Euro 2024: Austria ta jagoranci Faransa da Netherlands a Rukunin D

Austria

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Austria ce ta ɗaya a rukuninsu duk da kasancewar Faransa da Netherlnads a ciki

Austria ta yi rawar gani da ta kai ta ga doke Netherlands 3-2 da kuma samun gurbin zagaye na biyu a gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024.

Tawagar ta Ralf Rangnick ta ƙare a matsayin ta ɗaya a Rukunin D da ya ƙunshi Faransa da Poland.

Da ma tuni Netherlands ɗin ta samu gurbin zagayen 'yan 16 amma dai za su wuce ne a matsayin ɗaya daga cikin tawagogi huɗu da suka masu hazaƙa da suka ƙare a mataki na uku, sai kuma Faransa ta biyu.

Austria ta cancanci wanna nasara saboda yadda suka yi wasa da ƙarfin zuciya da kuma yunwar neman nasara.

Donyell Malen ne ya fara ci wa Austria ƙwallo a minti na 6 bayan ya ci gidansu, sai Gakpo ya farke wa Netherlands jim kaɗan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Schmid ya sake ci wa Austria ta biyu, yayin da Depay ya sake farke ta, inda a ƙarshe Baumgartner ya ci ta nasarar ana saura minti 10 a tashi daga wasan.