Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mabiya addinin Kirista a duniya na bikin Kirsimeti
Al'ummar Kiristoci a faɗin duniya na bikin Kirsimeti da aka saba gudanarwa a rana irin wannan ta 25 ga watan Disamba.
Bikin na bana ya zo ne cikin jimami, yayin da duniya ke fama da matsaloli iri daban-daban, musamman na yaƙi, hatta a yankin da aka haifi Yesu Almasihu, wato Betlehem, da ke Falasɗinu.
A cikin jawabinsa na barka da arziƙin wannan lokaci na Kirsimeti, Paparoma Francis ya yi kiran a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, inda ake yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza.
A cewarsa "Ana watsi da kiran Yesu na zaman lafiya hatta a inda aka haife shi. A sani cewa, Yesu bai kawo ƙarshen rashin adalci da ƙarfi ba, sai ta hanyar nuna soyayya da ƙauna".
"A daren yau, zukatanmu suna Batlehem, inda aka haifi yariman yarimomi, inda har a yau yaƙi ya hana gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa." Ya nanata kiran a kawo ƙarshen yaƙin da ake gwabzawa a Falasɗinu.
Ko duk Kiristoci ne ke wannan biki?
A cewar wani babban limamin Kirista a Najeriya, Pasto Yohanna Buro, ba duka kiristoci ne ke gudanar da wannan biki na Kirismeti ba.
Ya ƙara da cewa, akwai waɗanda ke da iƙirarin cewa babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da ke nuna cewa a wannan rana ne aka haifi Yesu Almasihu, don haka bidi'a ne gudanar da bikin na yau.
''Kamar yadda wasu a cikin musulmai ba su yadda da bikin Mauludi ba, haka mu ma a cikinmu kiristoci, akwai wasu ɗariƙoƙi da ba sa gudanar da wannan biki na yau saboda aƙidunsu''
Ya ce ''Ko a ƙasarmu Najeriya akwai wasu ɗariku da ba sa yi, haka a duniya ma baki ɗaya, suna ƙyamar wannan biki na yau, kamar Ƙifɗawa, da wasu da suka rabu da cocin katolika.
Akwai ma wani sashen Kiristoci a ƙasashe kamar Siriya da Iraƙi, haka kuma akwai wasu da suna yi, amma a mabambantan lokuta''.
A cewarsa ''Sai dai duk da haka mun haɗu a kan matsaya ɗaya, cewa Yesu ya shigo duniya, kuma ya yi rayuwa kamar mu, kuma ya mutu, amma zai dawo ya ceci duniya''
Me ya kamata Kiristoci su yi ranar Kirsimeti?
A cewar Pasto Yohanna Buro, Kirsimeti rana ce mai muhimmanci da ake bukatar a sada zumunci, a ƙaunaci juna, sannan a kauce wa abubuwan da Allah ba ya so.
''Lokaci ne da za a yaɗa kowacce bushara irin ta salama, da haɗin kai, da ƙaunar juna da kyautata zamantakewa da kuma fahimtar juna.
"Sannan a taimaka wa marasa hali, a kyautata maƙwabtaka, da kuma duk wani abu na ci gaban al'umma," in ji shi.
Sai dai ya ce kamar yadda akwai abubuwan da ake so a kyautata, haka kuma akwai abubuwan da ake son Kiristoci su kauce musu a wannan rana, kamar shan giya, da rashin wadatar zuci, da sauran munanan ayyuka.