Za a ɗaure tsohon shugaban Honduras a Amurka

Zanen hoton Juan Orlando

Asalin hoton, Reuters

Wata kotu a Amurka ta samu tsohon shugaban kasar Honduras da laifin hada baki da masu safarar miyagun kwayoyi wajen yin sumogal din kwayoyi zuwa Amurka.

Kotun da ke New York ta gano cewa, Juan Orlando ya yi amfani da sojoji da ‘yansandan Honduras, wajen satar shigar da tarin hodar Ibilis ta koken zuwa cikin Amurka.

Babbar madogarar lauyoyin tsohon shugaban kasar ta Honduras ta kariya daga zargi ko musanta laifin, ita ce, cewa shedun da gwamnatin Amurka ta gabatar a shari’ar miyagun masu laifi ne, wadanda ko kadan bai kamata a gabatar da su a matsayin shedu ba, ballantana ma a yarda da maganarsu.

To amma masu taimaka wa alkali yanke hukunci, a kotun ta New York, sun zabi yarda da bayanan tsoffin masu laifin na kisa da kuma masu satar shigar da miyagun kwayoyi a kann tsohun shugaban na Honduras.

A yanzu Mista Hernandez ya kasance tsohon shugaban wata kasa a Latin Amurka, da aka samu da laifin da ya danganci miyagun kwayoyi a Amurka, tun bayan tsohon shugaban Panama mai karfin fadi a ji Manuel Noriega, a 1992.

Yanzu dai faduwar bakar tasa da ya yi, daga amini na kut da kut ga gwamnatin tsohon shugaban Amurka, Donald Trump zuwa mai laifin safarar miyagun kwayoyi, ta kammala.

Kotun ta gano cewa ya rika karbar cin hanci daga babbar kungiyar nan ta masu safarar miyagun kwayoyi ta Sinaloa Cartel, musamman ma shugabanta Joaquin ‘El Chapo’ Guzman, domin bayar da kariya ga jiragen ruwa na safarar kwayoyin zuwa arewa wato Amurka, ta hanyar amfani da sojoji da ‚yansanda.

Daga cikin wadanda suka bayar da sheda a kansa, har da wani tsohon shugaban ‘yansanda, Juan Carlos ‘El Tigre’ Bonilla wanda ya rika masa aiki a baya, da kuma dan wani tsohon shugaban kasar shi ma, Fabio Lobo.

Tarin wasu masu zanga-zanga da suka kasance a wajen kotun sun yi ta murna kan hukuncin, wanda yawanci za a yi maraba da shi a can Honduras, cewa a karshe dai bayan mulkinsa na cin hanci da rashawa da kama-karya da muzgunawa na tsawon shekara takwas, a karshe ya gamu da gamonsa.

Sai dai iyalan tsohon shugaban na Honduras za su ci gaba da nuna cewa ba wani laifi da Mista Hernandez, ya yi bi-ta-da-kulli ne da kutungwilar siyasa kawai.

To amma tuni kaninsa wanda tsohon dan majalisar dokoki ne, Tony Hernandez, yana zaman gidan sarka na rai da rai har ma da karin shekara talatin, kan laifin rawar da ya taka wajen satar shigar da tarin hodar Ibilis ta koken zuwa cikin Amurka.

Yanzu dai tsohon shugaban kasar ta Honduras ka iya samun irin wannan hukunci.