Abin da ya sa sabon fim ɗin Shah Rukh Khan ke haifar da gagarumar muhawara

Taurarin fim din Pathaan: Shah Rukh Khan, Deepika Padukone da John Abraham

Asalin hoton, YRF

Bayanan hoto, Taurarin fim din Pathaan: Shah Rukh Khan, Deepika Padukone da John Abraham

Sabon fim na Fitaccen dan wasan Indiya Shah Rukh Khan Pathaan, da ya fito ranar Laraba, ya mamaye kanun labaru a kasar Indiya a `yan makwannin nan.

Khan- yana cikin manya-manyan taurarin Indiya, da aka fi kauna kuma sha`awar da ake ta nuna masa ba a bar mamaki ba ce.

Mai farin jini, da ban dariya da ke da miliyoyin masu sha`awar fina-finansa a gida da kasashen ketare, akan kwatanta afton a matsayin dan wasan Indiya “da ya fi muhimmanci wajen fitar da al`adu”, wanda sunansa da ficensa suka zarce fina-finansa.

Masu kaunarsa, suna kiransa da Sarki Khan ko Sarki na fina-finan Indiya.

Kuma Pathaan shi ne fim na farko da ya yi bayan likimon da ya yi na shekara hudu.

Mai shekara 57 a duniya, ya sake yunkurowa a manya-manyan allunan majigi bayan matsaloli daban-daban da koma baya daya bayan daya da yake ta cin karo da su a rayuwarsa ta kashin kansa da kuma ta sana`arsa, ciki har kama dansa Ason Aryan Khan a shekarar da ta gabata, a kan tuhume-tuhume na karya na mallakar miyagun kwayoyi- daga bisani an janye tuhume-tuhumen – da kuma wasu fina-finansa da ba su fito da farin jini ba.

Gibin da likimon nasa ya haifar ya ja hankali ga Khan da kuma haddasa sa ido ba kadan ba, a kan wannan fim, wanda har ila yau jarumai irin su Deepika Padukone, daya daga cikin taurarin Indiya da suka fi yin suna, da John Abraham duk suka fito a cikinsa.

Da aka soma shi a watan Disamba lokacin da wadanda suka shirya shi suka soma fitar da samfotin bidiyon wakokin Pathaan, ya mamaye zantuka a soshiyal midiya. Kuma da aka sake shi a ranar 10 ga watan Janairu, zakuwar kallonsa da dokin ganinsa suka kai kololuwa.

An kalle shi sau fiye da miliyan 51 ta Youtube/Yutub. Ra`ayoyi ta twita da Khan ya samu a kan Pathaan sun kai miliyan 3.9, da karin rabin miliyan ga wadanda aka yi na Telugu da Tamil.

Rahotanni suna cewa an yi ribibin sayen tikitin shiga kallonsa a Amurka, da Daular Larabawa, da Jamus da Austireliya.

..

Asalin hoton, YRF

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasan wanda, masu kallonsa suka kwatanta a matsayin tsallen –badake tsakanin fina-finan James Bond da na Mission Impossible, abu ne da ake iya hasashen me zai auku a gaba.

Wata kungiya ta `yan ta`adda tana neman rusa Indiya da “wani hari da ba su taba tunaninsa ba”. Hukumomi suka soma rige-rigen yakarsu, sai dai lokaci yana kokarin kurewa. Babbar matsalar ita ce ya kasar za ta kasance nan gaba. Saboda haka suka zabo wanda shi ya fi kowa kwarewa domin wannan aiki.

“Idan ka yi gangancin sharholiya a gidan Pathaan, to zan kuwa zo in gaishe ka- da tartsatsin wasan wuta,” wata murya wacce babu kuskure a tattare da ita tana gatsine, a lokacin da Khan ya bayyana a gare mu.

Dan leken asiri da suma a caccakude, cikin kwanji, ba tare da wata-wata ba ya dinga zubar da abokan gaba, yana dafe motoci da suke kai komo, da dafe igiyoyin da aka daddaura a dogayen manya-manyan gine-gine da jan hankalin mata, a lokacin da yake kokarin ceto kasarsa daga mugayen mutane, karkashin jagorancin Abraham. Kida mai shiga jiki yana yi wa hotunan wannan fim rakiya.

Samfotin Pathaan mai tsawon minti biyu da rabi yana da masu sonsa da kuma sukarsa. Wani mai son shi ya kira shi da “paisa vasool (kwalliya ta biya kudin sabulu)”, tare da karin bayanin cewa zai kokarta domin samun wannan fim da zaran ya fito.

Sai dai tun farkon fara shi, Pathaan ya cabe da jayayya.

Khan ya yi tasa famar da `yan jarida, da kuma masu sukarsa a baya. Sai dai tun kalaman da ya yi a game da karuwar rashin hakuri da addinan juna a Indiya a `yan wasu shekarun baya, sukarsa daga kungiyoyi masu ra`ayin siyasar dama-dama, ta karu da kuma mayar da sukar tasa ta koma ta son rai.

“Abin ya koma ga ji wa juna, saboda suna neman nasabta ko danganta kamarsa da ta addininsa,” in ji marubuci kuma mai sukar fim Saiba Chatterjee.

...

Asalin hoton, YRF

Kungiyoyin masu tsattsauran/zazzafan ra`ayi na Hindu kuwa sun zafafa jayayya a kan launin rigar nono da na dan kamfan da Deepika Padukone take sanye da su a daya daga cikin wakokin da suke cikin Pathaan. In ban da `yan shekarun da suka gabata, ya ce ana daukar fina-finan Indiya a matsayin wani fage da ya kasance, ya zarce bambance-bambance na addinin da na siyasa. “nishadantarwa ce kawai aka sa a gaba” Sai dai ya kara da cewa, a yanzun masana`antar ta fina-finai tana ci gaba da samun rarrabuwa a cikinta. “Khan yana daya daga cikin sauran daidakun aftocin da suke wakiltar abubuwan da suka wuce, da wasu bangarorin suke son su kawar da shi gabadaya. Shi ya sa suka kasa iya fuskantarsa.”

Kungiyoyin na masu tsattsauran ra`ayi da tuni sunan na Pathaan – wanda suna ne na Musulunci – suka tayar da jijiyoyin wuya a kan daya daga cikin wakokinsa, bayan an ga Padukone sanye da rigar nono da dan kamfai launin ruwan kwai mai duhu-duhu a wakar Besharam Rang – da aka fassara daga Hindi zuwa launin rashin kunya.

Sun zargi Khan da zagin `yan Hindu domin kuwa launin ruwan kwai mai duhu-duhu, launi ne da ake danganta shi da addininsu, duk da Padukone tana ta sauya shigar da ta yi a lokacin wakar.

Akwai kiraye-kirayen a haramta wannan fim, har sai an cire wannan waka, masu boren sun fito da fastoci da konanniyar surar Khan, an gabatar da korafi a gaban wata kotu, ana zargin an ci zarafin al`umar Hindu kuma an zargi wannan fim da daukaka nuna tsiraici da fitsaranci.

Akwai kiraye-kiraye babu kakkautawa na a kaurace wa Pathaan, da kalaman zage-zage a soshiyal midiya.

Sai dai a daidai lokacin da aka soma kidayar mintocin da suka rage a saki wannan fim, Khan da masu shirya wannan fim sun soma kula jayayyar maimakon su mayar da hankali wajen daukaka shi.

A lokacin wasannin cin kofin Duniya na Fifa, dan wasan kwallon kafa Wayne Rooney ya fito tare da afto Khan a wani dan gajeren bidiyon talla, yana maimaita kalaman da Khan yake ambata cikin harshen Hindi – “Apnikursi ki peti bandh lo, Mausam bigadnewalahai (Ku daura madaurin kujerar zamanku katakam, domin kuwa ana shirin shiga wani mawuyacin hali)”

Sannan a farkon wannan watan, Khan ya ziyarci Dubai inda dandazon masu kaunarsa suka kalli samfotin Pathaan , da aka nuna a ginin Burj Khalifa.

...

Asalin hoton, YRF

An hada Khan da gungu na `yan ta`adda karkashin jagorancin Abraham. Daga kimar afton zuwa rupee biliyan 2.5 ($30m; £25m) da aka kasafta wa wannan fim- akwai batutuwa da dama da suke nan, kuma wasu suna jinjina ko bata sunan da ake masa, zai iya shafi nasarar wannan fim.

Tunani ne da Chatterjee bai amince da shi ba.

“Khan bai tsaya a matsayin afto kawai ba, shi wata babbar alama ce, watakila mafi girma da muka taba samu a kasar nan, kuma tabbas a fina-finan Indiya,” in ji Chatterjee.

Shrayana Bhattacharya, marubuciyar wani littafi da ake kira Neman Shah Rukh Khan tuwa a jallo, ta ce masu kaunar gwarzon ba “za su taba rage masa matsayi zuwa lissafi na addini ko siyasa ba”. “Za su kalli Pathaan ranar farko nunawar farko saboda sun dade ba su yi tozali da shi ba a bangon majigi,” kamar yadda ta kara da cewa.

Sai dai wasu suna da tunanin ko wannan fim na dan leken asiri, a cikinsa ne ya dace a ce Khan ya dawo babban bangon majigi bayan kewarsa ta wajen shekara hudu?

Khan ya yi fice ne a matsayin gwarzon soyayya, afton da ya fayyace mene ne so da kauna – harshen soyayya, da kwarkwasa ta soyayya, da sace zuciyar da juyayi da fargabar da suke tattare da ita- domin ilahirin jinsi na al`uma. Kuma mata, da su ne suka fi yawa a masoyan nasa, babu mamaki ba zai burge su, idan suka ga ya fito a matsayin afton da yake ballan basawa kawai ba.

A `yan kwanakin baya, afton ya ce yana so a kowanne lokaci ya ga ya fito a fina-finai na balla zalla, shi ya sa ma ya fito a Pathaan “burina ne ya cika”.

Chatterjee ya ce “yana da nasa tunanin” a kan wannan fim, amma “tunani ne na kuru”.

Shekaru da dama, ya yi nuni da cewa, afton ya gwada da rubutun da aka masa don ya masa jagoran wasan da ake so ya yi, ya taka rawa iri daban-daban kamar wacce ya taka a My Name is Khan, Chak de India da kuma Love You Zindagi.

Da Phataan, ya ce, a fili yake Khan “Ya hau turba mai wahalar gaske”

“Sai dai a wannan mataki na sana`arsa, zai iya yin hakan. Ba shi da tsoro kuma gwaji yake yi. Ba shi da wata asara.”