Hanyoyi huɗu da Najeriya za ta bi don kauce wa faɗawa matsalar yunwa

A makon da ya gabata ne Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi gargaɗin cewar 'yan Najeriya miliyan 82 - kimanin kashi 64 na 'yan ƙasar - ka iya fuskantar matsalar yunwa nan da shekara ta 2030.

Hukumar Abinci da Aikin Gona ko kuma Food and Agriculture Organization (FAO) ta ce alƙaluma daga binciken shekara-shekara kan abinci sun nuna cewa nan da shekaru masu zuwa lamurra za su ta'azzara a ƙasar.

Haka kuma MDD ta yi kira da gwamnatin ƙasar ta magance matsalar sauyin yanayi, da matsalar ƙwari masu lalata amfanin gona domin shawo kan matsalar.

“Sakamakon binciken ya tayar da hankali, kusan mutum miliyan 82 ne za su fuskanci yunwa nan da 2030,” kamar yadda jaridun Najeriya suka ambato jami'in Majalisar, Taofiq Braimoh na bayyanawa a wurin wani taro kan haɓaka ayyukan noma a Abuja.

Tuni matsalar ƙarancin abincin ta fara ɗaiɗaita wasu 'yan Najeriya. Wasu da BBC ta zanta da su sun bayyana yadda suke kwana su wuni ba tare da cin wani abincin kirki ba.

A gefe guda kuma, gwamnatin ƙasar ta fara ɗaukar wasu daga cikin matakan, ciki har da niyyar ƙirƙirar sabuwar ma'aikata ta inganta kiwo da Shugaba Bola Tinubu ya bayyana ranar Talata bayan ya ƙaddamar da kwamatin da zai yi aiki kan hakan ƙarƙashin jagorancinsa.

To ko waɗanne hanyoyi ne suka kamata Najeriya ta bi domin guje wa faɗawa gagarumar matsalar yunwa?

Dr Abubukar Suleiman shi ne tsohon mataimakin shugaban FAO a Najeriya, kuma ya bayyana matakai biyar da suka kamata a ɗauka.

Abubuwan da ke ta'azzara matsalar

Yanzu haka mutum miliyan 31 ne ke cikin matsananciyar yunwa, a cewar rahoton FAO, waɗanda suke cikin aji na uku cikin biyar na ma'aunin yunwa.

Sai kuma miliyan 81 da ke fuskantar barazanar shiga yunwar nan da shekara shida masu zuwa, in ji rahoton hukumar.

"Babbar matsalar da ta haifar da halin da ake ciki ita ce tattalin arzikin ƙasa," in ji Dr Suleiman. "Ɗagawar farashin abinci da sauran kayayyaki sun taimaka sosai."

Ya ƙara da cewa tashin farashin man fetur ta sa kayayyaki sun ƙara tsada saboda akan yi jigilar akasarin kayan noma ta tituna.

"Matsalar tsaro ma na saka mutane su yi gudun hijira, wanda ke sa su rasa gonakinsu," a cewarsa.

Matakan da suka kamata a ɗauka

Dr Abubukar Suleiman ya ce akwai matakai na gaggawa da kuma masu dogon zango da suka kamata a ɗauka. Ya yi bayani kamar haka:

Tallafi

Masanin ya ce akwai mutanen da suka riga suka galabaita, waɗanda hukumar WFP ta saka su cikin aji na biyu, da na uku a matakin matsalar yunwa.

Irin waɗannan lallai ne sai an taimaka musu, a ba su tallafi saboda ko ma me aka yi musu ba su da yadda za su yi su samu abincin saboda ba su da hanyar samun.

Kyautata tsaro

Akwai ƙarancin noma da kuma zuba jari a harkar noman kansa yanzu saboda matsalar tsaro.

Mutane kan yi noma amma ba su amfana da shi saboda wasu 'yanbindiga kan ƙwace amfanin ko kuma su ce sai sun biya haraji. Irin wannan kan sa noman ya ragu.

Sauya dabarun noma

Akwai buƙatar a sauya dabarun noma, musamman dabarun noman rani da kuma na ajiyarsa ta yadda abinci ba zai lalace a gona ko a rumbun ajiya ba.

Sannan sai an samar da iri na zamani waɗanda ba su buƙatar ruwa mai yawa.

Tallafa wa ƙananan manoma

Dole ne sai gwamnati ta tallafa wa ƙananan manoma saboda su ne ginshiƙin noma a Najeriya.

Ba wai gwamnati ba ta ba da tallafin ba ne, matsalar dai ba shi kaiwa ga manoma na ƙasa. Saboda dole sai an ƙara ƙoƙari.