Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta yi wa Saka sabon tayi mai gwaɓi, City da Madrid na rububin Olise
Bayern Munich na da niyyar mayar da zaman aro na ɗan wasan Chelsea da Senegal Nicolas Jackson mai shekara 24 zuwa na dindindin. (TBR Football)
Arsenal na shirin biyan ɗan wasan ƙasar Ingila Bukayo Saka mai shekara 24, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazarar 2027, albashin sama da fam 250,000 a duk mako. (Talksport)
Tottenham na shirin ƙulla sabuwar yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya na Uruguay, Rodrigo Bentancur, mai shekara 28, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazarar 2026. (Athletic)
Manchester City da Real Madrid suna sa ido kan ɗan wasan Faransa Michael Olise a yayin da Bayern Munich ke tunanin inganta kwantiragin ɗan wasan mai shekara 23. (Teamtalk)
Southampton na shirin bai wa ɗan wasan tsakiyar West Ham James Ward-Prowse, mai shekara 30 damar komawa filin wasan St Mary's a watan Janairu. (GiveMesport)
Chelsea na da ƙwarin gwiwa cewa za ta iya ɗaukar golan AC Milan da Faransa Mike Maignan mai shekara 30. (ASRomalive)
Tottenham da West Ham da Nottingham Forest suna zawarcin ɗan wasan Parma ɗan ƙasar Argentina Mateo Pellegrino, mai shekara 23, amma kulob din na Italiya ba ya son sayar da shi kafin bazara mai zuwa. (TuttoSport)
Liverpool za ta iya amincewa ta bar ɗan wasan bayan Ingila Joe Gomez ya tafi a watan Janairu - muddin za ta iya samun wanda zai maye gurbinsa - yayinda da AC Milan ke nuna sha'awa kan ɗan wasan mai shekara 28. (Caughtoffside)
Porto ta na sa ido kan ɗan wasan Brighton da Ingila na ƴan ƙasa da shekara 21 Tommy Watson mai shekara 19. (Football Insider)
AC Milan na zawarcin ɗan wasan gaban Barcelona da Poland Robert Lewandowski, mai shekara 37. (Sport)
Ɗan wasan gaban Argentina Julian Alvarez, mai shekara 25, ya ce baya barin rade-radin da ake yi kan zawarcin da Barcelona ke yi masa ya shafe shi, kuma ya mai da hankali kan samun nasara a Atletico Madrid. (ESPN)