Yadda suɓul-da-bakan da Joe Biden ke yi ke tsorata ƴan Democrat

    • Marubuci, Anthony Zurcher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent

Shugaba Joe Biden ya tsaya a gaban taron manema labarai ranar Alhamis da daddare inda ake hasashen zai tattauna batutuwan da suka haɗa da batun takararsa da fatansa na neman tazarce da kuma rayuwr siyasarsa baki ɗaya.

To sai dai kuma idan dai waɗannan batutuwa su ne ake sa ran zai magantu a kai, bai yi hakan ba a taron na awa ɗaya wanda shi ne abu na ƙarshe na taron ƙolin kungiyar tsaro ta Nato, inda ya ambaci shugaban Ukraine Zelensky a matsayin shugaba Putin na Rasha, a taruka daban-daban.

Taron manema labaran dai shi ne wani taro irinsa na farko da shi Joe Biden ya yi jawabi ba tare da riƙe takarda ba tun bayan muhawarar da ya yi da abokin takararsa, Donald Trump, abin da ya janyo aka yi ta kiraye-kirayen ya hakura da takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Democrat.

Mista Biden dai mai shekaru 81 ya fuskanci tambayoyi babu kaƙƙautawa dangane da shekarunsa da kuma ƙarfin iya ci gaba da jagorantar Amurka a wani wa'adin wanda hakan ya fito fili a bayan muhawar da ya yi da Trump.

To sai a wannan taron na manema labarai, ya yi watsi da tunanin da ake yi kan takararsa kuma ya sha alwashin cewa yana yaƙi ne domin kare abubuwan alkairi da ya gina a ƙasar da kuma ci gaba da yin su da ya fara a 2021 lokacin da ya kama aiki.

“Idan na yi ƙasa a gwiwa na ƙasa yin aikin, hakan alama ce da ke nuna ba zan iya ba," kamar yadda ya ce. "Amma kuma babu alamun hakan har kawo yanzu."

Ƴan mintuna bayan kammala taron manema labaran sai ƴan majalisar wakilai na jam'iyyarsa ta Democrat suka yi kiraye-kirayen da ya haƙura da takarar kamar yadda gomman wasu a baya suka yi kiran.

A lokacin taron manema labaran dai, mista Biden ya yi suɓul-da-baka da zai daɗe a zuciyar duk wanda ya kalli taron.

A amsar tambayar da aka yi mas ata farko, mista Biden ya kira mataimakiyarsa, Kamala Harris da "mataimakin shugaban ƙasa Trump"

Hakan kuwa ya faru ne awa guda bayan wani suɓul-da-bakan a lokacin taron ƙungiyar tsaro ta Nato, inda ya bayyana shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky a matsayin "shugaba Putin" wani abu da ya janyo ɗaukewar numfashin masu kallo.

Sai dai mista Biden ya gyara suɓul-da-bakan da yi na farko inda ya yi sauri ya gyara amma dai na biyun mai gano kuskuren da ya yi ba duk da yadda ƴan jarida da jami'ansa suka nuna mamakinsu.

Suɓul-da-bakan da shugaba Biden ya yi dai sun zamo waɗansu abubuwan da ke ƙara jefa faragaba a zukatan ƴan jam'iyyarsa dangane da abubuwan da ka iya fitowa daga bakinsa a wasu tarukan na gaba.

Wani abu dai ya fito fili shi ne yadda mista Biden ya zama wani jarumi wajen tsayawa kai da fata cewa zai iya takarar neman wa'adin na biyu. Sannan kuma wani abun birgewa shi ne yadda yake dariya da murmushi a lokacin da ƴan jarida ke zabga masa tambayoyi.

Mista Biden dai ya bayyana a fili cewa zai wuya a ƙwace takarar nan daga hannunsa. Mutumin mai shekaru 81 wanda lokaci zuwa lokaci ya kan riƙe kan abun magana da hannu biyu ya kuma tsaya kai da fata cewa shi ne "ɗan takarar da ya fi kowanne dacewa" kuma abin da hakan ke nufi shi ne ba lallai ya bar takarar.