Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Joe Biden ya ɓata rawarsa da tsalle
- Marubuci, Anthony Zurcher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent
- Lokacin karatu: Minti 8
Yayin da Mista Biden ke jawabi a babbar majami'ar ƙasa lokacin bikin jana'izar tsohon shugaban Amurka, Jimmy Carter, shugaban Amurkan mai barin gado Joe Biden ya tuna da irin gudumawar da marigayin ya bayar wajen gina Amurka.
Mista Biden ya yi jawabin ne a gaban tsoffin shugabannin Amurka uku, Bill Clinton da George W Bush da kuma Barack Obama – da kuma sabon shugaban ƙasar Donald Trump.
Kowa ya sa ran cewa marigayi Jimmy Carter ya yi abin da zai sa Amurkawa su sake zaɓen shi a wa'adin mulki karo na biyu.
Biden - wanda wa'adin mulkinsa ya ƙare ranar 20 ga watan Janairu - ya yi jawabin jinjina ga marigayi Carter, takwaransa shugaban Amurka da ya yi wa'adin mulki ɗaya tal.
"Da dama na kallon sa matsayin shugaban dauri, amma a haƙiƙanin gaskiya ya yi aiki a rayuwarsa ta duniya,'' in ji Biden.
Ya kuma ambato ƙoƙarin marigayin na haɓaka ayyukan kare yancin ɗan'adam da gudumawarsa wajen wanzar da zaman lafiya da taƙaita yaɗuwar makaman nukiliya, da kuma ƙoƙarinsa a fannin inganta muhalli.
"Ina fatan tarihi zai ce na zo kuma ina da shirin farfaɗo da tattalin arziki tare da sake inganta ƙimar shugabancin Amurka a idon duniya'', kamar yadda Biden ya faɗa a wata hira da gidan talbijin.
"Kuma ina fatan tarihin zai ce na yi hakan da kyakkyawar manufa da mutuntawa, wannan shi ne abin da ke a raina''.
Dangane da kalaman nasa, abu ne da ake ci gaba da tattaunawa don tabbatar da haka - amma ya fice daga Fadar White House yayin da kimarsa ta ragu sosai a ƙasar.
Ya zuwa saukar sa daga mulki, kashi 39 cikin 100 ne kawai na Amurkawa ke ganin cewa tsohon shugaban ƙasar ya taka rawar gani a zamaninsa, kamar yadda ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta Gallup ta nuna.
A farkon wannan makon ne mutumin da ya kayar a 2020 ya sake dawowa kan karagar shugabancin ƙasar, inda ya kawo ƙarshen mulkin Biden.
Biden ya gudanar da ayyuka kama daga ɓangaren zuba jari da ababen more rayuwa da samar da wasu dokoki ta hanyar majalisa duk kuwa da ɗan ƙaramin rinjayen da yake da shi a majalisar.
Ya kuma ƙarfafa tare da faɗaɗa kungiyar Nato, tare da naɗa manyan alƙalan ƙasar, amma duka waɗannan a iya cewa gazawar tasa ta ɓoye su.
Afghanistan ce farkon 'matsalarsa'
Abu na farko da ya fara fito da gazawar Biden shi ne janye dakarun Amurka daga Afghanistan a watan Agustan 2021.
An cimma yarjejeniyar janyenwar a watannin ƙarshe na mulkin gwamnatin Trump, amma sai Biden ya goyi bayanta, duk kuwa da gargaɗin yin hakan daga wasu mashawartan ayyukan soji.
Fargabar da aka yi ta janyewar ta tabbata, yayin da ƙasar ta faɗa cikin tashin hankali.
Zuwa ƙarshen watan Janairun 2025, farin jinin shugaban ya ragu zuwa kasa da kashi 50 kamar yadda ƙuri'ar jin ra'ayi ta Gallup ta nuna, farin jinin da har ya sauka bai ƙara samun irin sa ba.
Haka batun yake a cikin ƙasa, inda shugaban ya fara fuskantar matsala, zuwa bazarar shekarar hauhawar farashi ta ƙaru da kashi 5 a karon farko cikin shekara 30.
A lokacin, sakatariyar baitul malin ƙasar, Janet Yellen ta ce ta yi imanin matsalar ta ''wucin-gadi'' ce, kamar yadda shi ma Biden ya bayyana ta.
To sai dai Larry Summers tsohuwar mai bai wa Obama shawara kan tattalin arziki ta yi jayayya da kalaman nasu.
A lokacin da hauhawar farashin ta kai maƙura a shekarar, inda ta kai kashi 9.5 cikin ɗari a watan Yunin 2022, Yellen da Biden sun amince cewa sun yi kuskuren lissafi.
Kasa magance kwararar baƙin haure
Gwamnatin Biden ta kuma riƙa jan ƙafa dangane da daidaita al'amura bayan annobar korona, musamman dangane da tuɗaɗar ƴan ci-rani ta kan iyakar ƙasar da Mexico.
An riƙa kallon matakin a matsayin koma-baya kan shirin da gwamnatin Republican ta yi na sauya wa ƴan ci-rani wuri wuraren zama.
Ƙarancin kayan gwajin korona, da ƙarin farashin ƙwai, da sabuwar dokar zubar da ciki, da yaƙoƙin Ukraine da Gaza.
'Tsohon da ya fara gajiya'
A wasu lokutan martanin da gwamnatinsa ke yi kan wasu abubuwa ana jin su bambarakwai.
A lokacin wata hira da shi a cikin wani shirin talbijin kan ƙaruwar samar da mai a Amurka don rage farashin gas a watan Nuwamban 2021, sakatariyar makamashin ƙasar ta gwamnatinsa, Jennifer Granholm da dariya ta amsa tambayar.
"Wannan abin mamaki," in ji ta.
Biden – wanda a baya aka danganta da mai ƙwazo - ya kasa magance matsalolin Amurkawa. Haka kuma alamun tsufa sun bayyana a jikinsa.
"Idan ina kallon Biden na magana, nakan ce ikon Allah, wannan mutumin na da abin mamaki,'' in ji wani babban jami'in fadar White House da ya shafe shekaru yana aiki a fadar, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa.
Cika gwamnati da tsoffin abokansa
A lokacin gwamnatin, Biden ya keweye kansa da tsoffin ma'aikatan gwamnati. Sakataren harkokin wajen gwamnatinsa, Antony Blinken, ya kasance daya daga cikin manyan mashawartansa tun yana majalisar dattawa.
Ya kuma naɗa Merrick Garland, shugaban kotun ɗaukaka ƙara da ya raba gari da Barack Obama a 2016 a matsayin babban lauyan gwamnatinsa.
Sannan ya zaɓi Yellen, a matsayin sakataren baitul mali, wanda a baya ya shugabanci hukumar tara kuɗaɗen haraji ta ƙasar.
A cikin fadar white House, Biden ya zaɓi Ron Klain - wanda ya yi aiki da shugabannin ƙasa na jam'iyyar Dimokrats na tsawon gomman shekaru - a matsayin shugaban ma'aikatan fadarsa, haka kuma ya zaɓi Mike Donilon, wani tsohon abokin nasa a matsayin babban mashawarcinsa.
Buƙatar sake tsayawa takara
A ranar 5 ga watan Afrilun 2023, Biden ya ayyana matakinsa na sake tsayawa takarar shugabancin Amurka cikin wani saƙon bidiyo da ya fitar inda ya yi gargadin cewa manufar Trump kan tatalin arziki ka iya yin barazana ga Amurka.
Watanni bayan haka ya sake fitar da wasu jerin gargaɗi kan haɗarin da Trump zai yi wa dimokUradiyyar Amurka.
Haka kuma Biden ya sha faɗa wa hadimansa cewa yana da yaƙinin cewa shi ne zai iya kayar da Trump, kamar yadda ya yi a baya, kuma zai sake yi, kuma duka hadiman nasa sun yi ta kauce wa tambayoyi kan ko Biden zai iya.
"Ni ba ƙaramin yaro ba ne'' in ji Biden, kamar yadda ya faɗa a wani gangamin yaƙin neman zaɓensa.
Hamas da Hunter da kuma faɗuwar Kamala
A shekarun ƙarshe na mulkin Biden ya sake gamuwa da wani cikas a gwamnatinsa, bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta ƙaddamar a Isra'ila, ya gaggauta kiran Isra'ila da kada da ɗauki matakin da ya wuce ƙima, ta hanyar zubar jini.
Haka nan kuma mamayar da Rasha ta yi wa Ukriane ta sa shugaban ya karkatar da hankalinsa kan harkokin ƙasashen waje, saɓanin Ukraine, wadda a lokacin Biden ya samu nasarar haɗa kan ƙasashen Yamma don nuna adawa da mamayar, amma ci gaba da goyon bayan Isra'ila ya sa shugaban ya rasa farin jinisa a wasu sassan ƙasar.
A lokaci guda kuma, Biden ya fuskanci matsalar shari'ar ɗansa Hunter Biden.
Cikin watan Yuni aka gurfanar da shi aka kuma same shi da laifin mallakar bindiga, sannan kuma aka zarge shi da laifukan saɓa wa haraji, lamarin ya yi matuƙar taɓa Biden.
Haka nan kuma kayar da Kamala da Trump ya yi, ta ƙara fito da gazawar Biden, saboda an yi ta dangata faɗuwar ta da rashin janyewar Biden a kan lokaci.
Yaya kimar Biden za ta kasance idan a ce tun da farko bai bayyana buƙatar tsayawa takara ba?
Da babu kausasan kalamai ko yin muhawara da Trump wadda ta ƙara fito da gazawarsa a fili.
Sannan za a samu fitowar masu takara daga jam'iyyar Dimokrats masu yawa.
"Da za a gudanar da zaɓen fitar da gwani, kuma wanda ya yi nasara zai samu isasshen lokacin shiryawa yaƙin neman zaɓe" in ji Ms Estrich.