Brazil ta fara Copa America da canjaras

Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Brazil na Rukunin D tare da Colombia da Costa Rica da Paraguay

Brazil ta fara wasan gasar Copa America da canjaras tsakaninta da Costa Rica a birnin Los Angeles na Amurka.

Duk da cewa wasan ya tashi babu ci, Brazil mai kofin guda tara ce ta riƙe kashi 74 cikin 100 na ƙwallon, tare da buga shot 19 amma duk da haka ba ta iya zira ƙwallo a raga ba a wasan Rukunin D.

Marquinhos ya jefa ƙwallo a raga a minti na 30 amma sai na'urar VAR mai taimaka wa alƙalin wasa ta ce an yi satar gida.

Kociyan Brazil Dorival Jr ya saka matashin ɗan wasan Real Madrid Endrick da kuma Savio daga baya, amma ba su iya aikata komai ba.

Lucas Paqueta ya bugo tirke amma kuma ya ɓarar da dama biyu masu kyau a filin wasa na SoFi da ke birnin.

Sakamakon ya bar Brazil a mataki na biyu da naki ɗaya, yayin da Colombia ta doke Paraguay 1-0 kuma ta ɗare saman teburin rukunin na D.