Abubuwan da suka kamata Musulmi su yi a ranar Arfa

Asalin hoton, Getty Images
A Yau Alhamis, 5 ga watan Yunin 2025 ne ake gudanar da hawan Arfa na aikin Hajjin shekarar 1446 bayan Hijira.
Musulmai kusan miliyan 1.5 ne ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya.
Aikin Hajji ɗaya ne daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci, wanda ake son kowane Musulmi ya yi idan ya samu hali.
A cewar malamai, ranar Arfa ce mafi falala a cikin ranaku.
Sheikh Isa Ali Pantami ya ce ranar Arfa ita rana mafi daraja cikin ranakun shekara da Allah ya hallita.
''Kamar yadda a cikin darare babu daren da ya kai na laylatul qadar falala, haka ma a cikin ranaku babu wadda ta kai ranar Arfa falala da daraja a wajen Allah'', in ji Sheikh Pantami.
Sheikh Pantami ya ce saboda daraja da falalar ranar Allah S.W.T da kansa ya ambaci sunan ranar a cikin Alqur'ani mai girma, cikin suratul Bakara aya ta 198.
Shehin malamin ya ce a ranar ce kuma Allah ya cika wa bayinsa addininsa.
Shi ma Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce rana ce da Allah yake yin gafara ga waɗanda duk suke da rabo.
Asalin sunan 'Arfa'

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sheikh Ibrahim Mansur malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya ce akwai maganganun malamai har uku dangane da asalin inda ranar Arfa ta samo asali.
Magana ta farko, an kira ta Arfa ne saboda a lokacin ne mutane daga sassa daban-daban ke sanin juna saboda haɗuwa a wuri guda. Sai ake kiranta Arfa, kamar yadda malamin ya yi bayani.
Na biyu kuma, wasu malamai sun ce mala'ika Jibrilu ya ɗauki Annabi Ibrahim yana kewayawa da shi don nuna masa alamomi na aikin Hajji.
To idan ya nuna abu sai ya tambaye shi, "Aarafta, Aarafta" da Larabci - wato ka gane?. Shi kuma Annabi Ibrahim sai ya ce "Araftu, Araftu" - na gane, na gane.
''Wannan dalilin ne ya sa aka saka mata Arfa'', in ji malamin.
Magana ta uku, lokacin da Allah Ya sauko da Annabi Adam da Nana Hawwa'u zuwa duniya sun daɗe ba su haɗu ba. Amma da Allah Ya tashi haɗa su sai ya haɗa su a ranar Arfa.
''Wannan haɗuwa da suka yi suka gane juna, sai ya sa ake kiran ta Ranar Arfa'', kamar yadda ya yi bayani.
Falalar ranar Arfa
Arfa rana ce mai girma ƙwarai da gaske, kamar yadda malamai suka yi ƙarin bayani.
Manzon Allah ya ce babu wata rana da ake ganin shaiɗan a wulaƙance kamar irin wannan rana.
Kuma Sheikh aminu Daurawa ya ce akwai hadisi da annabi S.A.W ke cewa mafi alkairin addu'a ita ce addu'ar da aka yi ranar Arfa.
Abubuwan da suka kamata mahajjata su yi a ranar

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Arfa ta kasance ɗaya daga cikin muhimman ranaku ga mahajjata.
Abubuwan da ake son kowane mahajjaci ya yi a wannan rana sun haɗa da:
- Tsayuwar arfa: Ana yin tsayuwar ne a filin arfa da ke wajen garin Makka tun bayan kaucewar rana daga tsakiyar sama zuwa faduwarta don gudanar da daya daga cikin rukunan aikin Hajji. Sheikh Aminu Daurawa ya ce akwai hadisi ingantaccen da annabi S.A.W yake cewa ''Hajji ita ce arfa''. La'aari da wannan hadaisi ne malmai suke cewa duk alhajin da ya rasa tsayuwar arfa to ya rasa aikin hajji.
- Yawaita Addu'a: Sheikh Isa Ali Pantami ya ce abin da ake son alhazai su yawaita a ranar shi ne yawaita addu'o'i, saboda rana ce da ake ƙarbar addu'ar.
- Zikiri/Kabarbari: Wani abu da ake son alhazai su yawaita a wannan rana shi ne zikiri da kababari, kamar yadda Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana. Malamin addinin ya ce akwai buƙatar mahajjata su yawaita zikiri da kabarbari.
Abubuwan da suka kamata sauran musulmi su yi
La'akari da irin tarin falalar da ranar arfa ke da shi, akwai abubuwan da ake so sauran musulmai da ba su je aikin hajjin ba, su yi a wannan rana da suka haɗa da:
Azumi: Sheikh Ali Isa Pantami ya ce Hadisi ya zo annabi na cewa azumin ranar Arfa na kankare zunubin shekara biyu, wadda ta gabata da wadda za ta zo.
Don haka ne Sheikh Daurawa ya yi kira ga duka musulmai inda za su iya su daure su yi azumin wannan rana.
Addu'ar kuɓuta daga wuta: Hadisi ya zo Annabi na cewa babu wata rana da ake yawanita ƴanta bayin Allah daga wuta zuwa Aljanna kamar ranar Arfa, a cewar Sheikh Pantami.
Zikiri da kabarbari: Sheikh Daurawa ya ce zikiri mfi soyuwa aranar arfa sgi ne 'La'ilahalillah Wahadahu la sharikalak-lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai'in qadir''.
Karatun alqur'ani: Karatun alqur'ani na daga cikin manyan ayyukan alkari da ka fi so musulmi su yawaita a ranar arfa.
Sada zumunci: Sheikh Pantami ya ce sada zumunci na daga cikin abubuwan da ke sa mutum ya kuɓuta daga tsinuwar Allah
Duba marasa lafiya: Yana da kyau, musulmi su ƙarfafa duba marasa lafiya domin yi musu addu'a a wannan rana, musamman saboda rana ce ta karɓar addu'a, kamar yadda Sheikh Pantami ya yi bayani.
Sadaqa: Wannan ya kasance ɗaya daga cikin ayyukan alkairi da ake son mutum ya yawaita a ranar Arfa a cewar Sheikh Pantami.
''A na so mutum ya yawaita kyau da sadaqa musamman na abincin da mutane za su dafa da sallah da dabbobin da za su yanka sdomin layya'', in ji shi.
Abubuwan da ba a so Musulmi su yi a ranar arfa
Ranar Arfa rana ce da ba a son saɓo a cikinta, don haka malamai suke bayar da shawarar ƙaurace wa abubuwa kamar haka, kamar yadda Sheikh Ibrahim Mansur ya bayyana.
- Yawan kalle-kalle
- Gane-gane da ba su kamata ba
- Gulmace-gulmace da zantuka marasa kan gado
- Yawan jiye-jiye marasa amfani
- Ba a son jin zantukan banza











