Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda duniya ta manta da garin Chibok tare da ƴanmatan makaranta da aka sace
- Marubuci, Azeezat Olaoluwo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC reporter
- Aiko rahoto daga, Chibok, Nigeria
A watan Afrilun 2014, garin Chibok da ke arewa maso gabashin Najeriya ya yi suna a duniya bayan sace mata ƴan makaranta 276 da aka yi da kuma yunƙurin dawo da ƴan matan na #bringbackourgirls duniya wanda ya ja hankalin mutane da dama a duniya.
Bayan shekara goma, barazanar da ƙungiyoyi masu tayar da ƙayar baya ke ci gaba da yi na yin illa ga rayuwar mutane da dama a garin.
Yayin da take share hawaye a fuskarta, Esther Yakubu ta tuna yadda rayuwa ta kasance ba tare da ɗiyarta Dorcas ba.
''Yau shekaru 10 kenan da ƴata ke hannun ƴan Boko Haram. Lamarin ba shi da sauƙi ko kaɗan. Mutane na cewa na ci gaba da rayuwa, cewa ina da wasu yaran, amma duk lokacin da nake ni kaɗai, ina tunanin ta.''
Ganin kayan Dorcas a gida koyaushe yana haifar da tunanin abubuwan takaici kuma hakan ba zai bari ta warware daga ɓacin rai ba.
Esther ta yanke shawarar kawar da kayan, sai dai ta bar ƴan tsirarun hotuna.
'Na kyautar da kayanta ga mutanen da ba mazauna Chibok ba ne don ka da kayan su kasance kusa da ni. Ba na son ganin su ne kawai."
A daren ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne ƙungiyar Boko Haram ta sace ƴan mata 276 a makarantar kwana da ke garin Chibok.
Satar da aka yi ta haifar da wani yunƙuri a shafukan sada zumunta mai suna #BringBackOurGirls, wanda ya haɗa da uwargidan tsohon shugaban Amurka Michelle Obama, da wadda ta lashe kyautar Nobel, Malala Yusufzai, da dai sauran fitattun mutane.
Bayan shekara goma, an kuɓutar da ƴan mata da dama, wasu kuma sun yi nasarar tserewa. Duk da haka, 87 daga cikin 276 da aka yi awon gaba da su ba a san inda suke ba.
Dorcas na ɗaya daga cikin ƴan matan da suka ɓace wadda ta kasance ƴar shekara 16 kacal a lokacin da aka sace ta.
Ga mahaifiyarta Esther, rashin tabbas ɗin da ke tattare da rashin sanin makomarta na kawo mata cikas wurin ci gaba da rayuwarta.
''Ina so gwamnati ta bar ƴan matanmu su samu ƴancin dawowa gida. Muna so mu ga waɗanda suke da rai don mu ɗan yi farin ciki. Waɗanda ba su da rai kuma, sai ku sanar da mu saboda mu haƙura.
Esther ba ta sami wani bayani a hukumance kan inda ake tsare da ɗiyarta ba amma dai ta fito a wani bidiyon ‘tabbacin rayuwa’ da masu garkuwa da mutanen suka yi a shekarar 2016.
A cikin wannan bidiyon, Dorcas ta gabatar da kanta a matsayin Maida, sabon sunan da waɗanda ke tsare da ita suka saka mata.
"Idan Dorcas za ta ji ni yanzu, zan gaya mata ina raye kuma har yanzu garin Chibok yana nan, domin ta yi marmarin dawowa gida ta gan mu."
Kaiwa garin Chibok
Bayar da labari daga wannan yanki mai nisa da ke arewa maso gabashin Najeriya tafiya ce mai tsawo da wahalan gaske. Hanyar garin Chibok ta faro ne daga jihar Adamawa. Doguwar tafiya ce.
Mun wuce ta gefen wani turken sadarwa da ya faɗi. Jagoranmu ya shaida mana cewa ana zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta tumbuƙe ta don daƙile hanyoyin sadarwa. Ta yaya mutanen da ke zaune a nan za su nemi ɗauki?
Har yanzu Ƙungiyar tana tasiri a yankin.
Mun wuce akalla shingen bincike na sojoji guda shida kafin mu isa inda muka nufa.
Shi kansa Chibok gari ne mai dimbin sojoji. Sojojin sun ƙara kafa wasu shingayen binciken ababan hawa biyu da kuma dokar hana yawo daga yammaci har zuwa wayewar gari.
Sabuwar makaranta
An sake wa makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok fasali. An sake gina ta a cikin 2021, kuma an yi ƙarin shafe duk wasu alamun abubuwan da suka faru a wannan daren.
An rusa ɗakin kwanan daliban da aka sace. Babu wata alamar abin da ya faru shekaru goma da suka gabata -- sai dai wasu tubalan tsohon gini na siminti.
Ko da yake sabon gini ne, amma har sabon fentin da aka yi wa wasu gine-ginen makarantar ya fara koɗewa , watakila saboda yanayin zafi, wanda ya koɗar da launin ciyawar da ke gaban ginin gudanarwan makarantar zuwa launin ruwan goro.
An naɗa Muhammad Chiroma a matsayin sabon shugaban makarantar a lokacin da aka sake buɗe ta a shekarar 2021. Ya ce an samu ci gaba ta fuskar tsaro tun da ya fara aiki.
''Kusan kowane ɓangare na makarantar, ciki da waje, sojoji sun kewaye su. Muna da tsauraran matakan tsaro. Yayin da ka shigo nan, za ka ji kamar kana gida ne''.
''Iyayen da suka tura ƴaƴansu zuwa wasu makarantu yanzu suna dawo da su. Mun kasance muna karɓar sabbin dalibai da suke dawowa daga wasu makarantu” inji shi.
Babu zaɓin makarantu da dama a Chibok, daga makarantar firamare sai na sakandaren gwamnati
Mista Chiroma ya cewa ya bayyana mun tabbacinsa na cewa al’ummar nada cikakkiyar tsaro, kuma yana da ƙwarin guiwar kan sojojin da ke gadin su.
Sai dai an samu aƙalla hare-hare guda biyu na baya bayan nan na mayakan Boko Haram da suka kai a watan Disamba na shekarar 2023 da kuma Janairun 2024.
Ƴan bindigar sun kashe aƙalla mutane 14 tare da sace kayan abinci.
Ƙalubalen da ake fuskanta
An haifi Manasseh Allen kuma a garin Chibok kuma a nan ya girma. Amma ya koma babban birnin tarayya Abuja watanni takwas kacal bayan an sace ƴan matan makarantar.
A yau, yana fafutuka a madadin mazauna garinsu kuma yakan ziyarci iyayensa da ke fama da rashin lafiya.
''Akwai abubuwa da yawa da ba su canza ba a Chibok, har ma a makarantar. Haka ne, an yi gine-gine, amma babu wuraren koya da sadarwa na zamani, babu ɗakin gwaje-gwaje, babu ɗakin karatu, babu ruwa, babu komai.
''Ba a jin ɗuriyar gwamnati a nan yadda ya kamata, an shafe shekara 10 babu wutar lantarki; waɗanda ke yin kasuwancin da ke buƙatar lantarki ba za su iya aiki da kyau ba, ”in ji shi.
''Kafin 2014, na kasance ina aikin noma, da kiwon kaji da kifi. Na kasance ɗaya daga cikin manyan mutane masu zaman kansu da ke ɗaukar ma'aikata a Chibok.''
Mai fafutukar kuma ɗan siyasar ya ce an lalata masa sana’ar nomarsa a lokacin da ƴan Boko Haram suka kai farmaki.
“Mun yi asarar komai, komai ya ƙone, an kashe wasu direbobinmu a kan hanya. Mun yi asarar ababen hawa; mun yi asarar komai a hannun Boko Haram.''
Manassa ya yi imanin cewa babu wani ci gaba tun lokacin da ya yi hijira.
"Ina ganin gwamnati da duniya sun yi watsi da Chibok," in ji Manasseh.
Wurin da aka fi ganin hayaniya da kai-komo ita ce babbar kasuwar garin Chibok. Hassan Usman yana sayar da kayan gini a nan kuma yana maraba da ni cikin shagonsa, yana da sha'awar yin magana kan harkokin kasuwanci a Chibok.
“Tsaro a garin Chibok ya shafi kasuwancinmu sosai, musamman ma nawa. Ina sayar da kayan gini. Ba wanda ya yarda ya zo ya gina gidansa ko ya sake gyara gidansa.''
“Wasu sun yi hijira daga wannan unguwar tun a shekarar 2014, lokacin da aka sace ƴan makarantar. Amma yanayin tsaro yana farfaɗowa hankala a hankali," in ji shi.
Tun bayan sace ƴan matan makarantar Chibok a shekarar 2014, an sace dalibai sama da 1,400 a hare-haren makarantu aƙalla 10. A wasu hare-hare biyu a watan Maris, an sace dalibai sama da 300.
Ƙoƙarin da ake kan yi
A birnin tarayya Abuja, na gana da Sanata Muhammad Ali Ndume, wanda shi ne ɗan majalisar dattawa na ƙasa daga yankin Borno ta Kudu, inda garin Chibok yake, na jam’iyyar APC mai mulki.
"Gwamnati tana yin wani abu kuma gwamnati ta damu," in ji shi, "Zan roki iyayen yaran da su ci gaba da haƙuri kuma su ci gaba da addu'ar ƴaƴansu mata su dawo."
Ya ce biyan kuɗin fansa a lokacin gwamnatin da ta gabata, lokacin da aka sako ƴan matan Chibok sama da 100 bayan tattaunawa, ya ƙara ta’azzara matsalar.
''Allah ne kaɗai ya san adadin kuɗin da aka biya. Ina ganin daga nan ne mutane suka gane cewa idan ka sace wani, za ka iya samun kuɗaɗe masu yawa.
"Wannan banbban kuskure ne wanda ya kawo mu ga wannan halin rashin tsaron na yanzu."
Gwamnati a wancan lokacin ta musanta rahotannin da ke cewa ta biya kuɗin fansa domin sako ƴan matan Chibok 21 a shekarar 2016. Amma a shekara ta 2016, jami’ai sun bayyana cewa sun karɓo wasu ƴan matan Chibok 82 da ake tsare da su bayan sun amince da yin musayarsu da ƴan Boko Haram ɗin da aka kama.
Sanata Ndume ya yi watsi da sukar da ake yi masa na cewa ya gaza a idon mutanen Chibok, ya kuma ci gaba da kira ga gwamnati ta ɗauki matakin ceto sauran ƴan matan da kuma sauran mutanen da Boko Haram ke tsare da su.
“Majalisar dattawa za ta dawo ranar 16 ga Afrilu wanda zai kasance kwanaki biyu bayan cika shekaru 10 da sace ƴan matan Chibok,” in ji shi.
“Na yi alƙawarin gabatar da ƙudirin yin kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen hana sace-sacen mutane da kuma tabbatar da tsaro a makarantu,” in ji Sanata Ndume.
Fatan da iyayen ƴan matan makarantar Chibok 87 da suka bace ke yi na cewa za su dawo da ƴaƴansu mata na iya dusashewa, amma Esther ba ta yi ƙasa a gwiwa ba.
"Nasan cewa Allah yana tare da ita a can kuma ina fatan wata rana zan sake ganinta."