An kai wa shalkwatar PNDS hari bayan hamɓaras da Bazoum

Magoya bayan juyin mulkin sojoji a Nijar sun kai hari kan shalkwatar hamɓararren shugaban ƙasar, inda suka cinna wuta tare da jifa da ƙona motocin da ke gaban ginin.

Rukunin masu cinna wutar sun ɓalle ne daga cikin wasu ɗumbin mutanen da suka yi dandazo a gaban ginin majalisar dokokin ƙasar don nuna goyon baya ga sojoji masu juyin mulki, inda aka ga wasu na ɗaga tutocin Rasha.

Rundunar sojojin ƙasar a yanzu ta mara baya ga dakarun da suka ƙwace mulki kuma suke tsare da Shugaba Mohamed Bazoum tun ranar Laraba.

Rasha ta bi sahun sauran ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya wajen kira a saki Bazoum.

Mai shekara 64, wanda aka zaɓa a matsayin shugaban Nijar shekara biyu da ta wuce, babban abokin ƙawance ne ga Ƙasashen Yamma a yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi a Afirka ta Yamma.

Amurka da Faransa, tsohuwar uwargijiyar mulkin mallakar Nijar, duka suna da sansanonin sojoji a ƙasar mai arziƙin yuraniyam kuma sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

Sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya zanta da Bazoum inda ya yi masa alƙawarin "cikakken goyon bayan" gwamnatin Amurka.

Shugaban Jamhuriyar Nijar ɗin wanda sojoji suka hamɓarar da gwamnatinsa a ranar Laraba, ya wallafa wani saƙo a shafinsa na tuwita da ke nuna alamun turjiya.

Lamurra sun sauya ne a Nijar bayan da sojoji masu gadin fadar gwamnati suka yi garkuwa da Bazoum.

Ministan harkokin waje na Bazoum ya ce juyin mulkin bai samu goyon bayan sauran sojojin ƙasar ba, to sai dai babban hafsan sojin ƙasar ya sanar da cewa suna goyon bayan masu juyin mulkin.

Ko wane ne zai zama sabon shugaban Nijar?

Wasu gungun sojoji ne suka bayyana a tsakar dare, ranar Laraba, inda suka tabbatar da cewa sun tuntsurar da gwamnatin Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar.

Kuma sun bayyana cewa sun kafa 'Majalisar kare ƙasarsu ta gado.'

Kakakin sojojin ƙasar Manjo Ahmadou Abdrahamane ne ya yi bayanin ta kafar talabijin ta ƙasar.

Sai dai duk da haka sojojin ba su bayyana ko wane ne shugabansu ko kuma shugaban ƙasar ba.

To amma su wane ne ake tunanin za su zama a gaba-gaba wajen tafiyar da lammurarran ƙasar?

Bayanai dai na cewa Janar Omar Tchani shi ne jagoran sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar.

Janar Tchani shi ne shugaban dakaru masu gadin fadar shugaban ƙasa a halin yanzu, kuma ya kasance a wannan muƙami tun farkon mulki tsohon shugaban ƙasa Muhammadou Issoufou.

Sai dai yayin da ake cikin wannan hali, ministan harkokin waje na Nijar, Hassoumi Massoudou ya wallafa wata sanarwa a shafinsa na twitter inda ya bayyana cewa shi ne ke jagorantar gwamnatin ƙasar a yanzu.

Ya ce "Mai riƙon shugaban gwamnati, Ina kira ga masu son mulkin dimokuradiyya, da duk masu kishin ƙasa su juya wa wannan lamari da ke neman jefa ƙasarmu cikin hatsari baya. Allah ja zamanin dimokuradiyya, Allah ja zamanin Jamhuriyar Nijar."

Hassoumi na daga cikin masu faɗa a ji a gwamnatin tsohon shugaba Mohamed Bazoum da kuma jam'iyyar PNDS Tarayya.

Wane hali aka wayi gari a Yamai?

Titunan birnin Yamai na ƙasar Nijar, sun yi fayau, babu zirga-zirgar mutane da ababen hawa, tun bayan sanar da juyin mulkin da sojin ƙasar suka yi cikin daren da ya gabata.

Ana cikin hali na rashin tabbas.

Tun farko dakarun tsaro sun rufe dukkan hanyoyin shiga fadar shugaban ƙasar da ke Yamai a ranar laraba.

A ƴan kwanakin nan ƙasashen yammacin Afrika na fama da boren sojoji.

Me juyin mulkin Nijar ke nufi ga ƙungiyar ECOWAS?

Sanarwar juyin mulki a Nijar wata gagarumar koma baya ce ga shugabancin kungiyar Ecowas.

Hakan na nuna yadda yankin ke fuskantar matsaloli a ɓangaren mulkin dimokuraɗiyya a yankin yammacin Afrika.

Shekaru uku da suka gabata, sojoji sun yi juyin mulki a ƙasashen Mali da Guinea da kuma Burkina Faso.

Sai dai har yanzu waɗannan ƙasashe na fuskantar matsaloli.

Sojoji a Nijar sun ce sun yi juyin mulkin ne saboda rashin tsaro da kuma rashin iya mulki da ƙasar ke fama da su.

Sai dai ana hasashen akwai sa hannun wasu ƙasashen ƙetare wajen aiwatar da juyin mulkin musamman ƙasar Faransa da ta yi mulkin mallaka a Nijar din.

Makwanni biyu da suka gabata ne shugaban ƙungiyar ECOWAS, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi gargaɗin a ɗauki matakin gaggawa kan ayyukan yan bidindiga da yawan juyin mulki da ake yawan yi a ƙasashen yammacin Afrika

Yanzu haka dai Shugaba Tinubu ya naɗa shugaban ƙasar jamhuriyar Benin domin zama mai shiga tsakanin halin da ake ciki a Nijar.

Abin da muka sani

  • A daren ranar Laraba sojoji sun sanar da cewa sun tuntsurar da gwamnati mai ci ta Mohamed Bazooum.
  • Dalilan da suka bayar na yin juyin mulkin su ne yawaitar cin hanci da rashawa da hali na matsi da talakawa ke ciki, da kuma rashin tsaro.
  • Sojoji sun jingine amfani da kundin tsarin mulkin kasar.
  • An rufe iyakokin ƙasar na kasa da na sama har sai komai ya daidaita.
  • An sanya dokar hana fita daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na safe.
  • Sojoji sun umarci manyan sakatarorin ma’aikatu su karɓi ragamar tafiyar da ma’akatunsu daga hannun ministoci.
  • Sojoji sun tabbatar wa aminan ƙasar cewa komai na tafiya yadda ya kamata.