'Tsoro da rashi da fata a birnin Khartoum bayan sojoji sun ƙwace shi'

Ginin fadar shugaban ƙasa da aka ƙona a Khartooum, babban birnin Sudan - Maris ɗin 2025.

Asalin hoton, Barbara Plett Usher / BBC

    • Marubuci, Barbara Plett Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Khartoum
  • Lokacin karatu: Minti 7

Khartoum, babban birnin Sudan da aka ragargaza a yanzu ya kasance shiru, bayan tsawon makonni da aka ɗauka ana artabu.

Mun shiga birnin kwanaki kaɗan bayan da sojojin Sudan suka sake karɓe iko da shi daga hannun dakarun RSF, da suka shafe watanni shida suna bata-kashi a sassan tsakiyar ƙasar.

Khartoum wanda ya kasance cibiyar kasuwanci da fadar gwamnatin ƙasar, yanzu ya zama kufai.

Bayanan bidiyo, Yadda muka ratsa cikin Khartoum

Sake karɓe iko da babban birnin ƙasar Wata babbar nasara ce a yaƙin basasar ƙasar da aka shafe shekaru biyu ana yi, wanda ya faru sanadiyyar son yin iko tsakanin sojoji da kuma dakarun RSF.

Sai dai - yayin da mutane suka cika kan titunan Khartoum don murnar bikin sallah da kuma cewa yaƙin ya zo karshe - ba a san wane salo rikicin zai ɗauka ba yanzu.

Mun fara isa zuwa fadar shugaban ƙasar, wanda dakarun RSF suka mamaye tun soma yaƙin.

Wuri ne mai muhimmanci ga mayaƙan na RSF.

Wurin ya cika da ɓaraguzai da kuma gilasai da suka farfashe.

Kura ta turnuke kujerun da a baya ake amfani da su wurin shirya manyan taruka, akwai ragowar fanti a jikin bango, da kuma gizo-giza a saman ɗakunan.

An sace tare da lalata komai - har wayoyin lantarki ma an yanka su daga jikin bango.

Cikin fadar shugaban ƙasar Sudan da ke Khartoum da aka lalata.

Asalin hoton, Barbara Plett Usher / BBC

Bayanan hoto, An sace komai a fadar shugaban ƙasar, wanda a baya dakarun RSF suka mamaye

Wurin da aka fi lalatawa shi ne gaban ginin fadar shugaban ƙasar, wanda jirage marasa matuki na RSF suka faɗawa jim kaɗan bayan da sojoji suka ƙwace fadar.

An ragargaza kofar shiga fadar, akwai kuma jini da ya bushe kan tayils ɗin wurin har yanzu, tagogin sun ɓuɓɓule - inda suke kallon Kogin Nilu.

"Ina murnar kasancewa cikin fadar," wani soja ya faɗamin yayin da muke tafiya cikin fadar.

"Wannan ne lokaci na farko da na shiga fadar kuma na yi ta jiran wannan lokaci kamar suaran ƴan Sudan baki-ɗaya. Suna son wurin ya kasance cikin lafiya. Alama ce ta mutunci da girmamawa."

Wata alama ce kuma ta karfin ikon sojoji.

Sojojin Sudan na murna a fadar shugaban ƙasa.

Asalin hoton, Barbara Plett Usher / BBC

Bayanan hoto, Wani gidan sayar da abinci ya kai wa sojojin da ke murna abinci a fadar shugaban ƙasar, waɗanda aka kira a matsayin gwaraza

Sojoji sun yi ta rera waƙoki da kuma yin rawa, inda murnar su ta zo daidai da lokacin da al'ummar Musulmi ke bikin sallah ƙarama.

Wani gidan sayar da abinci ya kai wa sojojin abinci, waɗanda mutane da yawa suka bayyana a matsayin gwaraza.

Girman abubuwan da aka lalata a tsakiyar Khartoum ba zai misaltu ba: an lalata ma'aikatun gwamnati da bankuna da ofisoshi - sun ƙone ƙurmus, sun koma launin baki.

Filin jirgin saman birnin ya zama kufai ga jirage da aka rugurguza, wuraren duba fasfo da kuma kayayyaki a cikin filin jirgin ya koma toka.

Filin jirgin saman Khartoum.

Asalin hoton, Barbara Plett Usher / BBC

Bayanan hoto, An lalata jirage da kuma gine-ginen filin jirgin saman Khartoum da ke tsakiyar ƙasar

Mun yi ta ratsa birnin sannu a hankali, don kauce wa abubuwan fashewa da aka binne a kan hanya.

A wani wuri mun ga gawawwaki da kawunan mutum biyu. Mun kuma ga wata gawa yashe gaban wata mota, kilomita kusan 100 a gefen wata hanya.

Mun tsaya a wata majami'a mai suna St Mathew, wanda Birtaniya ta gina a 1908 - ya kuma kasance wuri da ƴan addinin Kirista marasa rinjaye a ƙasa ke ibada.

Saman cocin da aka gina da ƙawata wa na nan yadda yake.

Akwai wani rami damuka gani a gefen ginin majami'ar wanda harsashi ya ratsa.

Sai dai, cocin ya fi sauran wurare da dama da muka gani, saboda ba a lalata ginin sosai ba.

Ginin majami'ar St Matthew.

Asalin hoton, Barbara Plett Usher / BBC

Bayanan hoto, Yadda cikin majami'ar ta St Matthew yake, wanda ba shi da nisa da fadar shugaban ƙasar - ba a lalata yawanci gininsa ba

Wani soja da muka samu yana share ɓaraguzai, ya faɗa mana cewa yawancin wurare da aka lalata sun faru ne sakamakon fitar ƙarafa lokacin da aka harba harsasai a kusa da cocin.

Babu wanda yake lalata "ɗakin bauta", in ji shi, sai dai mayaƙan RSF sun lalata ginin ta hanyar bahaya da fitsari a cikinsa.

Ya ce an haifi ɗansa a ranar da aka fara yaƙi, amma saboda faɗa da ake yi babu tsagaitawa ya ƙasa zuwa gida ya ga ɗansa.

Dakarun RSF sun kuma ƙwace ko da yankunan da ofisoshin diflomasiyya suke.

Lokacin da aka fara faɗa, ƙasashe da kamfanoni sun yi gaggawar kwashe ma'aikatansu.

A kofar shiga ofishin jakadancin Birtaniya, an saka wani taken RSF a kan bango.

Gilasan ginin waɗanda harsashi ba ya ratsa su, sun ɗan samu lahani a wani ɓangare.

Ginin ofishin jakadancin Birtaniya da aka lalata.

Asalin hoton, Barbara Plett Usher / BBC

Bayanan hoto, An ga wani tutan Birtaniya da aka watsar kusa da gine-ginen da aka lalata a ofishin jakadancin Birtaniya

A can wurin ajiye motoci, ababen hawa ne da aka lalata ke wargaje.

A faɗin titin, tutar Birtaniya ce da aka maƙala kan wani gini da aka lalata, cike da kura da kuma datti.

Wannan shi ne yaƙin basasar Sudan na uku cikin shekara 70, a ɗaya gefen, shi ne mafi muni kan saura da aka samu - saboda sauran yaƙe-yaƙen an yi su ne a wasu sassan ƙasar.

Amma wannan ya ratsa ɗaukacin Sudan, da janyo rarrabuwar kawuna da kuma barazanar raba ƙasar.

Can nisa da fagen daga, masu murnar ƙaramar sallah ne suka cika kan tituna.

Ga mutanen da ke a nan, yaƙin ya kare, duk da cewa ana ci gaba da gwabzawa a wasu wurare.

Mata biyar sanye da sabbin tufafi don murnar ƙaramar sallah.

Asalin hoton, Barbara Plett Usher / BBC

Bayanan hoto, Mazauna Khartoum sun saka sabbin tufafi don murnar ƙaramar sallah karon farko cikin shekara biyu, ciki har da waɗannan mata a wani wurin sayar da abinci
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An zargi sojojin ƙasar da aikata manyan laifuka, kuma rahotannin sun ce dubun-dubatar mutane sun tserewa yaƙin da ake yi a baya-bayan nan. Amma a Khartoum, mutane sun yi murnar kawo karshen baƙin mamayar RSF.

Murnar ta kai har ga wani wajen sayar da abinci da ke makwabtaka da yammacin garin al-Jeraif.

"Ina jin kamar an sake halittata," a cewar Osman al-Bashir, inda ya bayyana irin wahalar da suka sha. Ya faɗa min cewa ya koyi Turanci daga sashen BBC mai watsa labarai a duniya.

Duaa Tariq wata mai rajin kare dimokraɗiyya ne, wanda kuma ke cikin gangamin da ya hamɓarar da shugaba Omar al-Bashir a 2019, bayan shafe tsawon shekara 30 yana mulki.

A yanzu ta mayar da hankali wajen taimakawa makwabtanta da suka tsira daga yaƙin.

"Muna murnar sallah karon farko cikin shekara biyu," in ji ta.

"Kowa na saka sabbin tufafi, ciki har da ni! Ina cike da farin ciki da kuma tausayi, kamar ƙoƙarin koyon yadda za a sake rayuwa. Yanzu muna cikin farin ciki, muna ganin haske, har ta iskar da muke shaƙa ta kasance daban."

Ms Tariq ta sha fama da na yadda take gudanar da wajen sayar da abincin lokacin yaƙi har ta kai abinci ya kare a wajen, dakarun RSF sun sace komai a birnin wanda kuma sojoji suka yi ƙawanya - ga kuma dakatar da ka agaji da Amurka ta yi.

Ana fama da matsalar ƙarancin abinci, amma akwai fata mai kyau yanzu.

"Ina jin daɗi. Ina cikin kariya, duk da cewa ina jin yunwa," a cewar wani dattijo, mai suna Kasim Agra.

"Ka sani, ƴanci shi ne abin da yafi muhimmanci.

"Kamar yadda kake gani, ina ɗauke da wayata," in ji shi, ya faɗa tare da nuna waya cikin aljihunsa.

"Ba za ka iya riƙe waya ba makonni biyu da suka wuce."

Wannan shi ne abin da mutane da dama a wasu sassan Khartoum suka faɗamin - wayoyin salula na da muhimmanci, kuma shi ne abin da mayaƙan RSF ke hari don sacewa.

Bearded Kasim Agra.

Asalin hoton, Barbara Plett Usher / BBC

Bayanan hoto, Duk da cewa mazaunin Khartoum Kasim Agra yana cikin yunwa, amma yana farin ciki a yanzu saboda samun ƴanci, riƙe kuma da waya a hannunsa - tare da fatan za a sake gina birnin

Mista Agra yana cike da fatan cewa Khartoum da kuma ƙasar Sudan za su farfaɗo.

"Ina tunanin gwamnati za ta kawo masu zuba jari daga: Amurka da Saudiyya da Canada da kuma China, za su sake gina wannan ƙasar, na yi imanin haka."

Ko da an sake gina waɗannan wurare da aka lalata, zai yi wuya a sake ganin irin wuraren tarihi da birnin Khartoum ke da su a baya.

Mata da dama sun bayyana cewa a yanzu za su sake komawa yin barci kamar a baya, bayan shafe tsawon lokaci a farke cikin dare sakamakon fargabar cewa mayaƙan RSF za su far musu.

Girman fargaba da kuma asara ba zai misaltu ba: akwai labarai daban-daban na cin zarafi da kuma rayuka da aka salwanta.

Wani karfe a cikin filin jirgin sama.

Asalin hoton, Barbara Plett Usher / BBC

Bayanan hoto, Sake gina Khartoum yana da babban kalubale - kuma ba za a iya kwatanta irin tasiri da yaƙin ya saka mazauna birnin ciki ba

"An firgita ƴaƴan mu," a cewar wata uwa mai suna Najwa Ibrahim.

"Yanzu suna buƙatar ganin likitan lafiyar kwakwalwa domin ya taimaka musu. Malamar ƴar uwata ta yi ƙoƙarin aiki da yaran, sai dai hakan bai wadatar ba.

Ms Tariq ta kuma yi magana kan tasirin da yaƙin ya yi: "Yaushe za a iya komawa rayuwa cikin birnin kamar a baya, yaushe za a buɗe shi?

"Wata tambaya kuma a matsayina na mai fafutika shi ne, me zai faru ga dukkan ƴanci da kuma hakkoki da muka samu a cikin shekara biyar da suka wuce bayan hamɓarar da gwamnati? ta tambaya, inda take misali ga shekarun da suka bi bayan tumɓuke Bashir, lokacin da haɗin gwiwar gwamnatin soji da farar hula ke ƙoƙari wajen komawa mulkin dimokraɗiyya.

"Ta yaya abin zai sake kasancewa ga ƙungiyoyin farar hula da masu fafutuka da masu neman ƴanci? Ban san ya makomarmu za ta kasance ba a yanzu."

Babu wanda ya san makomar Sudan yanzu.

"Muna yi wa mutanen Darfur addu'a," a cewar Hawaa Abdulshafiea ƴar shekara 16, inda take nuni da wurin da dakarunn RSF suka fi karfi, waje kuma da batun jin-ƙai ya taɓarɓare - wuri kuma da ake tunanin yaƙin zai karkata.

"Allah ya kare su."