Amfani 11 da kankana ke yi ga jikin ɗan'adam

Asalin hoton, Getty Images
Kankana na ɗaya daga cikin kayan marmari mai matuƙar farin jini ga mutane, musamman a wuraren masu zafi.
Mutane na son kankana saboda yadda take ɗauke da tarin ruwa mai matuƙar zaƙi a baki.
Kankana ta kasance kayan marmari da ta shafe shekaru aru-aru ana amfani da ita a faɗin duniya, kuma mutane da dama na yi mata kallon kayan marmari mai saurin gusar da ƙishi.
Kayan marmarin na ɗauke da tarin sinadari masu yawan gaske da ke taimaka wa lafiyar jikin ɗan'adam.
Binciken masana ya nuna cewa kusan kashi 92 cikin 100 na kankana ruwa ne.

Asalin hoton, Getty Images
1) Magance hawan jini
Dakta Sa'adatu Sulaiman wata ƙwararriyar likitar abinci a Kano ta ce kankana na taikamawa wajen rage kamuwa da hawan jini.
''Akwai farin ɓawo da ake samu jikinta, wannan yakan taimaka wajen rage hawan jini'', in ji likitar abincin.
Ta kuma ƙara da cewa wannan farin ɓawo yana samar da wani sinadari da ake kira arginine, da ke taimaka wa jini ya gudana cikin sauƙi a gangar jiki.
2) Bai wa jiki kariya
Ita ma Dakta Jawahira Muhammad, wata ƙwararriyar likita a asibitin Murtala da ke Kano ta ce kankana na ɗauke da ruwa mai yawa a jikinta da ke taimakawa wajen bai wa jiki kariya da ƙarin lafiya.
Ta kuma ƙara da cewa a duka nau'ikan kayan maramari kankana ce ke ɗauke da sinadarin calories ɗan kaɗan, da ke haifar da ƙiba.
3) Rage hatsarin kamuwa da ciwon siga
Dakta Sa'adatu Sulaiman ta ce ga duk mutumin da ke son daidata sikarin da ke cikin jininsa to ya yawaita shan kankana.
Yawan sikari a cikin jini kan haifar da hatsarin kamuwa da cutar ciwon siga.
''Idan ka sha kankana za ta rage yawan sikarin da ke cikin jini, fiye da sauran abinci'', a cewar ƙwararriyar likitar.
4) Tsaftace ƙoda da hanta
Dakta Jawahira ta kuma ce kankana na taimakawa wajen wanke ƙoda da hantar mutum.
''Wannan ne ma dalilin da ya sa idan mutum na da matsalar da ta shafi ƙoda idan ya ce asibiti ake ba shi shawarar yawaita shan kankana'', in ji likitar.

Asalin hoton, Getty Images
5) Ƙara lafiyar ido
''Haka kuma kankana na ƙunshe da nau'iran sinadaran vitamins, kamar vitamin A, da B da vitamin C, da kuma vitamin B1da B6'', in ji Dakta Jawahira.
Likitar ta kuma ce Vitamin A na taimaka wa wajen inganta lafiyar idanu.
''Shi kuwa Vitamin C yana taimaka wajen warkar da wani ciwo da mutum ya ji a jikinsa da wuri'', a cewarta.
6) Narkar da abinci
Dakta Jawahira ta ce baya ga tarin ruwa da kankana ke ɗauke da shi, akwai kuma sinadaran fibre.
Likitar ta ce idan aka cire ruwa duk abin da ya rage a jikin kankanka sinadarin fibre ne da ke taimakawa wajen narkar da abinci.
7) Ƙara lafiyar jijiyoyi da na zuciya
''Su kuwa vitamin B1 da B6 suna taimakawa wajen inganta lafiyar jijiyoyi da lafiyar zuciya'', in ji likitar.
Dakta Jawahira ta ce kankana na ɗauke da sinadaran da bayar da kariya daga kamuwa da ciwon zuciya.

Asalin hoton, Getty Images
8) Warware kumburi a gangar jiki
Dakta Jawahira ta ce kankana kan taimaka wajen warware duk wani kumburi da jiki ke fuskanta.
''Kankana na ɗauke da sinadarin citrulline da ke taimaka wajen warware duk wani kumburi da jiki ke fama da shi'', in ji ta.
Ta ƙara da cewa shi wannan sinadari na taimakawa duk inda aka samu kumburi a jikin ɗa'adam domin ya warware.
9) Daidata kitsen da ke cikin jini
Ƙwararriyar likitar ta kuma ce kankana na ɗauke da sinarin Cholesterol, wanda ke daidaita (kitsen da ke cikin jijiyoyin jini).
''Idan kitse ya yi yawa a cikin jijiyoyin jini hakan ka iya haifar da wasu matsalolin lafiya, to amma shan kankana zai daidaita wannan kitse ta yadda zai yi daidai da abin da jiki ke buƙata'', in ji ta.
10) Magance ciwon jiki
''Idan jikinka na yi maka ciwo bayan ka yi atsisaye ko wani aiki shan kankana zai tamaka wajen magance wannan, ta hanyar sinadarin citrulline da take ɗauke da shi'', in ji ta.
Ta kuma ƙara da cewa idan ba ka so jikinta ya yi ciwo bayan yin atisaye, to kafin ka fara atisayen ka sha aƙalla kofi byu na ruwan kankana.
11) Ingata lafiyar fata
Sinadaran Vitamin A da C, da kankana ke ɗauke na su na taimakawa wajen inganta lafiyar fata.
Vitamin C na samar da sinadarin collagen, da ke ƙara hasken fata da tsayin gashi, a cewar Dakta Sa'adatu.
''Shi ma sinadarin Vitamin A na ɗauke da sinadaran da ke ƙara lafiyar fata da samar da sinadaran da ke warkar da fata idan ta ji rauni'', in ji ta.
Sai dai likitoci na bayar da shawara ga masu ciwon sikari da su riƙa kauce wa shan abubuwa masu zaƙi.
Za a iya cin ƴaƴan kankana?

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwararru a fannin lafiya sun ce ƴaƴan kankana (iri)na ɗauke da ƙarancin sidarin sikari a cikinsu da kuma fibre mai yawa fiye da yadda yake a tsokarta.
Haka kuma sun ce ƴaƴan kankana na ɗauke da sinadarin citrulline a cikinsu.
Masanan sun kuma ce ƴaƴan kankana na ɗauke da sinadarin magnesium and folate, da ke taimaka wa jiki wajen kauce wa kamuwa da cututtuka.
Sannan kuma suna ɗauke da wasu sinadarai da ke taimaka wa wajen kauce wa bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki.
Binciken masana ya nuna cewa kankana na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar ɗan'adam.











