Tarihin ƙarin farashin man fetur a Najeriya daga shekarar 2000-2024

Lokacin karatu: Minti 4

A makon da ya gabata ne babban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, ya sanar da ƙarin farashin kuɗin man fetur a ƙasar daga naira 617 zuwa naira 897 kan kowace lita.

Ƙarin ya zo wa ƴan ƙasar da dama da mamaki, ganin yadda aka yi ƙarin a daidai lokacin da ƴanƙasar ke kokawa kan halin matsin tsadar rayuwa da suke ciki.

Najeriya ce ƙasa mafi arzikin man fetur a nahiyar Afirka, kuma ita ce ta fi kowace ƙasa a nahiyar fitar da man zuwa kasuwar duniya.

Lamarin da ya sa da dama ke ganin bai kamata a ce man ya yi tsada a ƙasar ba.

Sabon ƙarin kuɗin man shi ne na biyu tun bayan hawan shugaba Tinubu kan mulkin Najeriya a watan Mayun 2023.

An samu ƙarin farko bayan da shugaban ƙasar ya sanar da matakin gwamnatinsa na janye tallafin man fetur a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasa.

Duk da cewa ba wannan ne karo na farko da aka taɓa yin ƙarin farashin mai a ƙasar ba, hakan ya bai wa 'yan ƙasar da dama mamaki.

BBC ta yi nazari kan tarihin ƙarin farashin mai da aka fuskanta a Najeriya, tun daga shekarar 2000 zuwa yau.

Lokacin Obasanjo, 1999 - 2007

Jim kaɗan bayan hawansa mulki, Cif Olusegun Obasanjo ya ƙara farashin man daga naira 20 zuwa naira 30, a ranar 1 ga watan Yunin 2000.

To sai dai a ranar 8 ga watan Yunin 2000 Obasanjon ya rage farashin daga naira 30 zuwa naira 22, wato kimanin ragin kashi 10 cikin 100.

A ranar 1 ga watan Janairun 2002, Obasanjon ya sake ƙara farashin daga naira 22 zuwa naira 26.

A watan Yuni 2003 Obasanjo ya sake ƙara farashin daga naira 26 zuwa naira 42.

Ranar 29 ga watan Mayun 2004 kuma Cif Obasanjo ya mayar da farashin man naira 50. Ƙarin kashi 19.05%.

Ranar 25 ga watan Agustan 2004 ya sake ƙara farashin zuwa naira 65.

Ƙarin farashin mai na ƙarshe da Obasanjo ya yi shi ne na ranar 27 ga watan Mayun 2007, inda man ya koma naira 75, ƙarin kashi 15.38%.

Zamanin Ƴar'adua, 2007 - 2009

Shugaba Umaru Musa 'Yar aduwa ya rage farashin mai daga naira 75 zuwa 65 a watan Yunin 2007.

Marigayi Umaru 'Yar'aduwa ne kaɗai wanda bai ƙara farashin man fetur ba cikin shugabannin da suka mulki Najeriya tun daga 1973.

Zamanin Jonathan, 2009 - 2015

A ranar 1 ga watan Janairun 2012 Goodluck Jonathan ya yi ƙoƙarin ƙara farashin zuwa tsakanin naira 138 da naira 250, amma daga bisani ya tsaya a kan naira 97, sakamakon zanga-zangar adawa da matakin.

Lokacin Buhari, 2015 - 2023

Ƙarin farashin mai na farko da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi, shi ne ba da damar sayar da man a kan naira 87 da kobo 50 a gidan man 'yan kasuwa kodayake farashin bai sauya ba a gidajen man NNPC.

Tun daga wannan lokaci ba a sake samun ƙarin farashin man ba sai a ranar Laraba 11 ga watan Mayun 2016 da gwamnatin Shugaba Buhari ta mayar da shi naira 145.

A watan Maris 2020 - faɗuwar darajar fetur a kasuwar duniya ta sake tilasta wa gwamnatin rage kuɗin man daga N145 zuwa N125.

Bayan wata guda, a karo na biyu a watan Mayun 2020, hukumar ƙayyade farashin albarkatun man fetur ta PPPRA ta sanar da sabon farashi daga N121.50 zuwa N123.50 lita guda.

Sai kuma a ranar Laraba 2 ga watan Satumban 2020 da ƙungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta umarci 'ya'yanta su ƙara kuɗin farashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.

Sai a watan Nuwamban shekarar farashin ya ƙaru zuwa naira 170.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bar litar mai a kan naira 210 ya zuwa ranar da ya miƙa wa Tinubu mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Zamanin Shugaba Tinubu 2023 zuwa yanzu

Tun sanarwar janye tallafi da shugaba Tinubu ya yi a ranar kama aikinsa ta 29 ga watan Mayun 2023, farashin mai ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya.

Kwanaki kaɗan bayan sanar da matakin, babban kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya sanar da sabon farashin mai na naira 617 a kan kowacce lita wato ƙarin kusan kaso 300 a kan tsohon farashin.

A ranar Talata, 3 ga watan Satumbar 2024, wato kimanin wata 16 bayan hawansa, kamfanin na NNPCL ya sake fito da wani sabon farashin man na naira 897, inda aka samu ƙarin naira 280.

Wannan sabon ƙarin farashin na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce tsakanin al'ummar ƙasar, inda dayawa ke ganin lamari ne da zai ƙar ta'azzara mawuyacin halin da ake ciki sakamakon matsanancin tsadar rayuwa da 'yan ƙasar ke fama da ita.