Haramcin zuwa makaranta a Afghanistan ya shafi ƙarin yara mata 330,000

Asalin hoton, Raess Hussain/ BBC
- Marubuci, By Aalia Farzan da Megha Mohan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Unicef ta shaida wa BBC cewa fiye da ƴanmata 330,000 za a hana shiga makarantar sakandare a Afghanistan cikin wannan shekarar.
A 2021, gwamnatin Taliban ta ce ƴan mata da shekarunsu ba su wuce 13 ba, ba za su ɗora da karantu ba bayan aji shida na firamare.
Zainab mai shekara 13 ɗaya ce daga cikin waɗanda ba za su ci gaba da zuwa makaranta ba a watan Maris mai zuwa.
A watannin da suka gabata, Zainab ba ta son soyayyen ƙwai da ya ji haɗi. Ƙanshin da ke tashi na soya ƙwai da madara ya tuna mata da shekarar da ta wuce, lokacin da take zuwa makaranta.
Ƙasa da wata shida da suka gabata kuma a lokacin tana cikin farin ciki. Ta na ta tashi ta yi sallar asuba sannan ta yi tattaki zuwa makaranta tare da ƙannenta mata da kuma yayanta namiji.
A yanzu idan an koma makaranta, za a soma sabbin darussa ba ta nan sannan soyayyen ƙwan na tuna mata abubuwan da za ta yi kewa.
Zainab ta jima da sanin ba za a bar ƴaƴa mata su je makaranta bayan kammala aji shida na firamare ba, amma ta na fatan wani abu zai suya. Tana son koyon karatu kuma tana ƙoƙari a dukkan darusan da ake koya ma ta, tana da ƙwanya a ɓangaren kimiyya kamar dai yadda take a fannin dabarun rayuwa.
"I ta ce ta ɗaya a ajinsu" in ji mahaifinta da ke matukar alfahari da ita, ita kuma Zainab ta na murmushi cikin jin kunya. Za ta iya yin fice a kowane aiki take so. Amma bayan ajin ƙarshe na firamare a Disambar bara, babban malamin makarantarsu ya shigo ajinsu lokacin da suke rubuta jarabawa inda ya faɗa wa dalibai matan da ke ajin su Zainab, cewa ba za su iya ci gaba da kartu ko zuwa makaranta ba a wtan Maris.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Ranta ya ɓaci sosai," in ji mahaifinta Shaheer, wanda a kan idonsa yarinyarsa ta koma gida. "Babu daɗi ganinta cikin wannan yanayin. Ba zan iya yin komai ga ƴaƴana ba kuma a matsayin mahaifi, ina jin kamar ina da laifi." Yayi ta ƙoƙarin kwashe iyalinsa daga Afghanistan, amma bai yi nasara ba.
"Ina jin kamar na binne burika na a ƙarƙashi rami mai duhu," in ji Zainab tana faɗi cikin sanyin murya lokacin da ta ke magana da wata a wyar salula ta bidiyo, sai kuma ta yi shiru na tsawon daƙiƙu. Mahaifinta ya tambaye mu ko tana iya sararawa domin hankalinta ya koma jikinta. Tattauna wannan batu ba mai dadi ba ne ga iyalan Shaheer.
Zaɓi daya da yara mata kamar Zainab ke da shi, shi ne zuwa ɗaukar karatu a makarantun koyar da ilimin addini na gwamnati. Sai dai wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman a Afghanistan, Roz Otunbayeva ya shaida wa kwamitin sulhu na majalisar a wtan Disambar bara cewa ba su kai ga gano ko makarantun islamiyya na mata suna koyar da darasin lissafi da Ingilishi ba.
Mahaifin Zainab ya ce Islamiyya ba za ta bai wa ƴarsa ilimin darusa daban-daban ba.
"Ba za ta maye gurbin makaranta ba. Kawai za su koyar da darusan addini. Ba na jin ya zama dole a tura ta Islamiyya," in ji shi.

Asalin hoton, Raess Hussain/ BBC
A ƙarƙashin mulkinTaliban, yara mata ba za su wuce matakin karatun Firamare na hekaru shida ba.
Tun ranar 15 ga watan Agustan 2021 ne Ƙungiyar Taliban take mulki a Afghanistan bayan da ta ƙwace mulki a Kabul, babban birnin ƙasar. Sojojin Nato bisa jagorancin Nato sun janye bayan nan. Lokacin taronsu na manema labarai na farko, sun sanar cewa ba za su zama masu tsatstsauran ra'ayi ba kamar Taliban ɗin da ta mulki ƙasar tsakanin 1996 da 2001.
"Za mu bar mata su yi karatu, su kuma yi aiki bisa tsarinmu. Za a dama da mata sosai a al'ummarmu," shi ne alƙawarin.
Sai dai daga baya, sun bijiro da wasu dokoki da suka take ƴancn mata. Cikin ƴan watanni, yara mata da ke shiga aji na bakwai ko kuma zuwa sakandare, aka hana su dama.
Sai kuma jami'oi da wuraren aiki da dama, suma aka yanke cewa na maza ne kawai.
A yanzu, ba a barin mata su fita daga gida ba tare da rakiyar muharraminsu ba, ko kuma zuwa wuraren shaƙatawa.
Yanayi ne maras daɗi. Unicef ya shaida wa BBC cewa jumullar yara mata da haramcin zuwa makaranta ya shafa tun 2021 ya zarce miliyan 1.4. Cikinsu, yara mata 330,000 da suka kammala aji shida na Firamare a 2023 waɗanda ba za su iya ci gaba da karatu ba a wannan shekarar.
Sai dai ba kowa ne ke bin dokokin Taliban.
Dangin Zainab sun ce akwai wasu shirye-shirye na al'umma da ake yi a unguwanni kuma Zainab tana zuwa ajin koyon Ingilishi. Babu wanda ya san tsawon lokacin da za a ɗauka ana yin karatun, amma a yanzu, tana samun damar ganin ƙawayenta a nan.
Tana iya ƙoƙarinta ta faranta mu su rai, tana karfafa mu su gwiwa. "Ina ƙarfafa mu ku gwiwa ku samu abubuwan da kuke sha'awar yi," ta faɗa wa BBC, "Ina ƙarfafa masu gwiwa su yi zane."

Asalin hoton, Raess Hussain/ BBC
Zainab ta tura wa BBC wani zane da ta yi na wata yarinya tsaye a gaban makarantar da aka rufe. Ta kira zanen nata "Kwanakin baƙin ciki ne ga yara mata a Afghanistan".
Zainab tana son yin zane. Abin da take yi ke nan idan ta koma gida daga makaranta a ranar da babban malami a makarantarsu ya ce babu gudu ba ja da baya.
"Abu na farko da na zana bayan da aka haramta mani zuwa makaranta shi ne na wata ɗaliba tana kallon ƙofar makarantarsu a rufe," in ji ta.
Sai dai cikin ƴan watannin da suka wuce, ta tilasta wa kanta zama mai kyakkyawan fata. A yanzu, tana zana abubuwa masu kyau - sararin samaniya da dogon gini da furanni da rana ko kuma ta hararo wani yanayi a gaba na burikanta sun cika. Saƙonta ga duniya shi ne kada a manta da yara mata kamar ta a Afghanistan.
"A taimaka wa yara mata ƴan Afghanistan su samu dawowar ƴancinsu," ta ce. "Yaran Afghanistan suna da kwanya sosai. Abin da kawai muke so shi ne dama."
BBC ta tambayi Taliban ta yi magana amma ba ta ce komai ba.
Additional reporting by Mariam Aman and Georgina Pearce
Names in this story have been changed for security reasons











