Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jagoran juyin mulkin soji na son zama sabon zaɓaɓɓen shugaban Gabon
- Marubuci, Paul Njie & Natasha Booty
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Libreville & London
- Lokacin karatu: Minti 3
Jama'a na tururuwa domin su je su kaɗa ƙuri'a domin zaɓen shugaban ƙasar Gabon, inda a karon farko a gomman shekaru babu wani daga gidan iyalan Bongo da ke takarar.
An hamɓare tsohon shugaban ƙasar Ali Bongo daga mulki wata 19 baya a juyin mulkin da Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya sauya kundin tsarin mulkin ƙasar don ya tsaya takara a zaɓen na ranar Asabar, ya jagoranta
Akwai jimullar ƴantakara takwas da suka tsaya zaɓen - ciki har mace ɗaya Gninga Chaning Zenaba.
Sauran ƴantakarar sun haɗa da Firaministan ƙasar Alain Claude Bilie-by-Nze, wanda ya riƙe wannan muƙami a lokacin mulkin Bongo, da kuma wasu manyan ƙusoshin tsohuwar jam'iyya mai mulki PDG, Stéphane Germain Iloko da Alain Simplice Boungouères.
Za a iya fara bayyana sakamakon zaɓen a ranar Lahadi, yayin da jami'ai ke ci gaba da ƙirga ƙuri'un har zuwa cikin mako na gaba.
Kimanin mutum miliyan ɗaya ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri'a a cikin Gabon da ƙasashen waje inda 'yan ƙasar suke.
Ƴar ƙaramar ƙasar ta yankin tsakiyar Afirka wadda ke da ɗimbin arziƙin mai da itacen katako, tana da yawan jama'a miliyan biyu da rabi ne.
Duk da ɗimbin arziƙin da take da shi kusan kashi 35 cikin ɗari na al'ummarta suna rayuwa ne cikin katutun talauci - na rayuwa a ƙasa da dala 2 a rana.
A lokacin yaƙin neman zaɓe na mako biyu, yawancin ƴantakarar sun fi bayar da fifikon tallata manufofinsu ga al'ummar cikin ƙasar, inda suka taƙaita gangaminsu a babban birnin ƙasar, Libreville.
Yayin da fastoci da manyan allunan tallata shugaban mulkin sojin ƙasar Oligui Nguema suka mamaye titunan babban birnin, kaɗan ake iya gani na abokan hamayyarsa a birnin.
"Zan zaɓi mai gina ƙasa ne, Oligui Nguema," - wani rubutu ke nan na goyon bayan jagoran shugaban mulkin sojin, a kan motar tasin wani mutum, Obame-Mezui, wanda ke ƙaunar jagoran, saboda ya, "zo da sababbin hanyoyin gudanar da al'amura - aiki ba surutu ba".
To amma masu sukar lamirin Oligui Nguema ɗin suna cewa, tun farkon-fari ya jagoranci tsarin mayar da mulki hannun farar hula da kuma zaɓe wanda ba a yi adalci ba a cikinsa, inda ya samar da sabon tsarin mulki da tsarin zaɓe da ya tsara domin ya yi nasara a zaɓen, duk da alƙawarin da ya yi tun da farko na mayar da mulki hannun farar hula.
Haka kuma an taƙaita shekarun haihuwa na ƴantakara ta yadda hakan ya hana ɗaya daga cikin manyan ƴanhamayyar Nguema, wanda ya fi farin jini Albert Ondo Ossa cancantar shiga zaɓen saboda yawan shekaru.
''Koma bariki,'' wannan shi ne taken sukar da mutumin da ake gani yana kusa da kusa wajen hamayya da Nguema, Bilie-by-Nze, yake yi wa shugaban mulkin sojan. Ɗanhamayyar na ganin shi ne sauyin da ƙasar ke buƙata, to amma kusancinsa da hamɓararriyar gwamnatin har yanzu na janyo masa suka daga wasu.
Bayan shekara 55 a jere ƙarƙashin mulkin Shugaba Omar Bongo da ɗansa Ali Bongo, al'ummar Gabon sun gaya wa BBC cewa abin da suke so kawai shi ne kawo ƙarshen almubazzaranci da dukiyar ƙasar da jefa ta cikin bashi da rashin aikin yi da suka jure tsawon mulkin iyalan Bongon.
"Fatanmu shi ne samun sabuwar ƙasar Gabon mai mulki na gaskiya da adalci, babu nuna wariya da bambanci kowa ya kasance yana da dama daidai-wa-daida,'' in ji wani mai zaɓe Noel Kounta. "Muna son ganin Gabon ta bunƙasa sosai tare da yalwa".
"Ina son shugaba mai zuwa ya mayar da hankali wajen samar da ƙarin ayyukan yi," in ji wata ƴar ƙasar mai ilimin haɗa magunguna Shonnys Akoulatele, mai shekara 30, wadda ta ce ba a biyanta albashin da ya dace a aikin da take yi a yanzu.
"Marassa aikin yi sun yi yawa sosai, ya kamata su nuna damuwa a wannan fanni, musamman a ɓangaren kamfanoni da harkokin ƴankasuwa."
Za a rufe rumfunan zaɓe da ƙarfe 06:00 na yamma agogon ƙasar wato 05:00 na yamma agogon GMT, na Asabar ɗin nan.