'Matsalar tsaro ta karu matuka a Najeriya'

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya na fama da tashe-tashen hankali daban-daban da suka shafi matsalar tsaro, daga satar mutane domin neman kudin fansa zuwa ayyukan masu 'yan tawaye da kuma aikata miyagun laifuka da kusan daukacin kasar ke fama da shi.
Wani rahoto kan yanayin tsaro a Najeriya ya nuna cewa an samu ƙarin matsalar tsaro a ƙasar cikin watan Nuwamba.
Kamfanin Beacon Consulitng wanda ya fitar da rahoton ya ce matsalar tsaro ta ƙaru da kashi 16 cikin ɗari a watan da ya gabata.
Shugaban kamfanin Dr. Kabiru Adamu ya shaida wa BBC cewa an samu ƙarin mace-mace da kashi 16 cikin ɗari, inda mutane 1,308 ne suka rasu a watan Nuwamba, adadin da ya zarce na watan octoba.
Dr Kabir ya ce " Amman adadin mutanen da aka sace domin ansar kuɗin fansa a watan na Nuwamba ya ragu da kashi 10 cikin 100, inda aka sace mutane 464, ya yin da a watan Octoba aka sace mutane 518.
Me ke ƙara ta'azzara matsalar?
Shugaban kamfanin na Beacon ya ce "abin da ke ta'azzara matsalar tsaro shine rashin daukar matakin da ya dace kafin aukuwar matsalar, kuma hakan ba kai Najeriya inda take so ta kai ba.
"Matsin tattalin arziƙi da rashin hadin kan gwmanatin tarayya da ta jihohi na daga cikin abubuwan da su ƙara saka Najeriya cikin matsalar tsaro" inji Malam Kabir Adamu.
Dr Kabir Adamu ya ce "Ƙungiyoyi masu riƙe da makamai da suka mamaye sassan Najeriya na kan gaba wajen tabarbarewar tsaron ƙasar, kuma har yanzu matakan da gwamnati ke dauka bai hana ƙungiyoyin walwala ba, da kuma kai hare-hare a kauyuka, inda suke sace mutane tare da hana manoma noma".
Ina mafita?
Rahoton ya bada shawarar cewa " Akwai buƙatar Majalisar ƙasar ta bi diddiƙin kasafin kuɗin da aka yi domin a tabbatar da cewa an aiwatar da duk abin da aka tsara aiwatarwa a cikin kasafin, kamar irin su inganta fannin lafiya da ginenen hanyoyi, saboda idan aka magance matsalar tattalin arziƙi, z a a samu saukin rashin tsaro ƙwarai.
"Kuɗaɗen da aka warewa bangaren tsaro a tabbatar an yi amfani da su ta yadda ya kamata. Kuma ɓangaren zartarwa ya yi ƙoƙari ya inganta haɗin kan da ke tsakanin shi da gwamnonin jihohi. Akwai buƙatar yaƙin tsaron kowane yanki a fitar da shi daban.











