Juan Orlando Hernández: Ƴan sanda sun cafke tsohon shugaban Honduras kan zargin fataucin miyagun ƙwayoyi
An kama tsohon shugaban Honduras Juan Orlando Hernández kan zargin ta'ammali da safarar ƙwayoyi.
An tura 'yan sanda gidansa da ke birnin Tegucigalpa sa'o'i bayan Amurka ta bukaci a mika ma ta shi saboda kar ya tsere.
Sun damke shi bayan fitar da sammacin kama shi. Ya mika wuya sannan aka tusa keyarsa gaba sanye da ankwa daga gidansa.
Mr Hernández ya mulki Honduras daga Janairun 2014 zuwa wannan shekarar. Ya musanta tuhume-tuhumen da aka gabatar kan sa.
Ana zarginsa da hannu a badaƙalar fataucin ƙwayoyi inda yake aiki tare da wata ƙungiya da kaninsa ke ciki, Tony Hernández, wanda a shekarar da ta gabata aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a Amurka.
A lokacin shari'ar Tony Hernández, masu gabatar da kara sun zargi cewa fitaccen ƙasurgumin mai fataucin ƙwayoyi na Mexico Joaquín "El Chapo" Guzmán ya bai wa Tony Hernández $1m.
A cewar masu shigar da ƙara, "El Chapo" Guzmán ya shaidawa kanin Hernández cewa ya bai wa ɗan uwansa Juan Orlando kudi a matsayin toshiya.
Honduras a shekarun baya-bayanan ta kasance wata cibiyar safarar ƙwayoyi daga Kudancin Amurka zuwa Amurka, sannan a kwanan nan ta kasance inda ake samar da hodar-ibilis.
Juan Orlando Hernández ya sha nanata cewa ya yi iya kokarinsa wajen ganin ya yaƙi fataucin miyagun ƙwayoyi, kuma lokacin mulkin shugaba Donald Trump, ya goyi-baya gwamnatin Amurka a wannan yaƙi.
Amma alakarsa da Amurka ta yi tsami a karkashin mulkin shugaba Joe Biden.
A makon da ya gabata, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da sanya sunan Mr Hernández cikin jeren mutanen da aka haramtawa shiga Amurka saboda aikata miyagun ayyuka.
A wata sanarwa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce akwai rahotanni masu sahihanci da ke tabbatar da cewa tsohon shugaban Honduras na aikata mugan laifuka da suka shafi kwayoyi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Mr Hernández ya mayarwa Mr Blinken martani, ya na mai cewa zarge-zargen da ake masa na da alaka da bayanan mutanen da aka samu da harkar ta'ammali da ƙwayoyi, kuma mutane ne da ke daukar fansa a kan sa.
Lauyansa ya shaida cewa yana da kariya daga garkame shi saboda tsohon shugaban mamba ne na majalisar tsakiyar Amurka.
Amma kwararu a fanin shari'a sun ce ana iya dage kariyar idan kasarsa ko mamba a majalisar ta bukaci hakan.












