Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lokuta biyar da aka yi juyin mulki a Nijar
- Marubuci, Umar Mikail a Abuja, da Tchima Ila a Nijar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Hausa
Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya kasance shugaba na biyar da aka hamɓarar daga mulki a ƙasar cikin shekara 63 - tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a 1960.
Ana iya cewa shi ne shugaban mulkin farar hula da ya fara da juyin mulki kuma ya ƙare da juyin mulki bayan wani ɓangare na sojojin ƙasar ya yi yunƙurin ƙwace gwamnati kwana biyu kafin rantsar da shi a 2021.
Tun bayan da sojoji suka garƙame fadar shugaban ƙasa ranar Talata da dare, har yanzu ba a san takamaimai halin da Shugaba Bazoum ke ciki ba, duk da cewa fadar ta ce shi da iyalansa "na raye" kuma "cikin ƙoshin lafiya".
Bayanai na cewa Janar Omar Tchani ne ya jagoranci sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin ta Bazoum, suna masu iƙirarin taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma barazanar tsaro.
Ƙasashen duniya kamar Najeriya, da Amurka, da Faransa, duk sun yi tir da juyin mulkin, wanda ya fara a matsayin yunƙuri kafin daga baya sojoji su bayyana juyin mulkin ta kafar talabijin.
Ƙasashe maƙwabtan Nijar kamar Mali da Burkina Faso, sun fuskanci juyin mulki har karo huɗu cikin shekara uku da suka wuce.
1974
Daga 2020 zuwa 2023, an yi yunƙuri ko kuma samu nasarar yin juyin mulki sau bakwai a yankin Afirka ta Yamma, inda ya shafi ƙasashen Nijar, da Mali, da Burkina Faso, da Guinea.
Ƙasa da shekara 15 bayan samun 'yancin kai daga Faransa a 1960, Nijar ta fuskanci juyin mulki na farko, lokacin da sojoji suka hamɓarar da gwamnatin shugaban ƙasa na farko Hamani Diori.
Laftanar Kanal Seyni Kountche ne ya jagoranci juyin mulkin, wanda daga baya ya zama shugaban ƙasar.
1996
Tun bayan sake kafa mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar a shekarar 1991, sojoji sun hamɓarar da gwamnatoci huɗu daban-daban.
Juyin mulki ya sake afkuwa a 1996 lokacin da Mahamane Ousmane ke mulkin Nijar. Janar Ibrahim Bare Mainassara ne ya kifar da gwamnati, kuma ya ci gaba da jan ragamar ƙasar.
A lokacin Mainasara ya zayyana wasu matsaloli kamar na taɓarɓarewar tsarin dimokuraɗiyya a matsayin dalilansa na yin wannan juyin mulki.
1999
Shekara uku bayan haka, a 1999 shi ma Janar Mainassara ya yi bankwana da mulkin bayan yi masa juyin mulki.
Wannan ne juyin mulkin da Nijar ba ta taɓa ganin irinsa ba, wanda kuma ba za ta manta da shi ba a tarihi saboda irin jinin da aka zubar.
A juyin mulkin ne Janar Ibrahim Bare Mainassara ya rasa ransa, kuma Daouda Malam Wanke ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar bayan juyin mulkin da ya jagoranta a watan Afrilu.
2010
Nijar ta samu 'yar natsuwa tsawon shekara 10 kafin a sake yunƙurin juyin mulki a 2010.
A ranar 18 ga watan Fabrairu ne Laftanar Janar Salou Djibo ya jagoranci sojojin da suka kifar da gwamnatin Tandja Mamadou, wanda ya yi yunƙurin ci gaba da zama a kan mulki bayan cikar wa'adinsa.
An yi juyin mulkin ne salin-alin ba tare da zubar da jini ba.
Juyin mulkin da Janar Omar Tchani ya yi ya kawo ƙarshen shekara 13 ta mulkin dimokuraɗiyya a Nijar, inda Shugaba Mahamadou Issoufou ya shekara 10 a wa'adin mulki biyu.
Shugaba Mohamed Bazoum ya hau mulki a watan Afrilun 2021 bayan nasarar da jam'iyyarsa ta PNDS-Tarayya ta yi a zaɓen shugaban ƙasa.
Ya fara da juyin mulki, ya ƙare da shi
Ita kanta gwamnatin Shugaba Bazoum da aka hamɓarar a yanzu ta fara ne da yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Kwana biyu gabanin rantsar da Bazoum ɗin a watan Maris na 2021, wata bataliyar sojan ƙasar ta yi niyyar ƙwace iko da fadar shugaban ƙasa.
Tun misalin ƙarfe 3:00 na tsakar aka fara jin harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa kuma an ɗauki kusan minti 15 ana yi.
Gwamnatin Mahamadou Issoufou ta lokacin ta ce ta ƙaddamar da bincike kan sojojin da suka jagoranci yunƙurin.
Miƙa mulkin da Shugaba Issoufou ya yi ga Bazoum, shi ne karo na farko a tarihi da gwamnatin farar hula ta gaji wata gwamnatin dimokuradiyya.