Yajin aikin NLC: Abubuwan da suka kamata ku sani kan yarjejeniyar 'yan ƙwadago da gwamnatin Najeriya

Asalin hoton, NLC
Da safiyar wannan Litinin aka wayi gari da samun labarin janye yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya ta sha alwashin gudanarwa.
Kungiyar ta bayyana janyewa daga yajin aiki ne a wata sanarwar hadin-gwiwa dauke da sa hannu shugabannin kwadago na kasa da bangaren gwamnatin, bayan sun kwashe talatainin dare suna tattaunawa.
Ta kuduri aniyyar tafiya yajin aikin ne domin tilasta wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta janye karin da aka yi na farashin fetur da hasken wutar lantarki da kuma tsadar kayan masarufi.
Sanarwar da karamin minista a ma'aikatan kwadago da samar da ayyuka na kasa, Fetus Keyamo, ya fitar ta ce "bangarorin sun amince su kafa kwamitin kwararru wanda ya kunshi ministoci, da shugaba a bangaren ma'aikatu, cibiyoyi da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, wanda za su yi aiki tare na tsawon mako biyu, daga wannan Litinin din, 28 ga watan Satumba 2020."
Kwamitin zai yi nazari da fayyace halascin sabbin tsare-tsare da karin kudade da kuma hauhawan farashi, kalubale da lokacin da aka diba domin cimma hakan.
Mambobin kwamitin sun kunshi, Karamin minista a ma'aikatar kwadago da ayyuka, Mr Fetus Keyama, Minista a ma'aikatar lantarki, Mr Godwin Jedy-Agba, Farfesa James Momoh, shugaban hukumar da ke sa ido kan wutan lantarki NERC, Injiniya Ahmed Rufai Zakari.
Sauran su ne mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsare-tsare da gine-gine, Dr. OnohoOmhen Ebhohimhen, na kungiyar (NLC); Kwamred Joe Ajaero, mamba a (NLC); Comrade Chris Okonkwo, mamba a (TUC), da wakilan kamfanonin bayar da wutar lantarki.
Aikin da kwamitin zai gudanar cikin mako biyu.
Me kwamitin zai yi?


Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin zai yi nazari kan halasci ko akasin haka kan sabbin tsarin biyan kudin wutar lantarki.
Aikin kamfanonin rarraba wutar lantarki da sabbin tsare-tsare na biyan kudin wutar lantarki.
Zai yi nazari da bai wa gwamnatin shawara kan matsalolin da suka haifar da tsaiko wajen raba sabbin mitocin wutar lantarki miliyan shida.
Zai yi bincike kan abin da doka ta ce karkashin kundin ayyukan NERC da fadada shi ta yadda kungiyoyin kwadago za su samu wakilci.
Sannan za a sake nazari kan yadda gwamnati ta sayar da hannun jarin wutar lantarki ga kamfanoni, matsayin ma'aikata ga rukunin kamfanonin da ke rarraba wutar lantarki.
Sannan za a yi nazari mai zaman kansa kan ayyukan samar da wutar lantarki kamar yadda yake kunshe a takardar sayar da kamfanin samar da wuta kafin karshen shekara ta 2020, da wakilcin kungiyar kwadago.
Kazalika za a kafa kungiyar bayar da shawarari kan kwadago - National Labour Advisory Council, NLAC, kafin karshen shekara ta 2020 domin shiga tsakani da daidaita matsaloli tsakanin bangaren ma'aikata da gwamnati, musamman batutuwa masu wuyar sha'ani.
Ana sa ran kwamitin da zai yi wannan nazari ya bayar da rahotansu a cikin mako biyu.
Abubuwan da aka cimma kawo yanzu
Kamfanonin rarraba wutar lantarki za su dakatar da amfani da sabon tsarin biyan kudin lantarki, zuwa lokacin kammala aikin kwamitin nan da mako biyu.
A fannin karin farashin man fetur, gwamnatin za ta sanar da sabon farashi a cikin makonni biyu masu zuwa.
Za a samar da sabon tsarin tallafin noma karkashin kungiyiyon NLC da TUC da babban bankin kasa da ma'aikatar noma.
Gwamnati ta ce za ta cire haraji kan albashi mafi karanci, domin rage radadin tasirin sabbin tsare-tsarenta kan mai karamin karfi.
Gwamnatin ta alkawarta samar da manyan motocin bas 133 cikin gaggawa a manyan tittuna biranen kasar da ake da bukata, sannan daga bisani za ta fadada zuwa dukkanin jihohi da kananan hukumomi kafin Disambar 2021.
A fannin gidaje, za a bai wa ma'aikata kashi 10 cikin 100 na gidajen da gwamnati ke ginawa karkashin ma'aikatar gidaje da kudade ta hannun NLC da TUC.












