Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da zai faru idan aka kama Trump
Donald Trump na ci gaba da faɗi ta shi a Florida yayin da ake ta raɗe-raɗin za a kama shi a wannan makon, game da tuhumar da ake masa kan binciken da ake yi na dala 130,000 da ya biya wata fitacciyar mai fina-finan batsa Stormy Daniels a 2016.
Zai zama shugaban Amurka na farko da zai fuskanci tuhume-tuhume kan manyan laifuka.
Ga wasu tambayoyi da za su iya zuwa zuciyar mai karatu kan wannan rikici:
Me zai faru idan aka zargi Trump da haka?
A 2016, shahararriyar mai fina-finan batsar nan Stormy Daniels ta yi tayin sayar da wani faifan bidiyonta da suka yi da Donald Trump a 2006, ga kafafen yaɗa labarai, bidiyo irin na sana’arta.
Tawagar Trump ta girgiza da wannan barazana, abin da ya sanya lauyan Trump Micheal Cohen ya biya Daniels dala 130,000 domin ta yi shiru.
Hakan bai saba shari’a ba. Amma daga baya Trump ya biya Mr Cohen kudin da ya bayar, yana cewa kuɗin aikin da ya yi ne ya biya shi. Masu gabatar da ƙara sun musanta wannan kuɗaɗe a matsayin na biyan kuɗi – wannan laifi ne – A New York.
Masu gabatar da ƙarar za su iya sake zargin hakan ya saba dokar zaɓe, saboda boye kuɗin da ya biya Daniels wani mataki ne na hana masu zaɓe sanin abin da ke faruwa na mu’amala da wata. Hakan shi ma wani gagarumin abin tuhuma ne.
Ko masu fafutuka kan gabatar da ƙara sun amince ta ko wacce fuska wannan babbar shari’a ce a kotu. Akwai banbanci tsakanin kuɗaɗen da ake kashewa wajen neman zaɓe da kuma kashe kuɗin da mutum yake yi na raɗin kansa.
“Zai zama abu mai zafi, in ji Catherine Christian, tsohuwar mai gabatar da ƙara kan harkokin kuɗi a New York.
Shin za a iya tuhumar Trump?
Yanke hukuncin kan ko a tuhumi Trump yana hannun Antoni Janar na New York Alvin Bragg. Ya kafa wata tawagar alƙalai su bincika in akwai cikakkun hujjojida za su isa a gabatar da shi gaban kotu, kuma shi kaɗai ne ya san -yaushe za a sanar da lamarin ga jama’a.
A makon jiya, lauyoyin tsohon shugaban Amurkan sun ce ya nemi ya bayyana a gaban tawagar lauyoyin, wanda hakan ke nuni da cewa binciken ya kusa zuwa ƙarshe.
Lauyoyin sun musanta cewa dga su har Trump ab sanar da su wata tuhuma da za a yi mutu, wanda ya ce kalamansa da ake ta ya ɗawa na ranar Talata sun dogara ne da rahotannin kafafen yaɗa labarai.
Akwai kuma alamun da ke nuna cewa tawagar alƙalan na shirin naɗe tabarmarsu.
Daga Micheal Cohen har tsohon mai ba shi shawara kan harkokin shari’a Robert Costello sun bayar da shaida a ‘wan yakwankin nan.
Mai zai faru idan aka samu Trump da laifi?
Idan Mista Bragg ya yanke shawarar ci gaba da tuhumar, zai fara sanar da Mista Trump ne da lauyoyinsa, domin tattaunawa kan yaushe da kuma yadda Trump zai bayyana a kotun da New York a sauraren ƙarar da za a yi na farko.
Sanarwar tabbatar da laifin ka iya zuwa ne daga jami’in Antoni ko kuma lauyoyin Trump, waɗanda suke gaggawar shaida wa ‘yan jarida abin da ke faruwa.
Ba za a saki takardar da ke bayyana tuhume-tuhumen da ake yi wa Mista Trump har sai alƙali ya karanta masa.
Lauyoyin Mista Trump sun ce zai bayar da hadin kai ga hukumomin New York a don haka ba sai an bayar da takardar izinin kama shi ba.
Mista Trump ya mallaki jirgi na kashin kai don haka zai iya sauka a daya daga cikin tashoshin jiragen saman New York domin zuwa kotun Manhattan da mota.
Idan aka kama Trump, za a ɗauki hoton zanen yatsunsa?
A wani bangare na tattaunawa da masu gabatar da kara, kotun na iya amincewa ta bai wa Trump damar zuwa kotun a asirce a maimakon bi ta gaban gomman yan jarida kamar yadda aka saba.
Da zarar ya shiga kuma, za a ɗauki hoton zanen yatsun mista Trump da hoton fuskarsa kamar yadda ake yi wa wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka.
Za kuma a karanta masa ikon da yake da shi a tsarin doka na damar samun lauya da zabar kin yi wa yan sanda bayani.
Ana sakawa wadanda ake zargi da laifi ankwa ta wani dan lokaci duk da cewa lauyoyin Mista Trump za su yi kokarin kare afkuwar haka ga wanda suke karewa.
Zai kuma kasance bisa tsaron jami'an farin kaya har a kammala aikin.
Daga nan kuma Mista Trump zai dan jira har sai an kira shi gaban alkali.
Ana gurfanar da shi kuma, mutane za su iya ganin abin da ke faruwa a hgarabar kotun.
Da zarar an zabi alkali, sauran batutuwa za su dau harami kamar lokacin da za a yi shari'ar da yiwuwar takaita masa zirga-zirga da bukatar beli ga wanda ake zargi.
Samunsa da laifi zai janyo a ci tararsa. Idan aka samu Mista Trump da aikata laifi, zai sha daurin shekara hudu a gidan yari duk da cewa wasu kwararrun lauyoyi sun yi hasashen yiwuwar a ci tara ta fi karfi.
Zai iya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa?
Zargi ko ma samunsa da laifi ba zai hana Mista Trump ci gaba da yakin neman shugaban kasa ba idan har ya yi ra'ayi - kuma ya bayyana alamu karara cewa zai ci gaba kan kudirinsa ba tare da la'akari da abin da ka iya faruwa ba.
A zahiri, babu wani abu a dokar Amurka da ya hana ɗan takarar da aka samu da aikata laifi yin kamfen neman shugaban ƙasa ko ma a matsayin shugaban ƙasa - ko ma daga gidan yari.
Yayin da hakan na iya sa magoya bayan jam'iyyar Republic su goyi bayan gwarzonsu da ke cikin taƙaddama, hakan na iya zama muhimmiyar damar kawar da hankula ga dan takarar a kokarin neman kuri'u da kuma samun damar shiga muhawara.
Mr Trump's arrest would certainly complicate his presidential campaign, however.
While it might cause some Republican voters to rally around their embattled champion, it could be a significant distraction for a candidate on the campaign trail, trying to stump for votes and participate in debates.
It would also deepen and enflame already sharp divides within the American political system.
Conservatives believe the former president is being held to a different standard of justice, while liberals view this as an issue of holding law-breakers - even those in the highest positions of power - accountable.