Ƙarin ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun ci alwashi shiga yajin aiki

NLC Mobilization

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya na ci gaba da amsa kiran uwar ƙungiyarsu ta NLC wadda ta yi kira ga ma'aikatan ƙasar su tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba saboda janye tallafin man fetur.

Cikin ƙungiyoyi na baya-bayan nan har da JUSUN - ƙungiyar ma'aikatan kotuna ta Najeriya wadda ta ce ta yanke shawarar shiga yajin aikin ne don nuna rashin amincewa da matakin sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Mataimakin sakataren JUSUN na ƙasa, Barista Saidu Magaji Ƙarƙaku ya shaida wa BBC cewa sun karɓi wasikar da NLC ta rubuta musu, kuma su ma za su rufe kotuna daga ranar Laraba.

"Eh, gaskiya ne, uwar ƙungiyar kwadago ta ƙasa ta zauna, kuma akwai wakilcin duka ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta a lokacin da ta ɗauki wannan matsaya ta shiga yajin aiki a ranar Laraba idan Allah ya kai mu," in ji shi.

Shawarar ta ƙungiyar JUSUN na zuwa ne bayan rahotanni sun ambato NLC na cewa ta rubuta wasiƙa don sanar da sauran rassanta musamman ƙungiyar ASUU da JUSUN game da buƙatar su shiga yajin aikin.

Mataimakin Sakataren na JUSUN ya ce la'akari da ganin yadda cire tallafin man fetur ɗin zai shafi kusan kowanne ɓangare na rayuwar al'umma a Najeriya.

"Ƙasar nan dai da ma abin da talaka za a ce a yau yana amfana da shi, bai wuce ya samu wannan ɓangare na man fetur cikin sauƙi ba, idan aka dubi duk sauran ɓangarorin rayuwa gaba ɗaya, babu wani guri inda talaka ke jin sauƙi".

"Babu asibitocinmu, babu tituna, ba ruwa, ba wuta, ba komai, ko ina aka duba a cikin ɓangarorin gwamnati, kusan babu abubuwan more rayuwa", a cewar Ƙarƙarku.

A ƙarshen mako ma, ƙungiyar ma'aikatan sashen wutar lantarki da ta 'yan jarida NUJ, duk sun bayyana aniyar shiga yajin aikin na NLC.

NLC ta ce ƙungiyoyi da dama ne zuwa yanzu suka nuna amincewarsu ta shiga yajin aikin ciki har da ƙungiyar ma'aikatan samar da man fetur da iskar gas ta ƙasa NUPENG wadda ta umarci jami'anta su rufe duk harkokin da suka shafi wannan fanni a faɗin Najeriya.

Ƙungiyoyi nawa ne suka bayyana aniyar shiga yajin aikin zuwa yanzu?

A wani saƙo da uwar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Tuwita, NLC ta ce tana ci gaba da gangami don wannan yajin aiki daga ranar Laraba.

Ta dai bayyana tallafin man fetur a matsayin "wata damfara" inda ta ce bai kamata kamfanin NNPC na 'yan kasuwa ya kasance wanda zai tsaida farashin mai a ƙasar ba.

Haka zalika, NLC ta ci gaba da wallafa sanarwar ƙungiyoyin da ta ce sun amsa kiranta na shiga yajin aikin.

A cikinsu akwai:

  • Ƙungiyar ma'aikatan samar da lantarki ta ƙasa (NUEE)
  • Ƙungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gas ta ƙasa (NUPENG)
  • Ƙungiyar ma'aikatan cibiyoyin ilmi NASU
  • Ƙungiyar ma'aikatan majalisun dokoki ta Najeriya (PASAN)
  • Ƙungiyar ma'aikatan jinya da ungozomomi ta ƙasa (NANNM)
  • Ƙungiyar ma'aikatan sufurin teku ta Najeriya (MWUN)
  • Ƙungiyar 'yan jarida ta Najeriya (NUJ)
  • Ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi ta Najeriya (NULGE)
Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

NLC ta ƙauracewa taro da gwamnati

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun farko dai, an gaza cimma matsaya tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya da kuma gwamnati game da batun janye tallafin man fetur, inda babbar ƙungiyar ƙwadagon ƙasar NLC ta ce tana kan ƙudurinta na tafiya yajin aiki daga wannan mako.

Bayanai dai sun ce NLC ta ƙauracewa taron da gwamnatin ƙasar ta kira a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ambato ƙungiyar tana cewa ba za ta yi wata tattaunawa da wakilan gwamnati ba, har sai an kafa halattaccen kwamiti.

Sai dai takwararta ƙungiyar TUC ta halarci taron, kuma ta buƙaci gwamnati ta koma kan tsohon farashin man fetur sannan ta ƙara yawan mafi ƙarancin albashin da ma'aikata ke karɓa a Najeriya.

Ta ce matuƙar ba haka ba, ɗaukacin 'ya'yanta a faɗin Najeriya su ma za su bi sahun wannan yajin aiki.

A ranar Lahadi ne gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sake kiran taro da ƙungiyoyin ƙwadagon don ci gaba da tattaunawa a ƙoƙarin ganin ba su shiga yajin aikin da suka ƙuduri aniyar tafiya ba.

Sai dai a tattaunawar da BBC ta yi da Kwamared Nasir Kabir, sakataren tsare-tsare na haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC, ya ce babu buƙatar ci gaba da tattaunawa da gwamnati.

"Babu abin da gwamnatin tarayya ta yi a kan sharuɗɗan da muka bayar cewa a dakatar da janye tallafin mai, don haka tun da gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki a ɓangarenmu ba gudu ba ja da baya.

Za mu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a fadin Najeriya baki daya" in ji Kwamared Nasir.

Dan kungiyar NLC

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto, Dan kungiyar NLC

Kwamared Nasir Kabir, ya ce “Mun bayar da sharuɗɗa kamar na gyara matatun mai ta yadda za a riƙa samar da man fetur daga wajensu a cikin ƙasar, sannan shi kansa tallafin ba za a cire shi ba, sai an kawo abin da zai sauƙaƙawa mutane halin wahalhalun da za su iya shiga”.

Ya ce ba su ji daɗi ba saboda gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin janye tallafin man fetur ba tare da kawo abubuwan da za su sauƙaƙa matsin rayuwar ‘yan ƙasar ke ciki.

Sakataren tsare-tsare na haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC, ya ce batun cewa nan gaba za a ga alfanun janye tallafin man fetur a Najeriya, duk zance ne kawai.

"A baya ma an yi haka amma ba abin da aka gani, saboda haka ko shakka babu a yanzu ma babu wani alfanu da za a gani, illa jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali” in ji shi.

Kwamared Nasir Kabir, ya ce za su yi wannan yajin aiki ne don nuna fushinsu a kan karin farashin mai da aka yi, wanda kuma duk wani mai kishin Najeriya zai goya musu baya.

A cewarsa, "kowa ya san ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali, sannan kuma a zo a ƙara musu wata ukubar, wannan sam ba daidai ba ne”.

Tun bayan sanarwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi ta cire tallafin man fetur, farashin man fetur ya ninka da kusan kashi 200%.