Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan bikin Easter a faɗin duniya
Fafaroma Francis ya jagoranci gabatar da bukukuwan Easter, inda ya yi jawabi kan muhimmancin zaman lafiya a gaban dandazon mutane a fadar Vatican, duk da damuwa da ake nunawa kan batun lafiyarsa.
A gefe guda, ana ci gaba da gudanar da shagulgula a faɗin duniya domin bikin Easter wanda yake da muhimmanci ga mabiya addinin Kirista.
Yesu Almasihu ya tashi daga cikin matattu ranar Lahadi, bayan gicciye shi a ranar Juma'a, kamar yadda littafin tsohon alkawari ya bayyana. Ya zama wajibi ga kowane Kirista ya halarci taron addu'o'i ranar Asabar da yamma da kuma Lahadi.
Fafaroma Francis ya halarci taron addu'o'i na cikin dare na tsawon sa'o'i biyu a ranar Asabar da yamma.
An nuna damuwa kan batun rashin lafiyarsa lokacin da bai samu damar halartar wani maci na addu'o'i ba ranar Juma'a.
Sai dai, Fafaroma mai shekara 87, ya gabatar da addu'a na dogon lokaci da kuma yin wankan tsarki.
Mutane da dama a faɗin duniya sun gudanar da bikin Easter, ciki har da Philippines inda masu ibada suka taru don ganin yadda ake murnar biki na bana.
Bikin Easter dai yana da muhimmanci a kalanda ta mabiya ɗarikar Katolika wanda kuma mutum biliyan 1.4 ke bi a faɗin duniya.
A cocin St Sebastian a Katuwapitiya, da ke Sri Lanka, wani fasto ya gabatar da jawabi ga mabiya addinin Kirista.
An kuma gudanar da taron addu'o'i a faɗin birane da kuma garuruwa da dama na Turai.
Dukkan hotuna suna da hakkin mallaka.