'Yadda na gano al'aurata na zazzagowa'

b

Lokacin da Natashja Wilson ta fara lura da alomomin lalurar zazzagowar farji ba ta san me za ta yi ba, saboda ba ta san me ke faruwa ba, kuma ta ji kunyar neman taimako daga wani.

Shekarunta 18 kacal a lokacin kuma ba a gida take zaune ba, tana zaune ne a jami'a, ba ta taɓa jin labarin wannan lalura ba, da ke shafar kusan kashi 50 cikin 100 na mata a rayuwarsu.

"Na lura lokacin da na shiga bandaki wani kumburi yana fitowa daga cikin farjina," in ji ta.

“Har ila yau, nakan samu rashin natsuwa da jin zafi a lokacin saduwa sannan nakan ji zafi a wajen kumburin.

"Gaskiya ban san abin da zan yi ba saboda gaskiya ban san komai game da jikina ba a lokacin."

A yanzu shekarun Natasha 24, ta ce ba ta san abin da ke faruwa da tsokar da ke a cikin ƙugu ko ma mahaifarta ba.

"Don haka na tambayi ƙawayena cewa wannan kumburin ba matsala ba ce?," in ji ta.

"Sai suka ce, 'Wataƙila kin ji ciwo ne a al'aurarki. Watakila tabo ne kawai."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Natasha, wadda 'yar yankin Greenwich ce a birnin Landan, ba ta san me za ta yi ba don haka ta bar shi da fatan kumburin zai tafi da kansa.

Amma alamun sun ci gaba da bayyana, har tsawon wata 18, inda daga ƙarshe ta faɗa wa mahaifiyarta, wadda ta rarrashe ta, ta kuma kai ta asibiti. Inda likitoci suka tabbatar da cewa mahaifarta ce ta zazzago

Zazzagowar wasu gaɓoɓi na faruwa ne lokacin da jijiyoyi da tsokokin da ke tallafa wa gaɓoɓin ƙugu suka zama masu rauni ta yadda ba za su iya riƙe duka goɓoɓin da ke cikin ƙugu da kyau ba.

Hakan na sa wasu daga cikin gaɓoɓin su yi ƙasa daga inda suke, lamarin da ke haifar da kumburi a ciki ko wajen al'aurar sakamakon zazzagowar wata gaɓa daga inda take a ainihi, gaɓoɓin da ke zazzagowar kuwa sun haɗa da mahaifa ko hanji ko mafitsara ko saman al'aura.

Alamun irin wannan yanayi na iya haɗawa da zazzagowar dubura, da jin saukowar wani abu a cikin al'aura, wanda a wasu lokuta mace za ta ji kamar ta zauna kan wani abu, da matsalolin mafitsara ko saman al'aura da kuma jin zafi a lokacin jima'i.

Motsawar ƙashin ƙugu da canje-canjen rayuwa na iya taimakawa wajen inganta alamun bayyanar cututtuka, amma wani lokaci ana buƙatar magungunan asibiti kamar na farji ko tiyata.

Samun juna-biyu da kuma haihuwa na ƙara haɗarin zazzagowar wata gaɓa musamman bayan naƙuda mai wahala.

Haka kuma mata kan fuskanci matsalar zazzagowar wata gaɓa musamman idan suka tsufa, musamman bayan daina jinin al'ada.

Amma Natasha na son sanar da sauran mata cewa matsalar ka iya shafar mata masu matsakaicin shekaru.

Tana ƙoƙarin yaƙi da ƙyamar da ake nuna wa matan da ke fama da irin waɗannan lalurori ta hanyar shafinta na sada zumunta da ta sanya wa suna ''Masu lalurar zazzagowa a al'aura''

"Har yanzu ana nuna ƙyama ga masu lalurar, kuma yana da kyau mu riƙa tattaunawa game da matsalar, don hakan zai bai wa mutane damar zuwa asibiti domin ganin likita," in ji ta.

"Na tabbata da a ce ba a ƙyama ko tsangwamar masu irin wannan lalura da na je asibiti tun da wuri."

Abin da ke kawo cikas wajen kula da lalurar

Cibiyar Kiwon Lafiya da Kulawa ta Kasa (NICE) a Birtaniya ta ce, mace ɗaya cikin 12 na cewa tana ganin alamomin zazzagowar a gabanta, amma awo na nuna cewa kashi 50 cikin 100 na mata na fuskantar matsalar.

Binciken da Jami'ar Stirling ta gudanar na nuna cewa jin kunya, da rashin masaniya game da lalurar da kuma fargabar rashin ɗaukar alamomin da muhimmanci, duk na taimaka wa wajen kawo cikas ga matan da ke bukatar taimakon likitoci kan lalurorin da suka shafi zazzagowar al'aura.

Binciken ya yi nazari kan takardu daga kasashe 24 da suka haɗa da Birtaniya cikin shekara 20 da suka gabata, inda aka ji ra'ayoyin mata fiye da 20,000.

Jagororin binciken Clare Jouanny da Dakta Purva Abhyankar sun ce: "Akwai manyan hujjojin da ke nuna cewa a Birtaniya da wasu ƙasashe a faɗin duniya, har yanzu mata na fuskantar cikas da yawa idan ana batun neman taimako ga al'amuran kiwon lafiyar mata kamar naƙuda.

"Muna bukatar mu mayar da hankali ba kawai a kan ƙara wayar da kan jama'a da ilimi a tsakanin mata da likitoci ba, amma mafi mahimmanci muna buƙatar yin aiki tare da likitoci don canza tunanin mata cewa likitocin ba sa ɗaukar lalurorin da suka shafi lafiyar abubuwan da ke cikin ƙugun mata da muhimmanci.''

b

Suzanne Vernazza, likitar ƙashin ƙugu ce da ke kan aikin wayar da kan mata game da lafiyar ƙashin ƙugu. Ita ce wadda ta kafa wani kamfani mai suna 'SqueezeAlong' da ke koyar da motsa jiki. Kamfanin kuma na da mabiya fiye 600,000 a shafinsa na TikTok.

Ta ce yana da mahimmanci mutane su riƙa sanar da likitoci matsalolin lafiyar ƙashi ko tsakar kugunsu.

"Idan kuna jin wani abu wanda a kowane lokaci ke damun ku, ko kuna da juna-biyu ko kuna shayarwa, ku yi bayani da kuma ku yi tambaya saboda a lokuta da dama kuna tunanin wata alama ba matsala ba ce, alhalin kuma matsalar ce, amma idan kuka samu taimako za ku iya magance lalurar'', in ji ta.

Kwalejin Royal da ke Birnitaniya, ta ce likitocinta na da ƙwarewa da za su iya tantancewa da kula da mutanen da suka kamu da cutar.

Dakta Chris Williams na jami'ar Scotland ya ce: "Likitoci na sane da irin jin kunya ko rashin kunya da za a iya danganta su da wannan yanayin kuma suna ƙoƙari don tabbatar da cewa mata sun ji daɗi da kuma bayar da damar neman taimako idan sun fuskanci alamun."

b

Sam Hindle ta fuskanci zazzagowar mafitsara bayan haihuwar ɗanta shekara 24 da suka gabata, kuma tun daga lokacin take fuskantar matsala.

"Abin takaicin da ba zan manta da shi ba shi ne ɗana a lokacin yana da shekara biyu ya je ya ɗauko min wanduna, abin kunya ne ɗanka mai shekara biyu ya gane irin halin da kake ciki, a lokacin har ce wa mutane yake yi mamarsa ta ji ciwo, don haka dole ya taimaka mata, saboda yanayin da na shiga'', in ji ta.

Matar, 'yar asalin Edinburgh, mai shekaru 47, na ɗaya daga cikin dubban mata a Birtaniya da aka yi wa tiyatar al'aura don magance matsalar zazzagowar al'aura.

An dakatar da tiyatar al'aura a Birtaniya a shekarar 2018 saboda wasu sauye-sauye da mata suka fuskanta. Sam ta fuskanci zafin ciwo akai-akai kuma, sannan ta kamu da lalurar yoyon fitsari sakamakon aikin.

Ta ce tana fatan wani ƙwararren likitan Amurka ya yi mata aiki, kuma a halin yanzu tana cikin jerin masu jiran ganin likita a Glasgow. Ta ce yana da matuƙar mahimmanci mata su riƙa magana game da lafiyar ƙashin ƙugu.

“Kamar daina jinin al'ada, batu ne da ya kamata mu cire ƙyama mu riƙa yin magana a kai, kada mutane su ji kunya, don haka mata su je su nemi taimakon likitoci'', in ji ta.

//

Asalin hoton, Natashja Wilson