Yadda sanya wa yara sunaye da yawa ke janyo ruɗani a Najeriya

Wasu ɗaliban Najeriya

Asalin hoton, AFP

    • Marubuci, Adaobi Tricia Nwaubani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wasiƙa daga Afirka

A baya-bayan nan dai ana ta ce-ce-ku-ce a Najeriya kan yadda ƴan takara uku a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a watan Fabrairu suka gabatar da shaidar karatu ɗauke da sunaye masu bambanci da waɗanda aka san su da su a yanzu.

Masu magana da yawun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar da kuma Peter Obi sun karyata zarge-zargen amfani da sunaye da takardun shaidar karatu na bogi.

Watakila kotunan shari’a za su tantance yadda za a warware wannan al'amari, amma hakan ya sa na dubi yadda wasu ƴan Najeriya ke amfani da sunaye da dama.

Ƴan Najeriya da dama na amfani da wasu sunayen bayan sunan mahaifi, na san mutane masu yawa waɗanda suke da suna biyar ko shida.

A al’umma mai al’adu da yawa da ke raɗa wa yaro suna bisa la’akari da yanayin haihuwarsu ko matsayinsu a cikin iyali ko kuma fatan iyaye game da makomar yaron, mutum ɗaya zai iya samun sunaye da dama da suke wakiltar abin da ake fatan ya zama idan ya girma.

Misali a ƙabilar Yarbawa za a iya raɗa wa yaro suna Taiwo Peter Tokumbo Olamide, Taiwo na nufin ɗan da aka fara haifa tsakanin tagwaye, Peter sunansa ne na addinin Kirista yayin da Tokumbo ke nufin wanda aka haifa a ƙasar waje, Olamide kuwa na nufin an samu arziƙi.

Jerin sunayen na haɗawa da sunan Ingilishi musamman ga mabiya addinin Kirista.

Yana kuma ƙunsar sunan da kakanni suka zaɓar wa jariri, wata dama da iyayen yaro suke bai wa iyayensu ta raɗa wa yaro suna.

Ina da sunaye uku, biyu na Igbo ɗaya kuma na addinin Kirista.

Na so ƙara wa kai na sunan addinin Kirista lokacin ƙuruciya yayin da na ke mamba a Cocin Katolika.

A makarantar kwana, shugaban cocin makarantarmu a kudu maso Gabashin Najeriya ya buƙaci mu ƙara wa kanmu sunayen addinn Kirista domin karrama bukin jaddada imani watau Sacrament.

Sai dai har yanzu ina gabatar da kaina a matsayin Tricia, wanda aka raɗa min a coci bayan an haife ni.

Ba na jin ina buƙatar ƙarin suna.

Wasu ƴan ajinmu sun yi amfani da damar su ta rashin iyaye a kusa a makaranta, inda suka ƙara wa kansu sunaye irin Madonna da sauran su.

Yan Najeriya da dama na sajewa da wasu daga cikin sunayensu saboda wasu dalilai.

Wataƙila saboda buɗe sabon babin rayuwa ko rashin son ma'anar sunan ko kuma saboda wahalar sunan a wasu yankunan.

Awai wadda muka taso tare a baya sunan ta Ogadimma amma yanzu ta koma Ego.

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu ƴan Najeriya na da sunaye daban-daban a takardunsu

Al'amarin ya fi rikitarwa idan ka ziyarci yankunan karkara a Najeriya.

A ci gaba da aikin bayar da rahoto a irin waɗannan yankuna, na sha cin karo da mutanen da sunayensu a katin shaidar su ya sha bamban da sunan da ke cikin asusun bankinsu. Wani lokaci sun bambanta da sunan da aka san su da shi a cikin al'ummarsu.

"Wannan sunana ne na ƙauye, wannan kuma shi ne sunana na makaranta," kamar yadda wasu suka shaida min.

"Wannan kuma sunan mahaifina ne."

Ba sa ganin cewa sanya sunaye da yawa a cikin takardun hukuma daban-daban na iya haifar da matsala, musamman idan ba zato ba tsammani sun sami kansu a cikin al'umma ko tsarin da ke bai wa takardun shaida muhimmanci fiye da Najeriya.

Masu bincike sun bayyana yadda samun takardun sauya suna da shekarun haihuwa ya ke da sauƙi a Najeriya.

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An ɗauki nauyin karatun 'yan matan Chibok da suka tsere daga hannun ƴan Boko Haram
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Na ci karo da irin wannan matsala ta bambancin suna yayin aiki da ƙungiyoyi daban-daban don taimaka wa al'ummar Chibok bayan an yi garkuwa da ƴan mata 276 daga ɗakin kwanan ɗalibai a shekara ta 2014 a Arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu ƙungiyoyin agaji sun fitar da jadawalin ƴan mata 57 waɗanda suka kuɓuta sa'o'i ƙalilan bayan an yi garkuwa da daliban, sun yi nasarar ficewa daga motar da ta ɗauki ɗaliban zuwa dajin Sambisa inda ƴan Boko Haram suka yi sansani.

Ƙungiyoyin sun ɗauki nauyin karatun wadanda suka kuɓutan don su yi karatu a makarantu daban-daban a fadin duniya.

Yayin da wasu daga cikin ƴan matan suka ƙi amincewa da ɗaukar nauyin karatun, sai iyayensu suka musanya su da ƴaƴan maƙwabtansu ko makusantarsu wadanda suke da sha'awa ba tare da sun sanar da ƙungiyoyin da suka ɗauki nauyin karatun canjin da aka samu ba.

Shugaban Ƙungiyar iyayen yaran da suka ɓata a Chibok, Yakubu Nkeki ya bayyana cewar:

"Akwai ƴan mata da suka kammala karatu a matsayin ƴan Boko Haram ba tare da kasancewar su daga cikin waɗanda suka kuɓuta daga hannun Boko Haram ba."

Ya shaida min cewa bai goyi bayan musayar ba. Amma al'ummarsa sun fi ƙarfin sa.

"Wasu daga cikinsu ba mazauna Chibok ba ne,"

"Iyayensu na Abuja ko Port Harcourt ko kuma Lagos amma suka ce su ƴan matan Chibok ne."

Watakila wadannan ƴan mata za su yi sauran rayuwarsu ta ilimi da sunan da ba nasu ba, kodayake ba abu ne mai wahala ba ga waɗanda suka saba amfani da sunaye daban-daban.

Irin wannan musayar ta faru lokacin da ƙungiyoyin agaji suka ɗauki nauyin karatun ƴan uwan ƴan matan da suka ɓata.

Abokan hamayyar shugaba Tinubu na fatan wannan dambarwa za ta sa Kotun Ƙoli ta soke zaɓensa.

Sun yi duk abinda za su iya a kafafen yaɗa labarai na gargajiya da shafukan sada zumunta don tabbatar da cewa sunaye daban-daban da ke cikin takardunsa alamu ne na cewar karatunsa na bogi ne.

Duk yadda sakamakon wannan al'amari ya kasance, zai iya zama darasi ga ƴan Najeriya a ko ina cikin duniya domin su daidaita sunayensu a muhimman takardu.