar Salah'

Ƙaramin ƙauyen Nagrig na noma ne a gefen kogin Nilu a Masar yana dauke da korayen filawar jasmine da kankana. Ana kuma zirga-zirga a ƙananan tituna tare da shanu da jakuna tare da motoci, babura da keken doki da sauran su.

A nan ne ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan gaba a duniya, wanda aka fi sani da 'Sarkin Masar', ya kwashe shekarunsa na farko.

El-Saadany, wanda ya kira kansa a matsayin kocin Salah na farko, ya kara da cewa "Iyalan Salah su ne tushe da sirrin nasararsa tun daga lokacin da yake shekara takwas da haihuwa."

"Har yanzu suna zaune a nan tare da dabi'u masu ƙyau da mutuntawa. Wannan shi ne dalilin da ya sa mutane ke son su sosai."

Cibiyar matasan ta sami haɓaka mai ban sha'awa kwanan nan aka daga darazarta don girmamawa daya daga ɗan ƙauyen da ya fi shahara,

''Iyalan Salah sun yi sadaukarwa tun lokacin da yake ɗan karami da cewar ''El-Saadany, wanda ke tsaye kusa da wani katon hoton da aka rataye tare da daya daga cikin kwallayen da ya zura a raga, an kuma nuna Salah yana dauke da kofin gasar zakarun Turai,''

"Sun kasance masu goyon baya sosai tun daga farko, musamman mahaifinsa da kawunsa, wanda a zahiri shine shugaban wannan cibiya."

Bajintar Salah ta kasance a ko'ina a Nagrig, inda yara ke gudu sanye da rigar Liverpool ko ta tawagar Masar da sunan dan wasan da lambarsa a bayansu.

Akwai wani bango dauke da zanen Salah a wajen tsohuwar makarantarsa, yayin da dan wasan yana murmushi.

A tsakiyar Nagrig akwai shagon aski inda matashi Salah ke zuwa yin aski bayan atisaye.

Ahmed El Masri ya ce "Ni ne na kirkiro masa wannan aski da yake yi har da na gemunsa."

"Abokansa sukan ce masa kar a yi masa aski a nan domin mu mutanen kauye ne , amma kullum sai ya zo wurina. Washegari sai abokansa su yi ta mamaki [ganin kyawun da yayi] sai su tambaye shi, wane ne wanzamin?

Mai askin ya tuna yana kallon gwanintar Salah a cibiyar samari da ke kan titunan kauyen.

Ya kara da cewa "Babban abin da na fi tunawa shi ne, lokacin da muka buga wasan PlayStation, Salah zai zaɓi Liverpool." "Sauran yaran za su zaɓi Manchester United ko Barcelona, amma shi dai ko yaushe yana Liverpool.

"Dukkan yaran da ke zaune a ƙauyen yanzu suna son su zama kamar shi."

Salah ya samu ilimin ƙwallon kafa saboda shekaru shida da ya yi a ƙungiyar Arab Contractors da ke birnin Alƙahira, wanda aka fi sani da Al Mokawloon.

Ya kasance tare da su yana da shekaru 14 kuma labarin yadda aka ba Salah izinin barin makaranta da wuri don yin tafiye-tafiyen yau da kullun, yana ɗaukar sa'o'i masu yawa, yana atisaye da buga wa Arab Contractors tamaula, hakan ya sa ya yi fice a Masar da wajen kasar.

Tafiya a cikin bas don halartar atisaye

Wasu fasinjoji sun je jikin mota kirar Suzuki mai daukar mutum bakwai a gefen Nagrig suna ta shawarwari.

"Za su shiga ne ko kuwa?"

Wannan ba bas ba ce da ke aiki kan ƙa'ida ko lokaci da zarar ta cika, direban zai tuka ya ƙara gaba.

Tun yana matashi wannan tashar motar bas ta kasance inda Salah ya fara doguwar tafiya zuwa atisaye a Arab Contractors. El-Saadany ya ce "Tafiya ce mai wahala kuma tana da tsada sosai."

Lokacin da muka hau motar bas din, sai aka matse mu a kujerar baya tare da wata uwa da 'ya'yanta biyu, muka nufi hanyar wani gari mai suna Basyoun, tasha ta farko a tafiyar Salah ta zuwa Alƙahira.

Daga nan sai ya hau wata motar bas zuwa Tanta, kafin ya sake canjawa zuwa tashar motar Ramses da ke birnin Alkahira, sai ya kara hawa wata motar kafin daga bisani ya isa inda yake.

Bayan kammala atisaye haka zai sake biyu hanya domin ya koma Nagrig tare da shiga bas da yawa a duk lokacin da zai je atisaye ya koma gida.

Fararen ƙananan motocin bas ɗin da ke kewaya tituna a kowane sa'o'i na ɗaya daga cikin abubuwan farko da za ka gani a lokacin da kuka isa Alkahira, cike da matafiya suna zirga-zirga.

"Wadannan motocin suna ɗaukar kusan kashi 80% na matafiya a cikin birni mai ɗauke da mutane sama da miliyan 10," kamar yadda ɗan jaridar Masar Wael El-Sayed ya yi bayani.

"Akwai dubban motocin da ke aiki dare da rana a koda yaushe,''

Ƙananun tafiye-tafiye zuwa Basyoun suna da wahala a cikin yanayi mai zafi da rashin jin daɗi a bayan motar bas, don haka za ku iya tunanin yadda ƙalubalen tafiya mai tsawo, sau da yawa a mako da Salah ya fuskanta.

Kocin da ya fara sa Salah a wasan farko a duniya ya yi imanin cewa hakan ya bai wa dan wasan tunanin samun nasara a matakin ƙoli.

Hany Ramzy ya ce "Fara taka leda a matsayin dan wasan kwallon kafa a nan Masar abu ne mai matukar wahala."

Ramzy yana cikin tawagar Masar da ta fuskanci Ingila a gasar cin kofin duniya a 1990 kuma ya shafe shekaru 11 yana taka leda a Bundesliga.

A watan Oktoban 2011 a matsayin kocin riƙon kwarya na Masar ya fara amfani da Salah.

Ya kuma kasance mai horar da 'yan wasan Masar 'yan kasa da shekara 23, inda Salah ya buga gasar Olympics ta London a 2012.

Ramzy ya kara da cewa "Na hau bas karo da yawa na yi tafiyar kilomita biyar ko shida kafin in isa kulob dina na farko Al Ahly kuma a lokacin mahaifina ba zai iya sayamin takalmin kwallon kafa ba."

"Salah yana wasa a matakin kololuwa a shekaru da yawa, saboda irin wannan rayuwa tana gina ƙwararrun 'yan wasa."

Tafiya zuwa birnin Alkahira akan daya daga cikin gada mafi yawan hada-hada da wani katafaren allo mai dauke da tallan Ice Cream kusa da hoton Salah da aka yi rubutu da Larabaci da cewar 'Shukran' wato mun gode.

Kusa da shi kuwa wani ofis ne na Diaa El-Sayed, ɗaya daga cikin masu horar da 'yan wasan da suka yi tasiri a farkon rayuwar Salah.

Shi ne kocin lokacin da Salah ya fara taka rawar gani a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 a 2011 da aka yi a Colombia.

''A lokacin kasar ba ta da kwanciyar hankali, an yi juyin-juya hali, don haka shirya gasar ta yi mana wahala," in ji mutumin da kowa ke kira da 'Captain Diaa'.

"Mun je tare da Salah, abin da ya fara fice shi ne gudunsa da kuma maida hankali, ya kan yi da duk shawarar da aka ba shi sosai, babu jayayya da kowa, kullum yana aiki tukuru, ya cancanci matakin da yake kai a yanzu haka."

'Captain Diaa' ya tuna lokacin da ya gaya wa matashi Salah cewa ya nisanta kansa daga zaman a yanken gidansu na bugun fanareti kuma ya mai da hankali kan kai hare-hare.

"Sannan a karawar da Argentina, waje ya dawo ya ƙare a cikin akwatin yadi 18 kuma ya ba da bugun fanariti," in ji shi, yana dariya.

''Sai gashi a wasa da Argentina ya dawo tsare gida sai ya jawo fenariti.

"Na gaya masa ka da ka tsare gida, mai ya sa ka dawo cikin dairarmu? Ka da ka koma mai tsare baya.

"Bayan da Liverpool ta lashe kofin Premier a kakar wasan da ta wuce, na ji yana cewa Arne Slot ya ce masa kar ya rinƙa komawa tsare baya. Amma ya ce ni ne koci na farko da na fara faɗa masa hakan."

Babban jakadan Masar

Salah dai ya shafe shekaru 14 yana buga wa babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar wasa, kuma muhimmancinsa ga kasar Masar ya sa wasu manyan jami'an gwamnati suka rika shiga tsakani a lokacin da ya ji rauni.

Dr Mohamed Aboud, likitan tawagar kasar ya ce "Na yi waya da ministan lafiya na Masar, a daidai lokacin da Salah ya samu mummunan rauni a kafadarsa a karawar da Liverpool da Real Madrid a wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai a 2018, lamarin da ya sa ake tunanin ba zai iya buga gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Rasha makonni kadan ba.

"Sai na ce masa ka da ya damu, komai zai tafi daidai."

Da yake magana daga asibitinsa na jinya da ke yankin Maadi a babban birnin Masar, Dr Aboud ya kara da cewa: "Ni karami ne amma sai aka yi tamin matsin lamba daga cikin kasar da har abin ya yi tsanani.

"Na samu kira daga mutane da yawa da ke kokarin taimakawa, daya daga cikin mambobin kwamitinmu ya shaida min cewa a yanzu ina daya daga cikin manyan mutane a duniya baki daya.

"Wannan lamarin ya canza ni a matsayina na mutum da sana'ata."

Salah ya murmure ya buga wasanni biyu daga cikin ukun da kasarsa ta buga na rukuni, inda Masar ta yi fice daga gasar bayan ta sha kashi a hannun Uruguay da Rasha da kuma Saudi Arabiya.

"Ina son na sanar da ku cewa Salah na da hannu a cin kwallo a fafatawarmu ta neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2018," in ji tsohon mataimakin kocin Masar Mahmoud Fayez a gidansa da ke wajen birnin Alkahira.

Salah ya ci fenariti a minti na 95 a karawar da Congo a birnin Alexandria, inda ta yi nasara da ci 2-1, hakan ya bai wa Masar damar shiga gasar cin kofin duniya, duk da saura wasa daya a karon farko cikin shekaru 28.

A wasan ne Salah ya farke ciwa Masar kwallo kafin Congo ta rama minti uku a tashi daga wasan.

Daga nan aka samu bugun fenariti, inda Salah ya zama gwarzon kasar.

Fayez ya ce "Ka yi tunanin, al'ummar kusan miliyan 120 suna jiran wannan lokacin na bugun fenariti a minti na 95 kuma Salah ya buga ya ci kwallon.

Ya zura kwallo a raga kuma ya sanya mun yi alfahari. A cikin dakin canja tufafi sai ya fara taka rawa, ya rungume kowa yana ihun cewa mun yi, mun yi, bayan shekaru 28, mun yi."

A birnin Alkahira akwai wata makarantar koyar da kwallon kafa da ake kira 'The Maker', wadda tsohon dan wasan Tottenham da Masar Mido ya kafa kuma yake gudanarwa, wanda ke fatan samar da 'yan wasan da za su bi sahun Salah.

"Na buga wa tawagar kasar wasa a gaban mutane 110,000 a lokacin ina da shekaru 17 kacal, dan wasa mafi karancin shekaru da ya wakilci Masar," in ji Mido. "Ina son jin cewa mutane sun dogara da ni da kuma Salah."

A lokacin da muka kai ziyara, darasi na aji ga matasa 'yan wasa game da tunanin da ake buƙata don zama ƙwararrun yan kwallo.

A ƙarƙashin sunan Salah a kan allo, ɗaya daga cikin masu horar da 'yan wasan ya rubuta "Tarbiya, sadaukarwa da kwarin gwiwa".

Mido ya kara da cewa "Dalilin da yasa Salah yake inda yake yanzu shi ne saboda yana tunanin kan yadda zai cimma burinsa a koda yaushe."

"Shi ne babban jakada a Masar da kuma 'yan wasan Afirka, ya sanya kungiyoyin Turai girmama 'yan wasan Larabawa, abin da Salah ya yi ke nan.

"Ina ganin da yawa kungiyoyin Turai a yanzu idan suka ga matashin dan wasa daga Masar sai su tuna da Salah. Ya sanya matasan 'yan wasa yin mafarki zama kamar shi."

Salah bai manta da mafari ba

Idan muka koma Nagrig kuma mun haɗu da Rashida, 'yar shekara 70 da ke sayar da kayan lambu daga ƙaramar rumfa. Ta yi magana ne game da yadda Salah ya canza rayuwarta da kuma rayuwar daruruwan mutane a kauyen da aka haife shi kuma ya girma.

Rashida ta ce "Mohamed mutumin kirki ne, mai mutunci da kirki, kamar kani ne ne a wurinmu."

Ta kasance daya daga cikin mutane da dama a kauyen da suka ci gajiyar ayyukan agaji na Salah, wanda ke mayar da hankali ga faranta ran wurin da ya fara har zuwa kwararren dan wasa.

Kazalika bayan agajin da ke taimaka wa mutane irinsu Rashida, Salah ya samar da wani sabon gidan waya domin yi wa al'ummar yankin hidima, sashen daukar marasa lafiya, cibiyar addini da kuma bayar da tallafin fili na tashar ruwa da sauran ayyuka.

Lokacin da Liverpool ta lashe kofin Premier League a karo na 20 a bara, magoya bayanta sun hallara a wani wurin shan magani da ke Nagrig don kallon talabijin tare da murnar shahararren wanda ya fito daga kauyen.

Ko za a yi karin bukukuwa a kauyen Salah a 2025-26?

Duk da taimakawa Liverpool ta lashe kofin Premier a 2019-20 da 2024-25, har yanzu dan wasan bai dagawa kasarsa kofi ba.

'Kafin zamain Salah, yan baya sun lashe kofin Afirka sau uku a jere tsakanin 2006 zuwa 2010. Tun daga wannan lokacin ne suka sha kashi sau biyu a wasan karshe, da Kamaru a shekarar 2017 da Senegal a shekarar 2021, wanda aka yi a farkon shekarar 2022.

Yayin da gasar cin kofin Afrika ta 2025 za ta fara ranar 21 ga Disamba - watanni shida kafin gasar cin kofin duniya - shin ko Masar na ganin cewa dan wasan mai shekaru 33 a yanzu yana bukatar ya taka rawar gani a fagen kasa da kasa?

"Salah ya riga ya yi abin bajinta, shi ne dan wasan kwallon kafa na Masar mafi shahara a tarihinmu," in ji Mido.

"Ba lallai ne ya gamsar da kowa da komai ba, gwarzon Liverpool ne kuma gwarzon Masar."