Yadda rashin lafiyar Sarki Charles III za ta shafi yarima William da Harry

Yarima Harry da yayansa Yarima William
Bayanan hoto, Yarima Harry da yayansa Yarima William

Lokaci ne mai wahala ga iyalin masarautar Birtaniya.

Yarima William da ƙaninsa Harry da kuma saurarn iyalin masarauta za su shiga cikin ƙarin hali na matsi da rashin tabbas yayin da aka gano cewa Sarki Charles na fama da cutar kansa.

Wannan hali da suka shiga ya faro ne kimanin mako uku da suka gabata, lokacin da aka bayyana cewa maiɗakin yarima Willaim, wato Gimbiya Kate (Catherine, Gimbiyar Wales), za a yi mata tiyata, kuma za ta ɗauki watanni kafin ta warke.

A daidai lokacin da gidajen talabijin suka garzaya suka kafa kyamarorin ɗaukar labarai a ƙofar asibitin da ke birnin Landan, sai kuma wani labarin ya fito, wanda ke cewa shi ma Sarki Charles III na Birtaniya za a yi masa tiyata a mafitsara.

Ana cikin haka kuma sai ga wani mummunan labarin, inda aka bayyana cewa tsohuwar matar Yarima Andrew, Sarah Ferguson (Gimbiyar York) na fama da kansar fata.

Yanzu kuma an bayyana cewa Sarkin na Ingila na ɗauke da cutar kansa. Sai dai lamarin ya bar mutane na yin wasu tambayoyi - wace irin cutar kansa ce? Ya muninta? Me zai faru a gaba: Sai dai babu wanda ya san amsar.

Yanzu zai iya yiwuwa iyalan masarautar su zaɓi sanar da irin wannan labari a shafin sada zumunta a madadin yadda aka saba a baya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To amma dai ko ta wace hanya ce, wannan mummunan labari ne ga iyalin masarautar.

A yanzu iyalan ba su cikin karsashi kamar yadda suka a shekara ɗaya da ta gabata, lokacin bukukuwan rantsar da Sarki.

To amma lokuta na damuwa irin wannan kan iya haɗa kan mutane wuri guda.

Nan take Yarima William ya bayyana cewa zai tafi Birtaniya domin ganin mahaifin nasa, inda zai taho daga Amurka cikin ƴan kwanaki masu zuwa.

Wannan na nufin dawo da sadarwa kai-tsaye. A baya, Yarima Harry ya kira mahaifin nasa a waya lokacin murnar cikar sa shekara 75 a duniya.

Saɓanin da yake samu ga alama tana tsakaninsa ne da yayansa da kuma jaridu, ba mahaifinsa ba.

Tuni dai Yarima William ya koma aiki kamar yadda ya saba bayan tiyatar da aka yi wa maiɗakinsa kuma ana sa ran yanzu zai karɓi ayyuka da dama na masarautar da kuma bayyana a bainar jama'a a madadin mahaifin nasa. Sai dai yana fuskantar ƙalubalen jinyar da mahaifinsa da kuma matarsa ke yi.

Yarima William shi ne mai jiran gadon sarauta, kuma mutane za su ran ganin ya yi irin abin da mahaifinsa ya yi cikin ƴan shekarun da suka gabata, lokacin da ya riƙa taimaka wa mahaifiyarsa.

Hankali zai karkata sosai ga Yarima Harry lokacin da zai bayyana a gaban jama'a cikin makon nan.

Zai ci gaba da tunanin rashin lafiyar maiɗakinsa, kuma fadar Buckingham za ta yi kewar ta kasancewar tana daga cikin mutane mafiya tabbas waɗanda iyalan masarautar ke dogaro da su a lokacin baƙin ciki, sai dai yanzu ta kwashe watanni ba ta gudanar da ayyukanta.

Ita kuwa Sarauniya Camilla ta kasance ba ta cikin masarautar tsawon shekaru 20 da suka gabata. Za ta ci gaba da bin abubuwa a hankali.

Ta kasance ɗaya daga cikin iyalan masarauta da ke gudanar da ayyuka, inda ta gudanar da wasu ayyukan a makon da ya gabata.

Yayin da Yarima Harry da Yarima Andrew suka ajiye muƙamansu, Sarki Charles da kuma Gimbiya Kate a yanzu ba su iya gudanar da ayyukansu yadda suka saba, batun da za a fi tattaunawa tsakanin al'umma shi ne yadda yawan masu tafiyar da lamurra a masarautar ke raguwa.

Iyalan masarautar na ƙara tsufa da kuma yin rauni. Yarima da Gimbiyar Wales ne kawai a cikin iyalan masarautar da ke riƙe da muƙamai suke da shekaru ƙasa da 50 a duniya.

A ɓangarensa, Sarki Charles, wanda shi ne a tsakiyar lamarin, zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na shugaban gwamnati, ciki har da sanya hannu a takardu da ganawa ta sirri.

Sai dai hakan na nufin ba zai riƙa yin ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara masa karsashi ba, wato haduwa da tattaunawa da mutane daban-daban.

Bayan kammala kowace ganawa da manyan mutane ko ƙaddamar da wani aiki, yakan so ya bayyana a gaban al'umma tare da ɗaga musu hannu.

Yanzu za a dakatar da duk waɗannan abubuwa, amma na har zuwa wane lokaci? Babu wanda ya sani.

Hakan na nufin cewa duk da muna gani da samun bayanai sosai game da masarautar amma har yanzu akwai abubuwa da dama da ba mu sani ba.

A wannan karo dai iyalan masarauta sun sanar da cewa za a yi wa sarkin aiki a mafitsara kuma an gano yana fama da cutar kansa, wani abu da ke alamta ƙoƙarin masarautar na yi wa al'umma bayani tare da faɗakar da al'umma musamman maza wajen ganin sun yi gwajin cutar.

To amma wannan wani yunƙuri ne na bayyana kadan daga cikin bayanan masarautar wanda daga baya ya ƙara buɗe wa mutane abubuwan da ke faruwa.

Sai dai babu wanda ya san me zai faru a gaba.