Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Al-Hilal za ta ɗauki Salah, Tottenham na harin Mateta
Ƙungiyar Al-Hilal da ke Saudiya ta ce za ta ɗauki dan wasan Liverpool Mohamed Salah a watan Janairu mai zuwa. (Sun)
Liverpool na son maye gurbin Salah da ɗan wasan Bournemouth Antoine Semenyo, mai shekaru 25. (Express)
Da alama sun saki jikinsu ne kan Salah, wadda ke ci gaba da tattaunawa da MLS da ke San Diego. (GiveMeSport)
Tottenham na sa ido kan ɗan wasa mai shekaru 28 Jean-Philippe Mateta, bayan da har yanzu ba a tsayar da magana ba kan kwantiraginsa ba da Crystal Palace. (Football Insider)
Ɗan wasan Crystal Palace Adam Wharton, na son buga gasar Champions League a ƙungiyar da zai koma nan gaba, yayin da Manchester United ke son ɗaukar sa. (Mirror)
An sanar da Liverpool da Barcelona cewar za su iya ɗaukar ɗan wasan Atalanta Ederson, kan fam miliya 50, a watan Janairu. (Football Insider)
Arsenal na gogayya da Real Madrid wajen ɗaukar ɗan wasan Turkiya Kenan Yildiz a watan Janairu, sakamakon dakatar da tattaunawa kan tsawaita kwantaraginsa da Juventus. (Goal)
Roma ce kan gaba wajen siyen ɗan wasa Joshua Zirkzee, mai shekaru 24, daga Manchester United. (Football Insider)
Newcastle United da West Ham United na cikin jerin ƙungiyoyi da ke son ɗauko Axel Disasi daga Chelsea(Caught Offside)
Manchester United ta ce za ta ɗauko Mouhamed Dabo, mai shekaru 17 don ƙara ƙarfafa tsakiyar ƙungiyar. (MEN)