'Kawo ƙarshen tasirin iyalin Bongo a Gabon zai ɗauki lokaci'

Sabon Firaministan Gabon ya shaida wa BBC cewa kasar za ta sake gudanar da sabon zabe nan da shekaru biyu masu zuwa, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a makon daya gabata.

Sojojin da suka hambarar da shugaba Ali Bongo sun yi alkawarin gudanar da zabe mai sahihanci amma ba su fitar da jadawalin zaben ba.

Sai dai Raymond Ndong Sima ya shaida wa shirin Newshour na BBC cewa: Na fadi haka a cikin wani kundi da na wallafa cewa zaben zai gudana nan da shekaru biyu,”

Ya ce nan da kwanaki kalilan masu zuwa ne za a fitar da jadawali.

A ranar Alhamis aka nada Mista Sima a matsayin firaminista na riko, bayan da janarar Brice Oligui Nguema, wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi wa Mista Bongo, ya zama shugaban kasa na wucin gadi.

Tun shekarar 2009 Mista Bongo ya ke mulkin kasar ta tsakiyar Afrika mai arzikin man fetur bayan ya gaji mahaifinsa wanda ya shafe fiye da shekaru 40 kan karagar mulki.

Iyalin na da alaka mai karfi da Faransa, wadda ta yiwa Gabon mulkin mallaka.

Kasashen Afrika da na yamma ciki har da Faransa sun yi Alla-wadai da juyin mulkin.

Alamu sun nuna cewa farar hulha sun yi maraba da wannan sauyi, tare da taya Janarar Nguema murnar ranstar da shi a ranar Litinin.

Sai dai wasu sun nuna shakku kan za a samu sauyi a mulkinsa, idan aka duba cewa da dama daga cikin shekarun da ya shafe yana aiki, ya yi su ne a gidan Mista Bongo.

Da aka tambaye shin ko me ya sauya tun bayan juyin mulkin, Mista Sima ya shaida wa shirin BBC na Newshour cewa: “ Abin da ya sauya shi ne sojoji sun ki yi wa jama’a dukan tsiya kuma mun yi alkawarin cewa za mu dubi cibiyoyi da za su dawo cikin gwamnatin mulkin dimokradiyya.

" A cikin harkar siyasa, gwamma ka dauki dan abin da za ka iya samu."

Mista Sima ya kara da cewa zai dauki lokaci kafin Gabon ta sauya sheka daga gwamnatin da ta gabata.

" Ba za ku iya kawo karshen tasirin siyasar iyalin da suka shafe shekara fiye da 50 suna mulki a cikin rana daya ba saboda akwai tasiri na kai tsaye da kuma na bayan fage," in ji shi.

Sabon firaministan wanda ya taba aiki a karkashin Mista Bongo kafin ya tsaya takara domin kalubalantarsa a zabuka biyu ya yi watsi da batun gurfanar da tsohon shugaban kasar gaban kuliya.

An yi ta kiraye-kirayen gurfanar da Mista Bongo gaban sharia kan zargin almundahana

Sai dai Mista Sima ya ce: “ Ina ganin abin da ke jan hankalin mutane shi ne kada ayi masa sharia. Ba na tsamanin za a iya fara bincike a halin yanzu.”

Faransa ta gudanar da wani bincike na tsawon shekaru bakwai kan iyalin Bongo, wanda ya bankado dukiyoyi da suka hada da kadarori da motocin alfarma tara kafin aka dakatar da binciken a shekarar 2017.

Iyalin sun musanta zarge-zargen.

An saki Mista Bongo daga daurin ta-la-la da aka yi ma sa kuma sojoji sun ce zai iya ficewa daga kasar domin duba lafiyarsa.

A baya ya yi jinya a kasar Moroko sakamakon shanyewar bangaren jiki.