Yadda ya kamata Najeriya ta tunkari barazanar Trump

Masana harkokin tsaro a Najeriya sun fara tsokaci kan rahotannin da ke cewa rundunar sojin Amurka ta gabatar wa shugaba Trump tsare- tsare yadda za a kai wa Najeriya hari, bayan umarnin da shugaban ya ba wa shalkwatar tsaron kasar ta Pentagon.
Wannan dai na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurkar Donald Trump, ya yi, ta kai hari Najeriyar saboda zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi.
Tsare-tsaren Amurka uku kan Najeriya
Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito cewa Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth ya fitar da tsare-tsare uku kan yadda Amurka ya kamata ta shiga Najeriya.
Tsare-tsaren dai sun hada da gagarumin hari, na matsakaici da kuma na mai dogon zango.
- Gagarumin hari; Shi ne wanda zai ƙunshi aika wata rundunar mayakan ruwa ta musamman zuwa gabar tekun Guinea tare da rakiyar manyan jiragen sama na yaki, wadanda za su iya yin barin wuta kan 'yan bindiga a yankin arewacin Najeriya.
- Matsakaicin hari: Shi ne wanda zai kunshi aika jirage marasa matuƙa, domin kaddamar da hare-hare kan sansanonin masu tayar da kayar baya, da ayarinsu da ababen hawansu.
- Tsarin hari sassauka: Shi ne wanda zai fi mayar da hankali ga batun samar da bayanan sirri, da bayar da taimakon kayan aiki, da kuma gudanar da sintirin hadin gwiwa da dakarun Najeriya domin ganin an kakkabe 'yan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin masu dauke da makamai.
Shawar masana

Asalin hoton, Tinubu X
Tuni dai masana harkokin tsaro irinsu Birgediya Janar Muhammad Muhammad Yarima, mai ritaya, suka ce wannan mataki na Amurka wata karfa-karfa ce kawai.
Ya ce,"Ya za a yi ka shiga kasar mutane da 'yancinsu ba wai karkashinka suke ba, sannan ka kawo wasu tsare-tsare har uku, to wadannan tsare-tsare ba wani bane face kawai Amurka na sony in fada da Najeriya ne domin babu wata kasa da zata yar da ta na gani ka shigo cikin kasarta ka yake ta sannan ka fita ka tafi kuma ba a tanka maka ba."
Masanin tsaron ya ce,"Idan har Amurka na son taimakawa ne to sai ta yi amfani da tsari uku data ambata a cikin tsare-tsarenta sai su zo su samu gwamnatin Najeriya su ce mata mun san inda wadannan 'yan ta'adda suke don haka mun zo mu taimaka muku."
"Idan Amurka ta dauki tsari na uku ta yi amfani da shi to yafi musu sauki haka muma a wajenmu 'yan Najeriya, amma idan ta ce zata dauki kowane daga cikin biyun nan ta yi amfani dashi to cin zali ne karara."In ji shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsohon hafsan sojin Najeriya, ya ce wajibi ne kuma a kauce wa wannan zaluncin, sai fa idan Amurka so take ta yi maye fake da agana a Najeriya.
Birgediya Janar Muhammad Muhammad Yarima mai ritaya, ya ce „ Idan an kula za a ga a kwanannan Amurka ta matsawa Venezuela, ba wani abu bane illa mai, saboda kasar na da man fetir, to a Afirka ai Najeriya na da mai don haka shi y asa Amurka ta ke so ta shigo mata."
Ya ce," A zahiri Trump ba zai shigo Najeriya saboda ana kashe kiristoci ba saboda mai zai shigo, a don haka ya kamata gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye don daukar matakin da ya dace."
Masanin tsaron ya ce, "Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi shi ne ta tashi mutane masu mutunci da kima wadanda suka san abubuwan da ke faruwa kamar jakadun da suka yi ritaya a sa su su je Amurka su yi magana, sannan gwamnatin Najeriya ta rubuta wasika ta ce ba wai mun bari ana kshe kiristoci bane, a'a ga abin da ke faruwa sannan ga matakan da muke dauka su yi bayani dalla-dalla, amma ba wai a tsaya ana ta ce-ce-kuce a cikin gida ana yadawa a kafafan sada zumunta ba.











