Hotunan bikin Easter a faɗin duniya

Fafaroma Francis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fafaroma Francis ya yi kira da kakkausar murya na ganin an kawo karshen yaƙi a Gaza da Ukraine

Fafaroma Francis ya jagoranci gabatar da bukukuwan Easter, inda ya yi jawabi kan muhimmancin zaman lafiya a gaban dandazon mutane a fadar Vatican, duk da damuwa da ake nunawa kan batun lafiyarsa.

A gefe guda, ana ci gaba da gudanar da shagulgula a faɗin duniya domin bikin Easter wanda yake da muhimmanci ga mabiya addinin Kirista.

Bikin Easter

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dubun dubatar masu ibada ne suka taru a dandalin St Peter's domin jin sakon Fafaroma Francis na bikin Easter yau Lahadi.
Easter

Asalin hoton, Reuters

Yesu Almasihu ya tashi daga cikin matattu ranar Lahadi, bayan gicciye shi a ranar Juma'a, kamar yadda littafin tsohon alkawari ya bayyana. Ya zama wajibi ga kowane Kirista ya halarci taron addu'o'i ranar Asabar da yamma da kuma Lahadi.

Fafaroma Francis ya halarci taron addu'o'i na cikin dare na tsawon sa'o'i biyu a ranar Asabar da yamma.

An nuna damuwa kan batun rashin lafiyarsa lokacin da bai samu damar halartar wani maci na addu'o'i ba ranar Juma'a.

Fafaroma Francis

Asalin hoton, Reuters

Sai dai, Fafaroma mai shekara 87, ya gabatar da addu'a na dogon lokaci da kuma yin wankan tsarki.

Mutane da dama a faɗin duniya sun gudanar da bikin Easter, ciki har da Philippines inda masu ibada suka taru don ganin yadda ake murnar biki na bana.

Fafaroma Francis

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dandazon mutane a Philippines sun taru domin kallon yadda ake gudanar da bikin Easter
Philippines

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A Manila, babban birnin ƙasar, yara ne suka yi shiga irin ta mala'iku da kuma yin addu'a.
Bikin Easter

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A can lardin Kiberia na ƙasar Kenya, masu ibada ne suka taru domin kunna kendura
Bikin Easter

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Nan, limaman coci ne suke jagoranci taron addu'o'i a Nairobi kusa da wani wuta da aka kunna a wajen majami'ar
Bikin Easter

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata mata lokacin da ta halarci taron addu'a na bikin Easter ranar Lahadi a cocin Holy Trinity Cathedral a Karachi, da ke Pakistan
Bikin Easter

Asalin hoton, Getty Images

Bikin Easter dai yana da muhimmanci a kalanda ta mabiya ɗarikar Katolika wanda kuma mutum biliyan 1.4 ke bi a faɗin duniya.

A cocin St Sebastian a Katuwapitiya, da ke Sri Lanka, wani fasto ya gabatar da jawabi ga mabiya addinin Kirista.

An kuma gudanar da taron addu'o'i a faɗin birane da kuma garuruwa da dama na Turai.

Bikin Easter

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Archbishop Pierbattista Pizzaballa, ya jargoranci taron addu'o'i a cocin Holy Sepulchre da ke Jerusalem
Bikin Easter

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mai ibada lokacin da yake sumbatar gicciye yayin taron addu'o'i na cikin dare a cocin Grand Immaculate a Al-Hamdaniya, da ke Iraqi
Bikin Easter

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu mahaya dawaki sun caɓa musu ado yayin da suke rera wakoki na gicciye Yesu Kiristi a Jamus

Dukkan hotuna suna da hakkin mallaka.