An koma teburin tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan ƙwadago a Najeriya

Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook
An koma kan teburin tattaunawa game da matakan rage raɗaɗin cire tallafin man fetur tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya.
Wakilan gwamnati da manyan ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar ne ke ci gaba da tattaunawa da yammcin Litinin a fadar shugaban Najeriya game da matakan rage wa talakawan ƙasar raɗaɗi sanadin mummunan tasirin cire tallafin.
Litar man fetur ɗaya a Najeriya ta zarce N500 a yanzu saɓanin ƙasa da N200 da aka riƙa sayar da ita a baya.
Lamarin dai ya haddasa ƙarin tsadar kayayyaki da ayyuka a faɗin Najeriya.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa taron 'yan ƙwadagon da gwamnati na zuwa ne bayan wasu makamantansa kwanakin baya inda ɓangarorin biyu suka cimma matsaya, har ma 'yan ƙwadagon suka amince su jingine aniyarsu ta shiga yajin aiki ya zuwa Litinin ɗin nan don ci gaba da tuntuɓar juna.
Ana sa rai tattaunawar za ta kai ga cimma yarjejeniya game da buƙatun 'yan ƙwadago da kuma matakan rage raɗaɗi da gwamnati ta ƙuduri aniyar ɓullo da su.
A taronsu na baya, gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya guda biyu kamar Nigeria Labour Congress (NLC) da Trade Union Congress (TUC) sun amince da ci gaba da hawa teburin tattaunawa da gwamnati a ranar 19 ga watan Yuni.
Cikin jami'an da ke halartar taron akwai ayarin ƙungiyar ƙwadago ta NLC ƙarƙashin jagorancin shugabanta Mista Joe Ajaero da ayarin ƙungiyar TUC ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Festus Osifo.
Daga ɓangaren gwamnati kuma akwai shugaban ma'aikatan shugaban Najeriya Femi Gbajabiamila da Mai bai wa shugaban shawara na musamman kan harkar kuɗin shiga, Zachaeus Adedeji da mai ba da shawara na musamman kan harkar makamashi, Olu Verheijen da babban sakatare a ma'aikatar ƙwadago da samar da aikin yi Kachallon Daju.













