Tunanin wasu 'yan Afirka kan Sarauniya Elizabeth ta biyu

A newspaper vendor seen reading a local daily reporting on the death of Queen Elizabeth II in the city of Nairobi. Queen Elizabeth II

Asalin hoton, Getty Images

Rasuwar Sarauniya Elizabeth na biyu ya jefa mutane cikin jimami da aike sakonni ta’azziya masu sosai rai daga shugabanni duniya da sauran daidaikun mutane.

Da dama a kasahen da Burtaniya ta mulka na tunawa da mulki da kuma alakarsu da Sarauniyar, wasu kuma na dauko tsofaffin hotunan da suke yi tare da mai alfarma Elizabeth a kasashensu.

Sai dai ba kowa ne ke yabonta ba. Wasu mutuwarta ta tuna musu da kazamin jinin da aka zubar a lokacin mulkin mallaka – cin zarafin da aka aikata a kasashen Afirka, satar kadarori da kayayyakin tarihi daga kasashen yammacin Afirka, gwala-gwalai da daiman daga Kudancin Afirka da Indiya, bautarwa da musgunawa.

Yayinda Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya bayyana Sarauniyar a matsayin mace ta daban da ta yi fice a duniya, da za a ci gaba da tunawa da ita a fadin duniya, dan jam’iyyar gwagwarmayar ‘yanci ta Economic Freedom Fighters party (EFF), ya ce ba ya cikin mutanen da ke wannan juyayi.

"A shekaru 70 da ta kwashe tana mulki, ba ta taba yarda da laifukan da Burtaniya da ‘yan gidan sarautar suka aikata a sassan duniya ba, kuma ta kasance wacce ke alfahari wajen daga tutar cin zali, " a cewar sanarwar da jam’iyyar da ke ta uku mafi karfi a kasar ke cewa.

"A wajenmu mutuwarta ta tunasar da mu mumunan yanayi na bakin ciki a wannan kasa da kuma tarihin Afirka. "

A shafukan sada zumunta ma, wasu masu sukan sun tsananta kalamansu.

Queen Elizabeth na taka rawa da shugaban Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth na taka rawa da shugaban kasar Ghana, Kwame Nkrumah, a 1961 - wannan hoto ya bai wa wasu daga cikin 'yan gwagwarmayar yaki da wariya mamaki a Afirka ta Kudu

Wani sakon tuwita da wata 'yar Najeriya amma haifafiyar Amurka, Farfesa Uju Anya ta wallafa, sa'o'i bayan mutuwar Sarauniyar, ya haifar da muhawara mai zafi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai sakon da shafin tuwita ma ya goge saboda saba ka'idojinsa.

A sakonta na biyu, ta rubuta: "Idan akwai wanda ya ke tunanin na ce wani abu face kyamar da nake yiwa masarautar da ta goyi-bayan gwamnati da ta dau nauyin kisan kare dangi da ya daidaita kusan rabin dangina, wanda har yanzu wadanda suka rayu na tattare da tasiri wannan ayyuka, za a jima ana mafarki."

Sakonta na nufin abin da ya faru a lokacin yakin Biafara a shekarun 1960, lokacin da gwamnatin Burtaniya ta goyi-bayan gwamnatin Najeriya da ba ta makamai wajen murkushe masu neman ballewa domin kafa kasar Biafra.

Wani a shafin tuwita din mai suna, @ParrenEssential, ya mayar da martani, yana mai cewa wannan ba da'ar 'yan Najeriya ce ba, ya kara da cewa: "Ba kya wakilartar al'adunmu da dabi'un 'yan kasa."

Wasu na cewa aibata mutum a lokacin mutuwarsa ba "halayen 'yan Afirka ba ne."

An kuma rinka wallafa sakon neman a dawowa da daiman din Afirka, wanda aka gano a Afirka ta Kudu a 1905 da yanzu ake ganinsa kan kambin sarautar Burtaniya, har lokacin mutuwar Sarauniyar. Da dama daga cikin mutane sun rinka cewa na "sata" ne.

Duk da cewa gwamnatin wancan lokaci ne suka bai wa gidan Sarautar Burtaniya a matsayin tukuicin nuna biyayyarsu, abin da ake cewa a shafukan sada zumunta shi ne kaddara 'yan Afirka ta Kudu ne.

Wani mai amfani da shafin tuwita @Qban_Linx ya ce daiman din da kudinsa ya kai dala miliyan 400 - irinsa mafi girma makale a jikin sandar girmar da sarakuna ke rikewa a lokacin nadi - na iya biyan kudin jami'a na dalibai dubu 75 a Afirka ta Kudu.

Sarauniya Elizabeth

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth a lokacin nadinta, dauke da sandar girma mai dauke da Daiman din Afirka a hannunta na dama

Hakazalika an samu irin wannan koke a Indiya, inda maudu'in "Kohinoor" ya rinka jan hankali a shafin tuwita bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth - wannan na nufin daiman din da ke jikin kambin sarautar da matar sarki wato 'Queen Consort' za ta rinka sa wa.

Wasu masu suka sun ce ya kamata Sarauniyar ta yi amfani da karfinta da tasirinta wajen tabbatar da cewa an mayar da kadarorin mutanen da suka yi yaki da Burtaniya lokacin mulkin mallaka.

Kenya da Afrika ta Kudu sun bukace a maido mu su da kawunan gwarazansu irinsu Koitalel Samoei, da ya jagoranci bijirewa mulkin mallaka a Kenya ta yanzu a karshe karni na 19, da Sarki Hinstsa kaKhawula na masarautar Xhosa a Afirka ta Kudu, da aka kashe a 1835.

An file kawunansu, sannan aka ta fi da su Burtaniya a matsayin lambar yabon nasara a yaki.

Dan kungiyar tawaye ta Mau Mau, Gitu wa Kahengeri ya yi alla-wadai da abubuwan da Burtaniya ta aikata, amma ya ce yana makokin Sarauniyar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dan kungiyar tawaye ta Mau Mau, Gitu wa Kahengeri ya yi alla-wadai da abubuwan da Burtaniya ta aikata, amma ya ce yana makokin Sarauniyar.

"Sun mamaye kasata, inda aka haifeni," kamar yada ya shaidawa kamfanin dilanci labarai na Reuters. "Amma dai muna makokinta saboda ita ma 'yar adam ce," a cewarsa.

"Muna tausayin wadanda suka mutu."

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, wanda ya bayyana Sarauniya a matsayin "wacce ta yi fice sosai wajen bautawa al'umma", ya fuskanci caccaka daga wasu 'yan Kenya bayan ayyana makokin kwana hudu a fadin kasar.

"Tsohon shugaban Botswana, Ian Khama, shi ma ya kasance wani mutum da ya kare martabar Sarauniyar, yana mai cewa maye gurbinta da wuya.

"Ya ce mulkin mallaka ba abu ne da muke son mu tuna da shi ba, yanayi ne mafi muni," a cewarsa.

"Sarauniya ta gaji wannan tsari ne, ba wai ita ce ta kirkiro hakan ba...amma da ta bayyana sai ya kasance kamar ta gyara barnar da aka aikata ne, abubuwan da mulkin mallaka ya haifar, ta nuna cewa babu wanda yake saman wani, ta nuna tana son aiki da kowa saboda cigaba da taimakwa kasashe su habbaka."

Nahiyar Afirka tayi mata kallo a matsayin wacce ta kawo sauyi da bude sabon babin rayuwa daga kuncin da aka fuskanta a baya" a cewarsa.

Mutane da dama na cewa Sarauniyar ba ta taba neman afuwa ba kan laifukan da aka aikata da sunan masarautar.

Kodayake ta taba magana kan yanayi mai wahala da kisan gilla da aka aikata a Amritsar, na arewacin India, a 1919.

Kafin ziyartar yankin a 1997, yankin da wani janar din sojin Burtaniya ta umarci a bude wuta kan masu zanga-zanga a wurin da ba za su iya guduwa ba, ta yi tsokaci nadama kan abin da ya faru.,

"Ba sa a iya sauya abin da ya faru a baya ba, duk da cewa ba hakan aka so ba. Komai na da bangaren bakin ciki da kuma na farin ciki. Dole mu koyi darasi daga bakin ciki domin gina farin ciki a gaba.