Me ya sa Tinubu ya zaɓi tura jakadu Amurka da Ingila da Faransa kawai?

Bola Tinubu da Emmanuel Macron

Asalin hoton, Nigeria State House

Bayanan hoto, Bola Tinubu (dama) na da kyakkyawar alaƙa da ƙasar Faransa da Shugaba Emmanuel Macron kuma ya ziyarci Faransa kusan sau 10 tun bayan zaɓensa shugaban ƙasa
    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Bayan sama da shekara biyu ba tare da jakadu a ƙasashen waje ba, a ƙarshe dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike wa majalisar dattawan ƙasar sunayen wasu mutane domin tantancewa da amincewa a matsayin jakadu.

Sai dai mutum uku ne kacal ya nemi naɗawa zuwa ƙasashen Amurka da Ingila da Faransa, abin da ya sa masana ke ganin akwai dalilin da ya sa ya ɗauki matakin a yanzu.

A ranar 2 ga watan Satumban 2023 ne shugaban ya bayar da umarnin dawo da jakadu 109 daga ofisoshin jadakancin Najeriya a ƙasashen duniya, ban da wakilan Majalisar Ɗinkin Duniya a New York da Geneva.

Umarnin ta bakin Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar, ya ce an mayar da su gida ne saboda "kyautata aikinsu".

Tun daga lokacin ne kuma wakilai da ake kira Chargés d'Affaires suka koma gudanar da ofisoshin jakadancin, waɗanda ba su da cikakken iko kamar na jakadu.

'Yan hamayayya sun sha sukar gwamnatin APC game da ƙin tura jakadun da wuri, har ma suka dinga alaƙanta barazanar Shugaba Donald Trump ta kai wa ƙasar hari kan rashin cikakken jakada a Amuukar.

Sai dai Minista Tuggar ya faɗa wa BBC cewa gwamnatin na kan yi wa ayyuka da ofisoshin jakadancin kwaskwarima, da yaƙi da cin hanci, kafin sake tura sababbi zuwa ƙasashen waje.

Su wane ne Tinubu zai tura Amurka da Ingila da Faransa?

A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen Ayodele Oke, da Kanal Lateef Are mai ritaya, da kuma Amin Dalhatu domin amincewa su zama jakadun Najeriya Amurka da Birtaniya da Faransa.

Shugaban Majalisar Dattawan Godswill Akpabio, wanda ya karanta wasiƙar sunayen a zauren majalisa, ya umurci kwamitin kula da harkokin waje ya tantance sunayen kuma ya kawo rahotonsa cikin mako ɗaya.

  • Amin Mohammed Dalhatu: Shi ne tsohon jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari a 2016
  • Ayodele Oke: Tsohon shugaban hukumar NIA mai tattara bayanan sirri ne, kuma tsohon jakadan Najeriya a ƙungiyar Commonwealth of Nations ta ƙasashen rainon Ingila a Landan
  • Lateef Kayode Are: Tsohon shugaban hukumar 'yansandan farin kaya DSS ne daga 1999 zuwa 2007. Ya riƙe muƙamin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro a 2010

Me ya sa aka zaɓi Amurka da Ingila da Faransa?

Tinubu da tsohon Ministan Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, A watan Janairun 2024 tsohon Ministan Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken (hagu) ya kai wa Tinubu ziyara a Abuja
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amurka

Alaƙa tsakanin Amurka da Najeriya na da girman gaske, musamman idan aka duba ɓangaren kasuwanci da tsaro.

Amurka na cikin abokan hulɗar kasuwanci da Najeriya mafiya girma. A 2022, kuɗaɗen zuba jari da suka shiga Najeriya daga Amurka sun kai dala biliyan 5.6. Hulɗar kasuwanci kuma tsakaninus ta kai dala biliyan 10.6 a shekarar.

Najeriya kan fitar da man fetur da wasu kayayyaki zuwa Amurka, yayin da Amurka kan shigar da ababen hawa da na'urori Najeriya.

A fannin tsaro kuma, Amurka kan bai wa dakarun Najeriya horo a famnnin yaƙi da Boko Haram, da kuma sayar mata da makamai kamar jiragen yaƙi ƙirar A-29 Super Tucano.

Sai dai Dr. Elharun Muhammad, masanin hulɗa tsakanin ƙasashen duniya, ya ce barazanar Shugaba Donald Trump ta kawo wa Najeriya farmaki ce babban dalilin zaɓar Amurka wajen tura jakada a yanzu.

"Wannan barazana ta fito da buƙatar tura jakada ƙarara. Da a ce muna da jakada a Amurka da Trump ba zai ɗauki wannan matsayar ba, da ba za mu kawo nan ba," in ji shi.

Ingila

A matsayinta na tsohuwar uwar gijiyar Najeriya a lokacin mulkin mallaka, Ingila na da tasiri babba a kan Najeriya da ma 'yan Najeriya. Mambobi ne a ƙungiyar Commonwealth of Nations ta ƙasashe rainon Ingila.

A fannin kasuwanci, Ingila babbar abokiyar hulɗa ce ga Najeriya. Hulɗar kasuwanci tsakaninsu ta kai fan biliyan 7.2 a 2024. Akwai yarjejeniyar kasuwanci tsakaninsu mai taken Enhanced Trade and Investment Partnership (ETIP), inda kamfanonin Ingila ke zuba jari a fannin makamashi, da fasaha, da harkokin kuɗi a Najeriya.

A fannin tsaro, ƙasashen sun saka hannu kan wata yarejeniyar tsaro a 2018, wadda ta bai wa Ingila damar horar da dakarun Najeriya, da kuma musayar bayanan sirri a tsakaninsu domin daƙile manyan laifuka.

Dr Elharun ya ce dalilin da zai sa a tura jakada a yanzu shi ne, "abin da ya yi Amurka shi ne ya yi Ingila".

"Ka ga ita ta yi mana mulkin mallaka. Sannan ita da Amurka Ɗanjuma ne da Ɗanjummai."

Faransa

Shugaba Tinubu na da kyakkyawar alaƙa da Faransa fiye da shugabannin Najeriya da aka yi a baya-bayan nan. Tun bayan zaɓarsa a matsayin shugaban ƙasa, Tinubu ya kai ziyara Faransa ta aiki ko ta shaƙatawa kusan sau 10.

Bugu da ƙari, Najeriya na ɗaya daga cikin abokan hulɗar Faransa mafiya girma a yankin hamadar Afirka a fannin kasuwanci. Ita ce ta huɗu a Afirka gaba ɗaya bayan Morocco, da Algeria, da Tunisia.

Najeriya kan yi safarar man fetur da gas zuwa Faransa, yayin da take sayo sararrafaffun kayayyaki da ababen hawa da kayan noma daga can.

Kuɗaɗen zuba jari na Faransa a Najeriya ya kai kusan yuro biliyan 7.2 a 2021. Kamfanonin Faransa kamar Total sun shafe shekaru suna hada-hada a Najeriya.

A fannin tsaro ma, ƙasashen na musayar bayanan sirri domin taimakawa wajen yaƙi da Boko Haram a Tafkin Chadi.

Sai dai Dr Elharun na ganin alaƙar Tinubu da Faransa ce kan gaba wajen yanke hukuncin tura jakada ƙasar.

Ta fuskar ƙasashen da Najeriya ke kai kayayyaki mafiya yawa, ƙasashen Sifaniya da Amurka da Indiya ne kan gaba. China ce ta ɗaya a jerin ƙasashen da suka fi shigar da kaya Najeriya.

Wannan ta sa ake ganin Shugaba Tinubu ya zaɓi Amurka da Ingila da Faransa ne domin yin aiki kan wasu batutuwa na musamman.

Sarki Charles na Ingila da Bola Tinubu

Asalin hoton, others

Bayanan hoto, A watan Satumban 2024 Tinubu ya kai ziyara Ingila inda ya gana da Sarkin Charles

'Bai kamata ba'

A matsayinta na ƙasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka, Najeriya na da hulɗa da ƙasashe masu yawa, na kusa da na nesa.

Bisa al'ada, ƙasashe kan ɗauki hulɗa tsakaninsu da maƙwabtansu da muhimman gaske musamman saboda tsaronsu da kuma cigaban al'ummominsu.

Wannan ta sa Dr Elharun Muhammad ke cewa zaɓar ƙasashen Amurka da Ingila da Faransa "na tumun dare ne" saboda ba su ne suka fi muhimmanci ba.

"Bai kamata ba gaba ɗaya [a zaɓi Amurka da Ingila da Faransa kawai]. Ƙasashen Nijar da Kamaru da Benin na da muhimmanci ga Najeriya," in ji shi.

"Akwai masanan da ke ganin alaƙar Najeriya da ƙasashen Nijar, Kamaru, da Benin ta fi ta fi muhimmanci a kan ta Amurka da Ingila da Faransa."