'Yan takara 19 za su fafata a zaben shugaban kasar Gabon

Masu kada kuri'a fiye da dubu 850,000 ne ake san za su je rumfunan zabe a wannan Asabar domin zabar shugaban kasar Gabon.

Za su yi amfani da kuri'a guda domin zabar shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki da kuma kananan hukumomi.

Shugaban kasar Ali Bongo, wanda ke neman wa`adin mulki na uku zai fafata ne da abokan hamayya goma sha takwas.

Da shugaba Bongo da sauran abokan hamayyarsa duka sun karade lungu da sakon kasar a lokacin da suke yakin neman zabe.

A tafiye-tafiyen da ya yi a lokacin yakin neman zaben ne, Ali Bongo mai shekara 64 da haihuwa ya yi kokarin ba marada kunya, musamman ma masu sukarsa, suna cewa ba shi da koshin lafiya don haka bai dace ya sake tsayawa takara har karo na uku ba, idan aka yi la`akari da jinyar da ya yi ta shanyewar bangaren jiki a shekara ta 2018.

Sai dai yadda ya dinga tashi da karfinsa yana tattaki a wuraren da ya je yakin neman zabe ya nuna cewa jikinsa na da sauran kwari, sabanin yadda a baya ake ganinsa a kishingide a kan keken marasa lafiya.

Wani salo da ya yi amfani da shi don jan hankali masu kada kuri`a shi ne alwashin da ya yi na rage kudin makaranta da tsadar rayuwa ga iyalai ta hanyar ba da tallafi.

A bangare guda, dadewar da gidan Bongo ya yi yana mulkin Gabon ya sa matasa da dama a kasar ba su san kowa a matsayin jigo ko shuagaba ba face `yan gidan.

Shi kuwa babban abokkin karawar tasa, Albert Ondo Ossa, wanda masanin tattalin arziki ne ya maida hankali ne wajen yi wa `yan kasar alwashin kawo sauyi, yana cewa 'lokaci ya yi da ya kamata shugaba Bongo da danginsa, wadanda suka shafe shekara 56 suna mulkin kasar Gabon su tattara nasu ya nasu su ba da wuri tun da mulkin ba gado ba ne'.

Albert Ossa ya rika sukar gwamnatin Bongo da gazawa wajen samar da aikin yi ga matasa, wadanda alkaluma na nuna cewa kashi daya bisa ukun matasan kasar Gabon ba su da aikin yi.

Wannan zaben dai zakaran gwajin dafi ne ga irin goyon bayan da shugaba Ali Bongo ke ikirarin yana da shi a wajen `yan kasar.

Wasu dai na zargin cewa ya gaza wajen inganta rayuwar al'ummar kasar, duk kuwa da arzikin da Gabon ke da shi na man fetur.

Amma Shugaba Bongo dai yana tinkaho da cewa ya dade a kan karagar mulki, don haka ya san bukatun al`umar kasar kuma ya san hanya don haka yana sa ran samun nasara a wannan zaben.

Ana dai cike da fargaba yayin da ake fara wannan zaben, sakamakon wasu sauye-sauyen da aka yi da suka shafi dokokin zabe, musamman ma yadda aka tsara za a yi amfani da takardar kada kuri`a daya wajen zaben shugaban kasa da `yan majalisa a cikin jam`iyya daya.

An kuma soke zagaye na biyu na zaben shugaban kasa daga cikin kundin tsarin mulkin kasar, tsarin da abokan hamayya ke cewa zai ba da damar samun rinjaye ga bangaren shugaba Bongo, amma ya musanta.

Ana dai zaman rashin yarda tsakanin jam`iyya mai mulki da bangaren `yan hamayya.

Ko da a zaben shugaban kasa biyu da aka yi a baya, wadan da Ali Bongo ya samu nasara, sai da suka kalubalance su, ballantana wannan karon da shugaban kasar ke neman ta-zarce.