Bellingham ne gwarzon ɗan ƙwallon La Liga na 2023/24

Jede Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

An zaɓi ɗan ƙwallon Real Madrid, Jude Bellingham a matsayin gwarzon ɗan wasan La Liga na bana a kakar farko da ya yi a Sifaniya.

Bellingham, mai shekara 20, ya ci ƙwallo 19 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, wanda ya taimaka Real Madrid ta lashe kofin bana kuma na 36 jimilla.

Ƙungiyar Santiago Bernabeu ta kare a matakin farko a teburin gasar da tazarar maki 10 tsakaninta da Barcelona ta biyu mai rike da La Liga na bara.

Haka kuma ɗan wasan tawagar Ingila, ya zura ƙwallo hudu a raga a Champions League, inda ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta kai wasan karshe a bana.

Ranar Asabar 1 ga watan Yuni Real Madrid za ta fafata da Borussia Dortmund a wasan karshe a gasar ta zakarun Turai.

Tsohon ɗan ƙwallon Dortmund ya yi takarar gwarzon dan wasan La Liga a bana tare da takwaransa, Vinicius Jr da Antoine Griezmann na Atletico Madrid da Artem Dovbyk na Girona da kuma Robert Lewandowski na Barcelona.

Ƙyaftin din ƙungiyoyin dake buga La Liga ne ke yin zaben tare da magoya baya da mahukuntan dake gudanar da ƙyautar.

Bellingham ne ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan Bundesliga a 2022/23 a lokacin da yake taka leda a Dortmund, daga baya Real Madrid ta dauke shi kan £88.5m kafin fara kakar da aka kammala

Ɗan wasan ya buga wa tawagar Ingila karawa 29, ana sa ran zai taka rawar gani a Euro 2024 da Gareth Southagate zai ja ragama da za a fara 14 ga watan Yuni a Jamus.

Ingila za ta fara wasan farko a gasar ta nahiyar Turai ranar 16 ga watan Yuni da Serbia a Gelsenkirchen.