Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu biyar game da shugaban mulkin sojan Gabon Janar Nguema
Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun bayyana sunan Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban riƙon ƙwarya a ranar Laraba, bayan hamɓaras da Shugaba Ali Bongo.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi nazari kan wasu batutuwa guda biyar game da shugaban mulkin sojan.
Daga inda ya fito
Janar Nguema ya fito ne daga lardin Haut-Ogooue, na kudu maso gabashin ƙasar Gabon, wanda ya yi iyaka da Jamhuriyar Kongo.
Shi ma Ali Bongo ya fito ne daga wannan ɓangare na ƙasar Gabon.
Aikinsa na soja
A watan Oktoban 2019 ne, Janar Nguema ya maye gurbin wani ɗan'uwan Ali Bongo a matsayin shugaban Dakarun Jamhuriya wato Republican Guard.
Dakarun rundunar ta musamman, su ne ke da alhakin tabbatar da tsaron shugaban ƙasa da iyalinsa da kuma sauran ƙusoshin gwamnatin Gabon.
Alhakin yaƙi da cin hanci
Jim kaɗan bayan ya karɓi sabon muƙamin a shekara ta 2019, Janar Brice Nguema ya ƙaddamar da wani sabon shiri mai taken "kowa ya wanke kansa".
A ƙarƙashin shirin dai, babban hafsan ya riƙa dirar mikiya a kan jami'an da ake zargi da ayyukan almubazzaranci da dukiyar ƙasa.
Kadarori a Amurka
An ambaci sunan Janar Nguema a wani bincike na 2020 a ƙarƙashin wani shiri mai taken Tsararren Aikin ba da Rahotannin Laifuka da na Cin Hanci (OCCRP), wanda rukunin wasu 'yan jarida masu binciken ƙwaƙwaf suka gudanar.
An yi zargin cewa wasu iyalan gidan Bongo da tsirarun makusantansu sun sayi kadarorin kece-raini a Amurka da dukiyar da suka jibge. Iyalan gidan Bongo sun mulki ƙasar mai arziƙin man fetur fiye da tsawon rabin ƙarni.
Babu wani a cikin waɗanda rahoton ya ambata, da ya yarda ya yi bayani lokacin da aka nemi jin bahasinsu.
Bayani game da juyin mulki
Duk da yake Janar Nguema da kansa bai fito ya karanta wata sanarwa ba, amma yana cikin manyan hafsoshin da suka fara fitowa suka sanar da yin juyin mulkin.
Rukunin dakarun, waɗanda suka kira kansu da Kwamitin Riƙon Ƙwarya da Dawo da Martabar Hukumomin Ƙasar ya ce zaɓen ranar Asabar 26 ga watan Agusta, ba sahihi ba ne kuma Gabon na fama da "matsananciyar matsala game da ƙimar hukumominta da shugabanci da tattalin arziƙi da kuma zamantakewa".
A wata hira da jaridar Le Monde ta ƙasar Faransa ranar Laraba, Janar Nguema ya ce mutane a Gabon sun fusata da gwamnati.
Ya nunar da halin rashin lafiyar Bongo bayan wani shanyewar ɓarin jiki a shekara ta 2018, inda ya ce takarar shugaban ƙasar karo na uku, ta saɓa wa tsarin mulkin Gabon.
"Kowa yana magana a kan haka amma ba wanda yake son ɗaukar alhaki," a cewarsa. "Amma yanzu sojoji sun yanke shawarar kawo sauyi.