Yadda yaƙin Isra'ila da Iran ya haifar da tashin farashin man fetur a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNCPL ya sanar da ƙarin farashin man fetur a gidajen mansa da ke faɗin ƙasar.
Kamfanin ya ƙara farashin zuwa naira 945 a gidajen mansa da ke Abuja, yayin da sabon farashin a legas yake naira 915.
Ƙarin na NNPCL na zuwa ne ƴan kwanakin bayan matatar mai ta Dangote mai zaman kanta a ƙasar ta sanar da ƙarin farashin a depo zuwa naira 880 kowace lita.
Ƙarin farashin ba ya rasa nasaba ta tashin man a kasuwannin duniya da aka samu sakamakon yaƙin Isra'ila da Iran.
Yaƙin da ake gwabzawa tsakanin ƙasashen biyu na ci gaba da haifar da tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya.
A jiya Litinin an sayar da gangar ɗanyen man fetur kan dala 80, sakamakon ƙaruwar tashin hankalin, bayan shigar Amurka cikin yaƙin.
Iran na cikin manyan ƙasashen duniya masu arzikin man fetur, da ke fitar da shi zuwa kasuwannin duniya, kamar yadda Datka Ahmed Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur a Jami'ar Nile da ke Abuja ya bayyana.
'Iran ce ƙasa ta biyar a jerin ƙasashen duniya masu arzikin man fetur, inda take fitar da ganga kimanin miliyan huɗu a kowace rana'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa ƙasar na daga cikin jerin ƙasashen da suka fi samar da man fetur mai araha a duniya.
Tuni shugaban Amurk, Donald Trump ya yi kira da a sauko da farashin man a kasuwannin duniya.
Ta yaya yaƙin ya kawo tashin man fetur a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Injiya Yabagi Sani mai Sharhi kan al'amuran man fetur a Najeriya ya ce abin da ya shafi sauran ƙasashen duniya shi ne ya shafi Najeriya.
''Abin da ke faruwa shi ne kusan kashi 20 zuwa 30 na man fetur da ake hada-hadarsa a kasuwannin duniya ana yi ne ta mashigar Hormuz, wanda ke ƙarƙashin ikon Iran'',
Ya ƙara da cewa sakamakon yaƙin, Iran ta yi barazanar rufe mashigin, kuma saboda fargabar abin da ke je ya zo tuni jiragen dakon man fetur suka fara kauce wa mashigar, lamarin da ke haifar da ƙarancin man a kasuwannin duniya.
Dakta Ahmed Adamu ya ce galibi man fetur da ake amfani da shi a Najeriya, ana shigar da shi ne daga ƙetare.
''Kuma ita kasuwar man fetur galibi a dunƙule take, idan aka samu tashin man a kasuwar duniya dole a same shi a ko'ina, ciki har da Najeriya'', in ji shi.
Injiniya Yabagi Sani ya ce ''Idan ka ɗauki matatar mai ta Dangote wadda ita ce ke samar da mafi yawan mai da ake amfani da shi a Najeriya, tana shigo da ɗanyen mai ne daga waje, to ka ga idan ta sayo da tsada, ai dole ya sayar da tsada'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa shi kansa babban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL yana shigo da mai daga ƙetare.
Masanin man fetur ɗin ya yi gargaɗin cewa ba ma kaɗai man fetur ba, farashin komai zai iya tashi a cikin ƙasar, sakamakon wannan yanayi da aka shiga.
''Saboda idan ka duba ita wannan mashiga ta Hormuz ba man fetur kaɗai ake hada-hada ta ciki ba har da na abinci da sauran abubuwa, kuma ka san indai farashin mai ya tashi a Najeriya to yana shafar kusan komai a cikin ƙasar'', in ji shi.
Ko Najeriya na amfana da tashin farashin man fetur a duniya?

Asalin hoton, Dada Olusegun/X
Injiniya Yabagi Sani ya ce gwamnatin Najeriya za ta amfana da wannan ƙarin mai da aka samu akasuwannin duniya.
''Saboda za ta samu ƙarin kuɗin shiga, tattalin arzikinta zai bunƙasa'', kamar yadda ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa ''gwamnatin Najeriya ta ƙayyade kasafin kuɗinta kan farashin dala 75 kan kowace gaggar mai, to idan aka samu ƙari, kwanan gwamnati za ta samu rara na abin da ta ƙayyade za ta kashe a shekarar da muke ciki'', in ji shi.
''Hakan zai sa a samu ƙaruwar ayyukan ci gaba a cikin ƙasa, da samar da ayyukan yi ga ƴan ƙasar, sakamakon ƙarin kuɗin shiga da gwamnati ta samu'', in ji shi.
To sai dai Dakta Ahmed Adamu ya ce duk da ƙarin kuɗin shiga da gwamnatin Najeriya za ta samu sakamakon tashin farashin man fetur ɗin, akwai hatsarin samun tashin farashin kayyaki da tsadar rayuwa a Najeriya.
''Idan aka samu tashin farashin mai, to su ma gidajen mai za su ƙara farashin mai, don haka farashin komai zai ƙara a ƙasar, sakamakon ƙaruwar kuɗin sufuri.'' in ji shi.
Ta yaya gwamnati za ta sassauta wa ƴan ƙasa?

Abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta inganta ayyukan matatun man fetur huɗu da take da su domin tallafa wa ƴan ƙasar, a cewar Injiniya Yabagi Sani.
''Kuma tunda matatun na gwamnati ne, gwamnati za ta iya rage farashin da za ta sayar wa masu gidajen mai a ƙasar domin tallafa wa ƴan ƙasar'', in ji shi.
''Ai dama ƙarƙashin dokokin Najeriya akwai wani adadi na man fetur da aka ware domin ƴan ƙasar su yi amfani a cikin Najeriya'', in ji shi
Injiya Yabagi Sani ya ce ita matatar mai ta Ɗangote tun da ta ɗan kasuwa ne mai zaman kanta, ba za ta iya rage farashin man ba, tun da sayowa ta yi.
To amma ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta ci gaba da amfani da tsohon tsarin sayar wa matatar ɗanyen man da ka haƙo a cikin ƙasar, ta hanyar amfani da naira.
''Haƙiƙa wannan zai taimaka wajen rage farashin man a cikin ƙasa, saboda Dangote ya saya da araha, don haka shi ma zai sayar da araha'', in ji shi.
To sai dai Dakta Ahmed Adamu ya ce a irin wannan yanayi, babu abin da gwamnatin Najeriya za ta iya yi, saboda a tuni gwamnati ta fitar da hannunta a cinikayyar man fetur bayan janye tallafi.
''Gwamnatin Najeriya ta riga ta bar kasuwancin mai a hannun kasuwa, wato kasuwa ta yi halinta, kuma dama ita kasuwa ta gaji riba da faɗuwa'', in ji shi.










