'Muna rayuwa a Rwanda tamkar a gidan yari'

Azhagu da Mayur
Bayanan hoto, Azhagu da Mayur sun isa Rwanda daga tsibirin Diego Garcia na Birtaniya
    • Marubuci, Alice Cuddy & Swaminathan Natarajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Rwanda

Wasu 'yan cirani da aka kuɓutar a tekun India sannan gwamnatin Birtaniya ta aike da su zuwa Rwanda sun bayyana yadda aka ci zarafinsu ta hanyar lalata da barazanar da suka fuskanta.

Yayin da jam'iyyun siyasar Birtaniya suka samu rarrabuwar kai kan shirin gwamnatin ƙasar mai cike da ce-ce-ku-ce na aika masu neman mafaka daga Birtaniya zuwa Rwanda, su waɗannan mutane tuni suna Rwanda fiye da shekara guda.

BBC ta ziyarci ƙasar da ke gabashin Afirka ta tsakiya domin haɗuwa da su.

Mutanen sun ce suna jin tamkar an ware su sannan kuma ba sa cikin kariya, sannan kuma su kan fuskanci matsala wajen samun magungunan da suke buƙata musamman na raunukan da suka samu sakamakon cin zarafi da fyaɗen da suke fuskanta.

Gwamnatocin Birtaniya da Rwanda sun amince da biyan kowane ɗaya daga cikinsu dala 50 a kowane wata domin sayen abinci da sauran muhimman abubuwan buƙata, to amma bisa tsarin yarjejeniyar zamansu, ba su da damar yin aiki a ƙasar.

Duka mutanen huɗu sun ce suna fuskantar cuzgunawa da cin zarafi na lalata a kan titi, sun ce suna jin tamkar a ''gidan yari'' suke rayuwa, suna fargabar fita waje, yayin da suke jiran gwamnatin Birtaniya ta samar musu wurin zama na dindindin.

''Rwanda ta zame mana tamkar gidan yari'', kamar yadda ɗaya daga ciki ya shaida wa BBC.

Mutane - waɗanda dukan su 'yan ƙabilar Tamil ne daga Sri Lanka - an gaggauta mayar da su Rwanda ne domin samar musu maganguna, bayan da uku daga cikinsu suka yi yunƙurin kashe kansu.

Mutum na huɗu mahaifi ne ga ɗaya daga cikin 'yan ciranin. A yanzu bayan ficewar su daga asibitin sojoji, suna zaune a wani gida mai ɗaki biyu a wata unguwa da ke wajen Kigali babban birnin Rwanda .

Hukumomin Birtaniya ne dai suka ɗauki nauyin gidan da suke zaunen.

Kigali
Bayanan hoto, Birtaniya ce ke ɗaukar nauyin kuɗin gidan da suke zaunen.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Matsayin da suke da shi a shari'ance a Ruwanda bai daidai yake da na masu neman mafaka da aka taso daga Birtaniya ba - amma lauyan da ke wakiltar biyu daga cikinsu ya ce "munanan abubuwan da suka fuskanta ya haifar da damuwa sosai" kan ko Rwanda ka iya ɗaukar nauyin masu neman mafaka ga" 'yan gudun hijira masu rauni sosai".

Wata babbar jami'ar Rwanda ta shaida wa BBC cewa tana da "cikakken yaƙini" kan tsarin kula da lafiyar ƙasarta kuma wasu baƙin hauren na nuna damuwa game da tsaron lafiyarsu.

Ta kara da cewa "akwai 'yan ƙasashen waje da ke ci gaba da rayuwa a nan."

Domin ɓoye sunan 'yan ciranin, mun sauya sunayensu.

Ba wanda a cikinsu ya yi ƙoƙarin shiga Birtaniya - maimakon haka sun shigar da buƙatar neman mafaka a Diego Garcia, wani tsibiri mai nisa na Birtaniyya da ke cikin Tekun Indiya da aka yi amfani da shi a matsayin sansanin sojin Birtaniya da Amurka.

Suna daga cikin gomman mutanen da suka isa tsibirin a watan Oktoban 2021, kamar yadda BBC ta ruwaito a baya.

Sun ce suna yunƙurin tsere wa cuzgunawa don haka suke yunƙurin shiga jirgin ruwa zuwa Canada domin neman mafaka.

Mutane huɗu sun ce sun gamu da cin zarafi da cuzgunawa a ƙasashensu na ainihi.

Mutanen huɗu da muka haɗu da su a Rwanda sun ce an sha azabtar da su da cin zarafi ta hanyar lalata da su a ƙasashensu - wasu saboda alaƙarsu da 'yan tawayen Tamil Tiger, waɗanda suka sha kaye a yaƙin basasar Sri Lanka shekara 15 da suka wuce.

Wasu na kallon waje
Bayanan hoto, Khartik da 'yarsa, Lakshani sun ce ko waje ba sa fita, saboda fargabar cin zarafi da cuzgunawa.

A cikin wani gida mai ɗakuna biyu, da ke gefen wani titi mai cike da datti, Azhagu ya ce an gano yana fama da matsananciyar cutar damuwa sakamakon damuwa kan rashin tabbas game da makomarsa.

“Ba ma samun magungunan da suka dace. Muna da matsalolin da suka shafi damuwa,'' in ji matashin mai shekara 23.

“A duk lokacin da muke je muka faɗa wa likitoci matsalarmu, ba sa taimaka mana.”

Ya ce likitocin Rwanda kan yi masa tsawa, ya kuma ce a wani lokaci da ya ji wa kansa rauni, ya ce an yi barazanar kama shi tare da mayar da shi tsibirin Diego Garcia.

Mayur, mai shekara 26, da suke zaune ɗaki ɗaya da Azhagu ya ce akan ba shi shawarwari. ''Bana samun magungunan da suka dace ba na samun damar yin cikakkiyar hira. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba na son zuwa asibiti.''

Wani lauya daga kamfanin Leigh Day na Birtaniya ya ce ''wani bincike mai zaman kansa na tabbatar da cewa duka mutanen da yake karewa suna fama da matsananciyar rashin lafiya a Rwanda''.

Mun tuntuɓi asibitin sojojin inda duka mutanen ke karɓar magani, to amma sai suka ce mu tuntuɓi gwamnatin Rwanda.

To amma babbar jami'ar Rwanda da ke kula da yarjejeniyar miƙa masu neman mafaka daga Burtaniya, Doris Uwicyeza Picard, ta kare tsarin kiwon lafiyar ƙasarta - ta ƙara da cewa ana kula da baƙin hauren " iya yadda za mu iya".

Doris Uwicyeza Picard
Bayanan hoto, Damuwa kan lafiyar bakin haure “ba kowa ne ke sani ba, ba duka 'yan Rwanda ne suka sani ba," in ji Doris Uwicyeza Picard

Hukumomin kula da yankunan Birtaniya da ke tekun Indiya da gudanar da Diego Garcia, (BIOT ) sun amince da buƙatar uku daga cikin bakin hauren – samari biyu da mace ɗaya, Lakshani – na kare lafiyarsu.

Majalisar Dinkin Duniya da lauyoyin da ke kare mutanen sun ce hakan ya ba su matsayin 'yan gudun hijira. Mutum na huɗu a cikinsu - mahaifin Lakshani, Khartik - an ba shi izinin raka 'yarsa.

Hakan na nufin ba za a iya mayar da su Sri Lanka ba, amma Birtaniya ta ce ba za ta karɓe su ba. Gwamnatin Conservative ta shaida wa BBC a bara cewa BIOT "ba za ta iya zama wata kofa ga Birtaniya ba".

Mutanen sun nuna mana takardun shari'a da sakonnin WhatsApp da na imel da wasiƙun da suka rubuta wa jami'an Burtaniya, ciki har da Firayim Minista Rishi Sunak, a shekarar da ta gabata suna neman a fitar da su daga ƙasar.

"Ban san shekara nawa za mu yi rayuwa a matsayin fursunonin gwamnatin Birtaniya ba tare da 'yanci ba," in ji wani sako.

Duka mutanen huɗu sun shaida mana cewa cuzgunawar da ake yi musu ya tilasta musu barin gidajensu.

A cikin gidan Lakshani, an ja labule mai launin toka a kan shingen tagogin - yana rufe dakin daga waje.

“Ba mu fita waje. Koyaushe muna jin tsoro,” in ji matashiyar mai shekara 23, a lokacin da muka ziyarce su da Khartik, mai shekara 47. “Ba ni da mata [da zan yi magana da] a nan. Babu abokai."

Azhagu da Mayur
Bayanan hoto, Azhagu da Mayur sun ce an yi yunƙurin yin jima'i da su a kan titi

Sun ce a lokuta da dama an yi yunƙurin shiga gidan nasu. Sun nuna mana bidiyon da ke nuna yadda wasu suka yi yunƙurin shiga gidansu da makwabta suka kama.

Sun kuma tuno da wani abin da ya faru a wani titi da ke kusa, inda suka ce, wasu gungun maza ne suka raba su kuma suka yi ƙoƙarin taba Lakshani yayin da suke amfani da "kalmomin da ba su dace ba".

Azhagu ya faɗa mana cewa akwai lokacin da aka kai su kan titi shi da Mayur. “Baƙi suka riƙa tambayarmu, suna cewa ''zan iya saduwa da ku?’ Mutane suna ta dariya. Muka ruga zuwa asibiti.”

To sai dai wakilan jami'an ƙasar ba su ce komai ba alokacin da BBc ta tuntuɓe su kan batun.

Taswira
Bayanan hoto, Baƙin-hauren na kan hanyarsu daga India, a lokacin da sojojin ruwan Birtaniya suka kuɓutar da su tare da kai su tsibirin Diego Garcia

Mutanen huɗu sun shaida mana cewa ba su tuntuɓi ‘yan sandan Rwanda don neman agaji ba. Dukkansu sun ce sun ki amincewa da jami'an tsaro masu sanye da kayan sarki bisa ga abubuwan da suka faru na cin zarafi a baya.

Misis Picard ta ce ''ba ta da tabbaci kan yadda za mu taimaka idan ba a tunkari hukumomi ba''.

Shawarar tafiye-tafiye da gwamnatin Birtaniya ta bayar ta ce, akwai ƙarancin aikata laifuka ba su da yawa a Rwanda, amma akwai ƙananan laifuka na sace-sace, irinsu fizgen jakankuna ko satar waya da sane a Kigali.

Khartik na girki
Bayanan hoto, Khartik da Lakshani sun ce yadda suke rayuwa a Rwanda ya fi yadda yake a Diego Garcia
Kan hanya a Rwanda
Bayanan hoto, Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Birtaniya ta samar da mafita kan halin da mutanen ke ciki a Rwanda

Jam'iyyar Conservative ta Birtaniya da ta Labour da ke mulki a ƙasar da duka ke hasashen lashe zaɓen ƙasar da ke tafe, za su yi ƙoƙarin samar da mafita kan makomar baƙin haure na Diego Garcia a Ruwanda ko kuma abin da za su nemi yi da su idan suka ci mulki.

Bangarorin biyu dai sun yi alƙawarin kawo cikas ga baƙin haure, amma jam'iyyar Labour ta ce za ta yi watsi da shirin 'yan Conservative na jigilar baƙin haure daga Birtaniya zuwa Rwanda.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Birtaniya ta "amince da mafita" ga mutanen na Rwanda, da waɗanda ke Diego Garcia, kamar yadda dokokin duniya suka tanada.

Yayin da suke zaman jira, baƙin-hauren na ci gaba da tunanin makomarsu.

"Muna mamakin ko za mu iya gode wa Birtaniya kan ceton rayukanmu lokacin da muka isa Diego Garcia, ko kuma mu yi fushi da su don sanya rayuwarmu cikin rudani," in ji Mayur.