Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayani mai sauƙi a kan juyin mulkin ƙasar Gabon
Sojoji a Gabon sun ƙwace mulki kuma sun yi wa Shugaba Ali Bongo mai shekara 64 ɗaurin talala.
Juyin mulkin na zuwa ne, jim kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen da ya sake bai wa Ali Bongo nasara, duk da ƙorafe-ƙorafen 'yan adawa na cewa an tafka maguɗi.
Tun farko, an zaɓi Shugaba Bongo a 2009, bayan mutuwar mahaifinsa, Omar Bongo Ondimba, wanda ya mulki ƙasar tsawon shekara 41.
Gabon, ta kasance tsohuwar ƙasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka a Afirka da ta gamu da juyin mulkin sojoji a 'yan shekarun nan - bayan Mali da Burkina Faso da Guinea da kuma ta baya-bayan nan Nijar.
A nan ga abin da muka rigaya muka sani:
Me ya sa aka yi juyin mulki a Gabon?
Shugabannin juyin mulkin sun bayyana ƙin amincewa da sakamakon hukuma na zaɓen ƙasar, wanda ya ce Ali Bongo ne ya lashe da kashi biyu cikin uku na adadin ƙuri'un da aka kaɗa.
'Yan adawa a ranar Talata sun ce ɗan takararsu, Albert Ondo Ossa, shi ne halastaccen ɗan takarar da ya yi nasara, kuma sun yi zargin cewa an tafka gagarumin maguɗi.
Hafsoshin soja sun ce sun yanke shawarar "kare zaman lafiya ta hanyar kawo ƙarshen gwamnati mai ci", sun ƙara da cewa zaɓukan da aka yi "ba su cika sharuɗɗan sahihin zaɓe mai tsafta da ke ba da ikon damawa da kowa kamar yadda al'ummar Gabon suka yi ta fatan samu ba".
Bayan sanarwar, ɗaruruwan mutane ne suka hau kan tituna don yin maraba ga sojoji masu juyin mulki.
A ina Gabon take?
Gabon tana yankin gaɓar Yammacin Afirka, kuma an san ta da ɗumbin albarkar ma'adanan ƙasa - musamman man fetur da koko, sai dai fiye da kashi ɗaya cikin uku na al'ummar ƙasar na rayuwa cikin fatara.
Gabon, ƙasar da girmanta bai fi kwatankwacin Birtaniya ba, tana da yawan jama'a miliyan biyu da dubu ɗari huɗu, kuma kashi 90 na ƙasar, daji ne ya lulluɓe.
A ƙarƙashin Ali Bongo, Gabon ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta karɓi kuɗi don rage fitar da gurɓataccen hayaƙi mai ɓata muhalli da nufin kare dazukanta.
Shirin Kare Dazukan Afirka ta Tsakiya mai samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya (Cafi) ya ba da fiye da dala miliyan 17 - kashin farko na yarjejeniyar dala miliyan 150 da aka cimma a 2019.
Ƙasar wadda Faransa ta taɓa yi wa mulkin mallaka har zuwa 1960, shugabanni guda uku ne kawai ne suka mulke ta.
A ƙarƙashin mulkin shugaban ƙasar na biyu, Omar Bongo, Gabon ta yi alaƙa ta ƙuƙut da Faransa, ƙarƙashin wani tsari da aka yi wa laƙabi da "Francafrique", da gwamnatin Gabon za ta riƙa samun tallafin siyasa da na ayyukan soji a madadin wasu alfarmomin kasuwanci.
Sai dai alaƙar ta yi sanyi bayan ɗansa Ali ya ci zaɓe a shekara ta 2009 kuma hukomomin Faransa sun ƙaddamar da wani binciken cin hanci da rashawa na tsawon shekaru cikin kadarorin iyalin Bongo, ko da yake tun tuni aka watsar da batun.
Ƙarshen daular gidan Bongo
Sojoji sun bayyana a gidan talbijin na ƙasar Gabon, inda suka bayyana cewa sun ƙwace mulki.
Sun ce sun soke zaɓen da aka yi na ranar Asabar.
Hukumar zaɓe ta bayyana Bongo a matsayin wanda ya lashe zaɓe amma ƴan adawa sun ce su ne suka yi nasara.
Wannan matakin ya kawo ƙarshen shekara 53 da aka shafe iyalan gidan Bongo na mulki a ƙasar Gabon.
Sojoji 12 sun bayyana a talbijin inda suka sanar da soke zaɓen tare da rushe “duk cibiyoyin gwamnati”.
Ɗaya daga cikin sojojin ya sanar a gidan talbijin na Gabon 24 cewa “Mun yanke shawarar tabbatar zaman lafiya da kuma kawo ƙarshen wannan gwamnatin.”
Wane ne Ali Bongo?
Wasu na kallonsa a matsayin sangartaccen ɗa, wanda ke kallon mulkin ƙasar Gabon a matsayin hakkinsa na gado.
Ya taba zama mawaki, inda daga baya ya gaji mahaifinsa a matsayin shugaban kasar, ya dora a kan shekara 50 da iyalansa suka kwashe suna mulkin kasar.
Wasu kuwa na masa kallon mai kawo sauyi, kuma sun ce talakawa ne suka zabe shi bisa tsari na demokuraɗiyya.
Sai dai rashin lafiyar da ya yi fama da ita a shekarun baya sun haifar da tantama a kasar mai yawan al’umma sama da miliyan biyu.
A ranar 7 ga watan Janairun 2019 wasu gungun sojoji sun yi yunkurin yi masa juyin Mulki, lamarin da bai yi nasara ba.
Sojojin sun ce dalilin yunkurin nasu shi ne domin su mayar da mulkin demokuradiyya a kasar bayan zaben shekara ta 2016, inda Mr Bongo ya yi nasara da kyar duk da zarge-zargen cewa an tafka magudi.
Gabon na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Afirka da ke samar da man fetur, inda kusan kashi 90 cikin 100 na kasar dazuka ne.
Idan juyin-mulkin ya tabbata, to za ta kasance ƙasar Afirka ta takwas, reinon Faransa da aka yiwa juyin-mulki a cikin shekaru uku da suka gabata.
Sai dai, sauran ƙasashen da suka fuskanci wannan yanayi a yankin arewa su ke na Sahel inda mayakan jihadi suka bada kafar korafi ko amfani da su wajen kifar da gwamnatin dimokuradiyya.
Sojojin na cewa sun kifar da gwamnatin dimokuradiyyar ne domin kare fararan-hula.
Sojojin na cewa sun kafa kwamitin riƙon kwarya da dawo da martabar kasar ta fuskar kundin tsarin mulki da wakiltar tsaro da bai wa kasa cikakken kariya.
A sanarwar ɗaya daga cikin sojojin ta kafar Talabijin na Gaban 24 na cewa: ''Mun yanke shawarar tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kawo ƙarshen wannan gwamnati."
Wannan, a cewarsa, sun biyo bayan nuna "rashin kwarewa, da gwamnati mara alkibila abin da ya haifar da tabarbarewar lamura da suka haifar da ruɗani a zamantakewar al'umma wanda ke neman jefa ƙasar a cikin rikici".
Ana iya jiyo karar bindiga daga birnin ƙasar na Libreville, bayan wannan sanarwar.
Editan BBC a Afirka, Will Ross ya ce akwai yiwuwar tsugono bata kare ba, domin abubuwa na iya sauyawa kuma ana iya smaun turjiya.
Gwamnati dai kawo yanzu ba ta ce komai ba kan matakin sojojin, kuma kawo yanzu ba ma a san inda Mista Bongo yake ba.
An katse layukan intanet bayan zaɓen ranar Asabar saboda dalilai na tsaro, sai dai kuma an dawo da layukan jim-kadan bayan sanarwar sojojin. An kuma sanya dokar hana fita.
Kamar lokacin zaɓukan baya a Gabon, akwai matukar damuwa kan yada aka gudanar da zaɓe a ranar Asabar.
Babban ɗan takarar hamayya Albert Ondo Ossa ya yi korafin cewa akasarin rumfunan zaɓe babu sunansa a takardun kaɗa kuri'a, sannan gamayar da ya ke wakilta na cewa sunayen wasu daga cikin waɗanda suka janye daga takarar shugaban kasa ba a cire ba a takardun kaɗa kuri'a.
Kungiyar 'yan jarida ta duniya ta ce an haramtawa kafofin yaɗa labaran ƙasashen ketare shiga ƙasar domin daukar rahoton zaɓe.
'Yan hamayya sun nuna rashin gamsuwa da dukkanin nasarorin Mista Bongo a baya.
A wannan lokacin, an sauya batutuwan da suka jawo ce-ce-ku-ce a kan takardun kaɗa kuri'a makonni kafin ranar zaɓe.
Mista Bongo ya gaji mulki daga hannun mahaifinsa da ya rasu a shekara ta 2009.
A 2018, ya yi fama da shanyewar ɓarin jiki abin da ya sa ya shafe kusan shekara guda ba a ji ɗuriyarsa ba, a wanan lokaci an yi ta kiran ya sauka daga mulki.
Shekara guda bayan nan, an yi yunkurin juyin-mulkin da bai yi nasara ba, abin da ya kai ga an tura sojojin da suka yi kokarin kifar da gwamnati gidan yari.