Mece ce makomar Liverpool idan ba Salah?

Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da ƙungiya irin Real Madrid ke tunƙaho da zaratan 'yanwasan gaba huɗu - Kylian Mbappe da Jude Bellingham da Vinicius Jr da kuma Rodrygo, waɗanda ka iya dama lissafin duk wata ƙungiya da ta yi karo da ita, shin ƙungiya irin Liverpool ya za ta kasance idan yau ba ta tare da tauraron ɗan gabanta Mohamed Salah?

Real Madrid ka iya dogaro da kowanne daga cikin zaratan nata huɗu a ranar da take cikin buƙata kuma ya fitar da ita kunya, kamar yadda Mbappe ya ci ƙwallo uku da ya sallami Manchester City (6-3 jimilla gida da waje) ya kuma kai ƙungiyarsa matakin ƙungiyoyi 16 na gasar Zakarun Turai a ranar Laraba a filin wasa na Estadio Santiago Bernabeu.

Wannan tambaya da ake yi kan Liverpool idan ba ta tare da Salah ta ƙara bayyana bayan karawar ƙungiyar a gidan Aston Villa inda suka yi canjaras 2-2.

Tauraron na Masar ne ya fara ɗaga raga a karawar ta Laraba inda a minti na 29 ya ci wa Liverpool ƙwallo da taimakon Diogo Jota, kafin kuma Y. Tielemans ya farke a minti na 38 wannan kuwa duk da cewa ba ya kan ganiyarsa a wasan na ranar Laraba.

Sai kuma O. Watkins ya sa Aston Villa a gaba ana shirin tafiya hutun rabin lokaci da ƙwallo ta biyu, wadda kuma T. Alexander-Arnold ya farke wa Liverpool a minti na 61 da taimakon Salah.

Ƙwallon da Salah ya ci da kuma wadda ya bayar aka farke sun sa a yanzu yana da ƙwallo 39 da yake da hannu a ciki a wannan kakar a Premier a bana - inda ya ci ƙwallo 24 ya kuma taimaka a 15.

Haka kuma da waɗannan alƙaluma Salah ɗin ya zama ɗanwasa na biyar da ya ci ƙwallo fiye da 15 ya kuma bayar da taimako aka ci 15 a Premier a bana, inda ya shiga rukunin su Eric Cantona, da Matt le Tissier, da Thierry Henry da kuma Eden Hazard, kuma shi har yanzu yana ci gaba da taka leda.

Salah ya kasance ɗanwasa na farko a gasar Premier da ya ci ya kuma bayar aka ci a wasanni daban-daban har goma a kaka ɗaya.

Sannan shi ne ɗanwasa na farko da ya yi haka a ɗaya daga cikin manyan gasar Turai biyar tun bayan Lionel Messi da ya yi wannan bajinta a kakar 2014-15, inda ya yi wa Barcelona hakan da ƙwallo 11.